Connect with us

LABARAI

Za Mu Yi Aiki Don Bunkasa Lafiyar Al’ummar Jihar Kano

Published

on

Shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano.Kwamred Nura Haruna Rimin gado yaci alwashin yin aiki tukuru wajen tabbatarda kare muradun ya’yan kungiyar ya bayyana haka ne da yake zantawa sa manema labarai bayan an zabe shi a matsayin sabon shugaban kungiyar.
Rimin gado ya gode wa Allah da dukkan masu ruwa da tsaki na kungiyar a kasa da jihar Kano da matakin kananan hukumomi bisa goyon baya da suka bashi na samun nasara ya ce, za su yi aiki tare da duk wadanda aka zaba dan sauke nauyi.
Kwamared Nura Haruna Rimin gado ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa irin ayyuka da yake gudanarwa wajen bunkasa cigaban lafiya a jihar Kano da kuma taimakawa cigaban ma’aikatan lafiya.Kulawa da harkar lafiyar na saukakawa mutane masu karamin karfi su amfana.
Shugaban kungiyar na ma’aikatan lafiya yaja hankalin ma’aikatan lafiya na jihar su rika aikinsu tsakani da Allah hakan zai anfanar da cigaban al’umma. Sannan kuma kungiya zata tsaya wajen kare hakkinsu da mutuncinsu.
Ya yi nuni da cewa a matsayinsa na wanda ya dade yana dawainiya a zababbun matakan shugabancin kungiyar daban-daban yasan tafiya rda kungiyar da manufofinta za su yi aiki da shawarwari da kuma tuntuba na masana masu kwarewa domin cigaban lafiya a Kano.
Kwamared Nura Haruna Rimin gado yace burinsa shi ne yaga dukkan ma’aikatan lafiya sun sami hakkinsu da doka ta tana da da kare musu mutunci da hakan zai tabbata da irin hadin-kai da goyon bayansu a gare shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: