Connect with us

LABARAI

NILOWb Ta Yi Taro A Bauchi Don Karawa Da Maza A Zaben 2023

Published

on

kungiyar Mata ta ‘League of Women voters of Nigeria’ (NILOWb) reshen jihar Bauchi, ta gudanar da wani taron ganawa domin tattauna yanda mata za su samu iko da zarafin shiga a dama da su ta fuskacin siyasa hadi da daukaka sautinsu ta fuskacin gudanar da shugabanci a matakai daban-daban domin tabbatar da matan suna bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban kasa.
kungiyar ta sha alwashin doke maza a kujerun siyasa daban-daban a zaben 2023 da ke tafe, inda suka ce, sun sanya damba da aniyar fito-na-fito da mazaje domin su ma su kasance zababbu.
Taron ganawar wanda ya samu marawar baya daga kungiyar kasar waje ta Global Affairs Canada da kuma ActionAid; muhimman batutuwan da ganawar ya maida hankali shine yanda matan za su samu shiga ana damawa da su ta fuskacin shugabanci, wuraren aiyuka, siyasa da sauran harkokin rayuwa.
Taron wanda ya wakana a karkashin shugabar kungiyar na mata masu zabe Hajiya Fatima Zakari, a jawabinta ta ce sannu a hankali kungiyar nasu tana kara samun tagomashi wurin cimma nasara ta yanda mata a jihar Bauchi ke kasa fahimtar muhimmancin shiga a dama da su wurin gudanar da jagoranci da shugabanci.
Fatima ta shaida cewar za su bayar da mamaki a zaben da ke tafe, yana mai shaida cewar nan gaba kadan a kasar nan mata za su amshi kujeru masu daraja domin suna da tasiri wajen kyautata shugabanci na kwarai.
A karshen taron, dukkanin mahalartan sun jaddada muhimmanci da alfanun shigar mata sha’anin gudanar da shugabanci da da harkokin siyasa. A gefe guda, sun bukaci gwamnatoci kama daga jiha zuwa tarayya da su ke la’akari da irin kokari da hazakar mata gami da basu dama da zarafin shiga sha’anin mulki da shugabancin jama’a.
Sun tsaida matsayar ganin an samu karin mata da za su fito a fafata da su a babban zaben 2023 a matakai daban-daban da suka hada da majalisar jiha da na tarayya, da sauran manyan mukamai da suka yi fatan da sa’ayinsu da kokarinsu za su kai ga cimma nasarorin samun hakan a zaben 2023 da ke tafe, sais u yi kira ga mata a dukkanin fadin kasar nan da su jure dukkanin kalubale su fito a dama da su a zaben 2023 idan Allah ya kaimu.
Shugaban kungiyar matan na jihar Bauchi Hajiya Zakari, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da basu hadin kai domin su kai kungiyar mataki na gaba da taimaka wa mata su samu cimma maradinsu na shiga a dama da su kan siyasa, shugabanci da jagoranci.
Mahalarta taron ganawar sun fito daga Sarakunan gargajiya, kungiyoyin fararen hula, jami’an tsaro, da kungiyoyi masu zaman kansu da daman gaske. Fitattun mutane daga cikin kari kan wadanda suka halarci taron sun hada da, Hamlet Shugaban Shar-Shar, sakatariyar kungiyar mata ‘yan jarida reshen Bauchi NAWOJ, Aisha I. Bamai; Hajiya Hajara Salami shugaban kungiyar Action Women; Hajiya Lami Geidam wacce ta wakilci kungiyar mata musulmai FOMWAN; Abdullahi Shitu da ya wakilci kungi
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: