Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

A Yi Hattara Da Bambancin Ra’ayin Siyasa Dake Bata Moriyar Al’ummun Duniya

Published

on

Kawo yanzu, ana ci gaba da kokarin yakar cutar numfashi ta COVID-19, wannan ne ma ya sa masu tsara manufofin gwamnatin kasar Sin suke ba da muhimmanci ga batun ba da kariya ga lafiya da tsaron jama’a a duk fadin duniya, misali mahukuntan kasar Sin sun dauki wasu matakan musamman kamar hana fita da killace unguwani a biranen da suka fi fama da yaduwar cutar kamar birnin Wuhan na lardin Hubei, duk wadannan sun samu amincewa da fahimta daga mazauna wuraren, inda suke zaune a cikin gida bisa radin kansu, domin ba da gudummowarsu kan aikin dakile annobar, lamarin da ya nuna cewa, al’ummun kasar sun nuna biyayya kuma suna kiyaye moriyar jama’a.

Michael Ryan, mai kula da aikin gaggawa a hukumar lafiya ta duniya ya yi nuni da cewa, yanzu haka adadin mutanen da suke kamuwa da cutar ya ragu, an samu nasarar haka, saboda gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suka dace.

Amma wasu kafofin watsa labaran kasashen yamma sun juya baya kan sakamakon da kasar Sin ta samu, inda suke zargin cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka a birnin Wuhan da sauran sassan kasar daya ne daga cikin ayyukan sarrafa al’ummun kasa mafiya tsanani a tarihi, zargin da ya kawo illa ga moriyar jama’a ta kasa da kasa.

Hakika ya zama wajibi a martaba kuma a kiyaye babbar moriyar jama’a, a don haka al’ummun kasar Sin suna kiyaye moriyar jama’a ta hanyar daukar matakan da suka shafi hakkinsu, duk wadannan sun nuna cewa, wayewar kan zamantakewar al’ummar kasar Sin ta samu babban ci gaba, annoba tana iya shafar daukacin bil Adama, a don haka, ya dace daukacin al’ummun kasashen duniya su hada kai domin ganin bayanta, kana ya dace a daina baza kwayar cutar siyasa ba tare da bata lokaci ba. (Mai Fassarawa: Jamila Zhou)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: