Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim din ‘Dawood’

Published

on

Suna: Dawood.
Labari: Dayyab Jibril MD
Kamfani: Karmatako Studio.
Shiryawa: Abdulaziz Dan Small.
Daukar Nauyi: Zahradden Karmatako.
Bada Umarni: Sunusi Oscar.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Ali Nuhu, Alhassan Kwalli, Zahradden Karmatako, Hauwa Maina, Bilkisu Shema, Rahama Nijar, A’isha Jos, Hajiya Hadiza da sauransu.
Fim din Dawood fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani attajiri mai suna Alhaji Dawood (Ali Nuhu), da Kuma matarsa Hajiya (Marigayiya Hauwa Maina), da ‘yarsa Maimuna(Bilkisu Shema) da kuma aminiyarta Aziza (Rahama Nijar).
A farkon fim din dai an hasko Aziza su na wanke-wanke tare da mahaifiyarta (Hajiya Hadiza), mahaifinta kuma wato (Alhassan Kwalli) ya na zaune a bayansu. Aziza ta zo ta same shi ta na fada masa ya kwantar da hankalinsa indai maganar rashin kudin da za ta biya na jarrabawa ne to ita ta hakura ta yi wata shekarar tundaeba su da halin biya. A haka dai ta kwantar wa da mahaifin nata hankali.
Daga nan kuma sai a ka koma gidan Alhaji Dawood su na tare da matarsa da kuma Maimuna, ta na shirin tafiya makaranta, a nan ne ta ke shaida masa cewa ‘yarsa fa wato Aziza ba ta biya kudin makaranta ba kuma gashi yau za a rufe. Sai ya fara fada ya na cewa me ya sa ba su fada masa da wuri ba, sai ya bata kudin ya ce ta kai mata su je su biya.
Ita dai Maimuna da Aziza aminai ne sosai domin sun yi sabo da junansu sosai, domin kuwa sabon nasu har ya kai ‘yan uwantaka, domin kuwa kowaccensu na zuwa gidan kowacce ta yi kwanaki. Duk da cewa Maimuna gidansu su na da kudi sosai, hakan bai taba alakarsu da Aziza ba duk da cewa gidansu ba masu kudi bane. Watarana Maimuna su ka tsara da Aziza cewa za ta dawo gidansu Maimuna da zama saboda su rage kewar juna a su ke idan su na nesa da juna. Hakan kuma a ka yi, domin Aziza ta tattaro kayanta ta dawo gidansu Maimuna da zama.
A haka dai Aziza ta ci-gaba da rayuwarta a gidansu Maimuna. Sai dai labari ya fara chanja salo ne lokacin da a aka matsa musu a kan su fito da mazajen aure, kuma gashi sun yi wa junansu alkawarin ba za su yi aure ba sai rana daya. Ita Maimuna ta na da saurayi wato (Zahradden Karmatako), ita kuma Aziza ba ta da saurayi. Da matsi ya fara yawa ne fa Aziza ta shaidawa iyayenta cewa fa ita tun tana karama ba wanda take so duk duniya ba wanda ta ke su sai baban Maimuna wato Alhaji Dawood.
Abu kamar wasa dai magana sai ta tabbata, domin kuwa kowa ya amince da maganar auren bayan sun tabbatar da gaske fa Aziza ta ke a kan abinda ta ke so. Haka dai a ka amince daga karshe a ka yi auren su Maimuna da saurayinta, da kuma na Aziza da Alhaji Dawood. Kuma su ka zauna cikin farin ciki, sai daga baya mijin Maimuna ya rasu, yayin da ita ma Aziza ta rasa ranta sakamakon haihuwa.
ABUBUWAN YABAWA
1. Fim din ya dace da sunansa.
2. Labarin bai yanke ba tun daga farkon fim din har karshensa.
3. Fim din ya samu aiki mai kyau da kwararrun ma’aikata da kuma kwararrun jarumai.
4. Babu matsalar sauti ko hoto a cikin fim din.
5. Fim din ya nuna tasirin aminci, domin da babu aminci babu yadda za a yi Maimuna da mahaifiyarta su amince Aziza ta auri Alhaji, bayan sun rike ta a matsayin ‘ya a gidansu.
KURAKURAI
1. An nuna Aziza tare da Abdul M Sharif su na tsaye su na hira, kuma ba tare da an nuna cewa Azizan tunani take ba.
2. An ji Aziza na kukan kudin jarrabawa amma kuma an ji Maimuna kuma ta na fadawa Alhaji cewa kudin makaranta za a biyawa Aziza.
3. Me ne ne hikimar mutuwar mijin Maimuna da kuma Aziza a karshen fim din?
kARkAREWA
Fim din Dawood fim ne da ya zo da labari mai jan hankali, domin kuwa abinda ya faru a cikinsa, abu ne da bai cika faruwa ba a cikin al’umma. Fim din ya samu aiki mai kyau, ya kuma samu nasarori da yawa. Kuma fim din na daya daga cikin fina-finan da su ka haskaka a cikin wannan shekarar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: