Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Likitanci Da Magungunan Gargajiya Na Kasar Sin Sun Ba Da Gudunmawa Wajen Yaki Da Cutar COVID-19

Published

on

Mataimakin ministan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Xu Nanping ya bayyana a gun taron manema labarai da majalisar gudanarwa ta yi a kwanan baya cewa, Likitanci da magungunan gargajiya na kasar Sin sun bada gudunmawarsu wajen hana wadanda suka kamu da cutar COVID 19 fadawa cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.
Hukuma mai kula da likitanci da magungunan gargajiya ta kasar Sin ta bada kididdiga cewa, an baiwa wadanda suka kamu da cutar har ya kai dubu 60 magungunan gargajiya, tare da samun ci gaba a mataki-mataki, hakan ya sa, likitanci da magundunan gargajiya na kasar Sin sun kara shiga aikin bada jinya a fannoni daban-daban, har an ce, hada fasahohi da kimiyyar gargajiya ta kasar Sin da na zamani tare zai bada gudunmawa sosai wajen yaki da cutar. (Mai Fassarawa: Amina Xu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: