Connect with us

LABARAI

Tsofaffin Daliban WTC Sun Yi  Rawar Gani – Farfesa Fatima

Published

on

Shugabar kungiyar Tsofaffin dalibai ta Kwalejin Makarantar Koyarwa ta Mata (Women Teachers College) WATCOSA, wadanda suka kammala karatunsu a shekarar 1973 ta bayyana cewa, tsofaffin dalibai na wannan kungiya tasu ta matukar taka muhimmiyar rawa wajen kawo a gaji da taimakawa wannan makaranta, musamman ta hanyar amsa kisa na kowace daliba da Allah Ya horewa hali da kuma wadata, da ta kawo a kalla kujera daya zuwa abinda ya sauwaka.

Kazalika, wadannan tsofaffin dalibai, na bayar da hadin kai wajen kawo abubuwan da suka shafi kujeru, gadaje da sauran kayayyakin da ake bukata. Don haka, wannan abin a yaba ne kwarai da gaske, a cewar Shugabar ta WATCOSA.
Farfesa Fatima, ta bayyana haka ne a lokacin da tsofaffin daliban makarantar suka yi bikin cika shekaru 43 da kammala makarantarsu a wannan lokaci, inda ta ce gudummawar gadaje 200 na kwanan dalibai daga mai dakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafsatu Abdullahi Umar Ganduje abin a yaba ne matuka gaya, sai kuma gadaje 100 na kwanan dalibai daga mai dakin Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Asama’u Muhammad Badaru Abubakar da dai sauransu suka kawo.
Haka zalika, Farfesar ta kara da cewa, tana matukar alfahari da wannan makaranta, domin kuwa ita ce silar zama dukkanin abinda ta zama a halin yanzu, sannan kuma duk da kasancewar Turawa da Larabawa da sauran makamantansu sun koyar da su, amma wannan bai raba su da Addininsu da kuma al’adunsu masu kyau, musamman na kunya, da’a, kara da kuma sanin ya kamata ba.
Har wa yau, Hajiya Umma Kabir Bayero, Hajiya Mariya Tsohuwar Shugabar Makarantar Kabo da WTC, wadda kuma Darakta ce a halin yanzu, Hajiya Saude Sumaila, Hajiya Aisha Mannir Matawalle da sauran manya-manyan daliban wannan makaranta, sun yaba wa kokari da irin gagarumar gudunmawar da ita kanta Shugabar wannan kungiya ‘WATCOSA’ ta kasa, Farfesa Fatima take bayarwa musamman na ginin Rijiyar Burtsatsai da Shugabar ta yi tare da farfado da darajar wannan makaranta a koda-yaushe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: