Connect with us

RAHOTANNI

Tabbatar Da Wanzuwar Sabbin Masarautu  A Kano Tare Da Yin Watsi Da karar Masu Nadin Sarakuna

Published

on

A ranar Litinin 17 ga watan Fabrairun wannan shekara ne, Kotun daukaka kara karkashin jagorancin Mai Sharia A.T Badamasi, ta kawo karshen cece-kucen da ake yi kan batun kirkirar sabbin Masarautu a Kano, wanda kamar yadda aka sani masu ruwa da tsaki wajen nadin Sarkin Kano, ke kalubalantar dokar samar da Masarautun da aka kirkira a shekarar 2019.

Mai Shari’a Badamasi dai, ya zartar da hukunci akan rokon da masu nadin Sarkin suka suka gabatar a gabansa, wanda tuni aka wuce wannan wuri, kasancewar dokar da suke bukatar sake nazarinta tuni wata Babbar Kotun, wadda Mai Shari’a U,M Na’abba, ke jagoranta ta gama da ita. Bisa wannan dalili, babu wani dalili ta kowace fuska da za a cigaba da saurari karar. Wanda hakan yasa aka yi watsi da ita kwata-kwata, sannan kasancewar dukkanin wasu dalilai zai zama an yi wa harkar shari’a illa idan aka cigaba da sauraron wannan kara, wadda ba ta da wani sauran hurumi a tsari na doka.
Idan za a iya tunawa, Mai Shari’a Na-Abba ya yanke hukunci cewa, dokar da ta
bayar da damar kafa sabbin Masarautu ta shekarar 2019, ba a cika ka’idar samar da ita ba, shi yasa masu nadin Sarakunan ke kalubalantar ta a gaban Kotunsa. Daga nan ne kuma, sai Majalisar Dokokin Jihar Kano, bisa lamuncewar doka da kuma cika dukkanin wasu matakan da suka dace, suka tabbatar da sabunta matsayin wannan doka, wadda kuma aka rattabawa hannu ta zama dokar da Gwamna Ganduje ya tabbatar da ita.
Kamar yadda al’amarin yake, ”na fahimci tawagar wadanda ke kare masu karar sun bayyana cewa, wannan wani shiryayyen al’amari ne ga Gwamnan Jihar Kano, abinda suke nufi da irin wannan bayani, bai dame mu  ba ta kowacce  hanya, amma dai duk wani mai kyakkyawan tunani, ya gamsu da wanzuwar wannan doka ta sabbin Masarautun Kano, wadda aka bi dukkanin ka’idoji, wanda kuma babu wata Kotu da za ta ga aibun wannan hukunci.
Amma duk da haka, zai zama akwai rashin sanin ya kamata idan masu nadin Sarakunan tare da tawagar Lauyoyinsu suka cigaba da tunkarar wata Kotun kan wannan batu. Domin kuwa, ga wadanda suka san shari’a, Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba su na samar da doka ga kowane bangaren na Gwamnati, ciki har da Masarautunmu na Gargajiya.”
Kamar yadda na taba bayyanawa a cikin wani rubutu da na yi a baya, domin tabbatar da kyakkyawan matsyi da kuma kokarin ciyar tsarin gaba kamar yadda duniya ta cigaba, dole a sake yi wa al’amarin duban tsanaki ta yadda lamarin zai yi daidai da cigaban tattalin arzikin da jama’a ke bukata. Donhaka, ba za mu yarda a ce abinda aka yi shekaru dubbai da suka gabata, shi kuma za a cigaba da yi a yau ba. Ya zama wajibi mu motsa, domin tafiya daidai da cigaban da duniya ke kai a halin yanzu.
Har ila yau, ina tabbacin cewa, masu kyakkyawan tunani za su aminta da ni kan cewa, kirkirar sabbin Masarautu hudu zai cigaba da samar da ingantaccen sakamako. Musamman yadda lamarin ya dakatar da yawan kwararar mutane daga Karkara zuwa Birane, sannan samun karin masu zuba jari na cikin gida da waje, wadanda su ma ke kwarara zuwa wadannan sabbi Masarautun, suke kuma zuba makudan kudade tare da samar da damammaki ga al’ummar wadannan Masarautu.
Kwanan nan wani dan kishin kasa, Honarabul Sulaiman Abdurrahaman Kawu Sumaila, ya kafa Jami’a mai zaman kanta ta farko, a karamar Hukumar Sumaila wadda ke karkashin Masarautar Gaya. Ko shakka babu, wannan mataki nasa na zuba wannan gagarumin jari a wannan yanki, ya samu karfin guiwa ne sakamakon
kirkirar wannan Masarauta ta Gaya. Shi yasa a halin yanzu jama’a ke nuna godiyarsu bisa wannan babban cigaba da wannan Jami’a za ta samar a wannan yanki.
Haka zalika a shekarar da ta gabata, zaman Majalisar Zartarwar Jihar Kano, ta amince da kashe Naira Biliyan 2,543,819,588.67, domin ginawa tare da daga darajar ayyukan lafiya a shelkwatar sabbin Masarautun Bichi, Gaya, Rano da kuma Karaye. Wannan ya hada da gina sashin kula da taimakon gaggawa, dakunan kwantar da marasa lafiya mai dauke da gadaje 22, sashin duba lafiyar ido, hakori, gashi na kashi, dakunan gwaje-gwaje, wurin adana gawarwaki da samar da hanyoyi a cikin Asibitoci da sauran makamantansu.
Buga da kari, babu wata tantama kasancewar wadannan sabbin Masarautu sun kara kima da yawa, musamman ga Matasan wadannan yankuna ta hanyar samar da tsare- tsaren dogaro da kai, batun bayar da ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa da kowa tun daga matakin Firamare har zuwa na Sakandire, tsare-tsaren bayar da tallafin karatu da sauran harkokin kyautata cigaban al’umma, wadda wannan Gwamnati ta Ganduje ta bujiro da su. Irin wannan cigaban ne jama’ar wadannan bangare ke fatan samu tsawon shekara da shekaru.
Hasali ma samar da tsare-tsaren cigaba, wanda ya mayar da Jihar Kano wani kasaitaccen Birni, su ake gani yanzu bayan kirkirar Jihar Jigawa daga tsohuwar Jihar Kano. Saboda haka, sakamakon kirkirar sabbin wadannan Masarautu guda biyar masu daraja ta daya, cigaban da aka samu a wadannan Masarautu ya wuce duk yadda ake zato. Wannan yasa aka samar da wannan tsari, bisa gagarumar bukatar tarin al’umma, wanda Gwamnatin Ganduje ta yi domin bayar da damar fadada harkokin cigaba a Jihar Kano.
Bugu da kari, domin kaucewa harbin iska, masu nadin Sarki da wadanda ke bakin ciki da kirkirar wadannan sabbin Masarautu, tun wuri ma gwara su ajiye wannan tunani nasu. Sannan na sha fada cewa, wadannan Masarautu ba wai Gwamna Gandune ya fara yin su ba, da ma suna nan illa kawai abinda Gwamna ya yi shi ne, samar da kariyar doka domin cika burin al’umma.
Har wa yau, kirkirar sabbin Masarautu a Jihar Kano, ba an yi su ne kawai domin  wani yunkurin rage kimar kyakkyawan tarihi da al’adunsu ba, sai dai kawai an yi su ne domin kara jaddada kyakkyawan tarihi da kuma bukatar kai cigaba kai tsaye zuwa ga al’umma.
Sannan, Kotu ta tabbatar da su sakamakon al’amari ne na doka da kuma cika ka’ida. Kasancewarsa jagora mai bin doka da oda, Gwamna Ganduje ba shi wani iko na mayar da hannun agogo baya, bisa kirkira tare da samar da Masarautun  Bichi, Karaye, Rano da kuma Gaya.
A tawa fahimtar, Gwamna Ganduje ba shi da wata mummunar manufa akan mai
Martaba Sarkin Kano, Muhamamdu Sanusi II, domin kuwa a koda-yaushe yana tabbatar da kyakkyawar dangantaka da Sarkin, kuma ya yi hakan ne da kyakkyawar niyya. Shi yasa bisa girmamawa, Gwamna Ganduje ya nada Sarkin na Kano a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Kano, domin sake girmama shi.
Saboda haka, mun yi zaton Sarkin zai yi amfani da wannan matsayi nasa na Shugaban Majalisar Sarakuna, domin tabbatar da cigaban Jihar Kano, mun yi zaton Sarki Sunusi zai tabbatar da gudanar da zaman farko na Majalisar Sarakunan ta
hanyar yin amfani da kwarewa domin nuna kyakkyawan jagoranci.
Babu wani amfani a ciki, domin kuwa yadda wadannan sabbin Sarakuna guda hudun masu daraja ta daya ke mutunta shi, wanda kuma a koda-yaushe a shirye suke domin yin aiki tare da shi. Kasancewarsa na Uba, yanzu ya kamata Sarki Sanusi ya nuna gaskiyar daidaito, ya kuma yi biyayya ga dokar domin tabbatar da nutsuwa a Jihar Kano.
Ko shakka babu, Gwaman Ganduje ya nuna hakuri kwarai da gaske wajen baiwa Sarki Sanusi isasshen lokaci, domin sake yin tunani tare da kyale gaskiya ta yi halinta. Ba na zaton idan Gwamnati za ta cigaba da jira wajen mutunta wadannan sabbin Masarautu, ba tare da aiwatar da wannan sabuwar doka ba.
Wakazalika, babu wani abu da zai damu Gwamna Ganduje a cikin wannan al’amari. Domin kuwa, wannan abu da ya yi shi ne zai cika buri tare da fatan
daga Kano zuwa mataki na gaba. Sannan, a duk inda aka samu cikakken zaman
lafiya dole ne a kuma samu cigaba. Wannan ce tasa ya zama wajibi dukkanninmu mu ajiye wani banbance-banbancen da ke tsakaninmu mu hada hannu da Gwamna Ganduje a kokarin da yake yi na sake fasalin Jihar Kano zuwa wani kasaitaccen Birni. Malam Muhammad Garba ne, ya rubuta Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labaran Jihar Kano.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: