Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Abubuwan Da Allah Ya Ba Annabi Muhammadu (SAW) Shi Kadai (2)

Published

on

To sai abin da Allah ya ba Annabi Adamu (AS) na sanar da shi sunaye. Amma game da wannan da Allah ya ba Annabi Adamu na sanar da shi sunayen komai, shi ma Manzon Allah (SAW) an ba shi haka. Manzon Allah (SAW) ya ce “Ni Allah ya nuna mun al’ummata tun tana tsakanin ruwa da yumbu (tun kafin a halicce ta). Kuma an sanar da ni sunaye dukka kamar yadda aka sanar da Annabi Adamu”, Imamu Dailami ya fitar da wannan Hadisi daga Abi rafi’i. Allah ya nuna wa Manzon Allah al’ummarsa, ya san kowa da komai nasa daki-daki tun kafin a halicce ta. Wannan shi ne a takaice misalan mu’ujizozin da Allah ya bai wa Annabi Adamu (AS) wadanda aka ba Annabi Muhammadu (SAW) su duka, kuma da kari a kai fiye da na Annabi Adamu (AS).

Amma game da mu’ujizozin da aka bai wa Annabi Idrisa (AS) kuwa, Allah Tabaraka wa Ta’ala ya fada mana a cikin Al’kur’ani cewa ya daga shi zuwa bigire madaukaki, “wa rafa’anahu makanan aliyyah”. Manzon Allah (SAW) ya ce ya gan shi a sama ta hudu ranar Isra’i. Wannan girma ne sosai. Amma shi kuwa Manzon Allah (SAW) Allah ya ba shi Mi’iraji. Bayan ya yi tafiya daga Makka zuwa Baitul Makdisi, sai Allah ya hau da shi sama, ya zo ma ya shige saman bakidaya. Ka ga ko da sama ta bakwai aka tsaya ai an wuce wanda yake sama ta hudu ballantana ma an shige nan aka tafi Magaryar Tikewa, ita ma Manzon Allah ya wuce ta ya tafi wurin da Allah ya ce ya kusanta har ya zamo tsakaninsa da Allah kamar baka da tsarkiya ko kuma a ce baka biyu wato “()” ko kuma da Turanci a ce “Opening bracket and close bracket). Ka ga wannan ai ya nuna abin da Allah Ta’ala ya ba Annabi Idrisu bai kai na Annabi (SAW) ba.
Amma game da Shugaba Annabi Nuhu (AS), Allah Ta’ala ya tserar da shi tare da wadanda suka yi imani ba su dulmiya a ruwa ba. A cikin Alkur’ani mai girma, Allah ya ce “sai muka tserar da shi da wadanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwa da aka take”. A nan, shi kansa Annabi Nuhu (AS) sai da aka tserar da shi kuma aka tserar da mutanensa. Amma idan aka zo janibin Annabi Muhammadu (SAW), shi a karan kansa ne Tsirar. Kamar yadda ya gabata a karatuttukanmu na baya, Allah ya ce in dai Annabi (SAW) yana cikin mutane Allah ba zai musu azaba ba. Me ya sa Allah ba zai musu azaba ba? Saboda Annabi (SAW) da ya kasance Tsira yana cikinsu. Haka nan idan Annabi (SAW) ya koma ga Allah, Allah ba zai musu azaba ba irin ta dufana ko makamancinta matukar suna Istigfari. Idan kuma zancen jirgin ruwa ne na Annabi Nuhu (AS), akwai Hadisi Ingatacce da Manzon Allah (SAW) ya ce Iyalan Gidansa Jirgin Ruwa ne na Tsira duk wanda ya hau su ya tsira. Haka nan a wani Hadisi kuma Manzon Allah (SAW) ya ce Sahabbansa Taurari ne na Shiriya duk wanda ya kama kowanne ya shiryu. Malamai suka ce tsakanin wadannan Hadisan biyu babu bugun juna, duk abu daya ake nufi. Ko ka hau jirgin ruwa na tsira idan ba ka nemi hanya da tauraro ba; za ka halaka. Masu jirgin ruwa da taurari suke aiki. Misalin wannan, idan ka hau mota ba ka kallon allunan kan hanya (Symbol) ka ga sunayen garuruwa ko tafiyarka saura kilomita nawa ka kai inda za ka, za ka bata hanya. Sahabban Manzon Allah da Iyalan Gidansa abu daya ne da Annabi ya hade su wuri daya. Mutum zai hau jirgin tsira kuma dole ya yi amfani da taurari domin gane hanya. Babu bata a wurin Iyalan Manzon Allah (SAW), babu bata a wurin Sahabbansa (SAW), haka nan a wurin Malaman Al’ummarsa (SAW). Allah ya tsare su, ya kiyaye su. In dai Malaman nan suna isar da sakon Manzon Allah (SAW) ne, Annabi ya ce su kamar Annabawan Bani Isra’ila ne. Wanda ya rike Malami zai hadu da Allah lami lafiya; in dai Malamin na Allah ne mai isar da sakon Manzon Allah.
Allah ya ba Annabi Nuhu tsira tare da mutanensa, amma shi Annabinmu, shi ne tsirar a karan kansa.
Bayan haka, Allah ya ce Annabi Nuhu (AS) ya shekara dubu ba hamsin yana kiran mutanensa su yi imani amma wadanda suka yi imani ba su fi mutum tamanin (80) ba (Akwai wani gari a Iraki sunansa Garin Mutum Tamanin). Duka wadannan mutum Tamanin din sun rasu, illa ‘ya’yan Annabi Nuhu (AS) ne suka rayu. Su ne suka haifi dukkan al’ummomin duniya tun daga lokacin zuwa yau. To a nan, ka ga Annabi Nuhu kusan shekara dubu ya yi yana kira amma mutanen da suka yi imani da shi ba su kai dari ba. Shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) cikin shekaru ‘yan kalilan ya samu dimbin mutane da suka yi imani da shi, saboda yana kira ne da wani izini na Musamman daga Allah kari a kan irin izinin da aka bai wa sauran Manzanni na kira.
Annabi (SAW) bai fara kira ba sai da ya shekara arba’in (40) a duniya, aka shekara 13 yana kira a fadi La’ila ha Illalallah a Makka, an kusa Hijira bai fi da wata shida ba Sallah ta sauka, daga nan ya koma Madina. Kwatakwata shekara goma Annabi (SAW) ya yi a Madina. Idan aka hada shekarun za ga ba su fi ishirin da uku ba yana kira. Amma a ranar Hajjin Bankwana Manzon Allah ya zo da Sahabi dubu dari da dubu ishirin da dubu hudu (124,000). Ka ga a cikin shekara ishirin da uku, Manzon Allah ya samu ninkin-ba-ninkin abin da Annabi Nuhu (AS) ya samu a cikin shekara dubu ba hamsin.
Idan kuma batun cewa Jirgin Annabi Nuhu ya hau kan ruwa ya yi tafiya kuma ga kayan mutane da dabbo a cikinsa ne, akwai hadisi da Ikrimah bin Abu Jahal suna bakin tekun Najjar ya ce ba zai yi imani da Annabi (SAW) ba har sai ya kira wancan dutsen ya taho ta kan ruwa ba tare da ya lume a ciki ba sannan ya yi imani. Manzon Allah (SAW) ishara kawai ya yi wa dutsen, dutsen ya taso ya yi tafiya a kan ruwa kuma bai lume ba a cikin ruwan har ya zo gaban Annabi (SAW) ya yi masa shaidar Manzanci. Ikrimah ya ce zai yi imani amma Annabi (SAW) ya sake ce wa dutsen ya koma mazauninsa, Manzon Allah ya sake wa dutsen ishara ya koma kuma ba tare da ya nitse a ruwa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: