Connect with us

RIGAR 'YANCI

Buhari Ya dauki Kyari Tamkar Mataimakin Shugaban kasa – Tsohon Sarkin Gwandu

Published

on

Tsohon Sarkin Gwandu, Manjo Janar Mustapha Haruna Jokolo (mai ritaya), ya yi zargin cewa, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya dauki shugaban maíaikatan fadarsa Abba Kyari, a matsayin mataimakin shugaban kasa ne.

Jokolo yana fadin hakan ne saíilin da yake fadin albarkacin bakinsa a kan takun sakar da a ke yi a tsakanin mai baiwa shugaban kasan shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, da kuma Abba Kyari, a kan yanayin tafiyar da harkokin tsaron kasar.
Jokolo ya nemi Buhari da ya sauke dukkaninsu biyun bisa zargin su da ya yi da son nuna iko da kuma son kai a wajen aiwatar da ayyukan nasu.
Tsohon dogarin na shugaba Buhari a zamanin mulkin soja, ya yi wadannan bayanan ne lokacin da ake zantawa da shi cikin wani shirin gidan rediyo a Kaduna.
Jokolo ya tunasar da Kyari da kuma Monguno da su sani cewa Nijeriya tana saman kowa ne, don haka ya kamata su san da cewa kuma idon alíumma yana kansu.
Jokolo ya ce: ìTakun sakar da ake yi a tsakanin mutanan biyu ta samo asali ne daga kokarin su na son nuna isa da kuma son kai, domin a cewar sa, in ba haka ba, mutanan biyu ai ëyaníuwan juna ne. Dukkanin su Musulmai ne, daga kuma kabila guda. Shugaba Buhari ya kawo su ne domin su taimaka masa ta fannoni mabambanta, don haka me ya sa suke yin sabani a kan aikin na su?
ìTabbas, Janar Monguno ya koka, amma bai kai kukan na shi wajen da ya dace ba, kamata ya yi ya rubuta kukan na shi ne kai tsaye zuwa ga Shugaban kasa Buhari, a kan abin da shugaban maíaikatan fadar na shi yake yi masa. Saboda kuwa Shugaba Buhari kamar ya dauki shugaban maíaikatan fadar na shi ne a matsayin mataimakin shugaban kasa.
ìBuhari da kansa ne ya ce duk wani abu a yi shi ta hannun shugaban maíaikatan na shi, wanda wannan yana nufin Buhari ya ba shi iko ne marar adadi, don haka yana iya yin komai. Amma dai hakan ba daidai ne ba.î
Idan dai ba a manta ba, wata wasika da ta bullo daga Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, ta yi zargin cewa Kyari ya yi kaka-gida a kan tafiyar da harkokin tsaron Nijeriya.
Cikin wasikar, Monguno ya yi zargin cewa, shugaban maíaikatan fadar ta shigaban kasa ya ajiye shi a gefe wajen yanke shawarwari a kan abin da ya shafi tsaron kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: