Connect with us

LABARAI

Shugaban NIS Ya Garzaya Ma’aikatar Harkokin Waje Domin Samun Nasarar Sabuwar Bizar Nijeriya

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede ya garzaya Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Nijeriya domin kara tattaunawa a kan yadda za a aiwatar da sabon tsarin bizar Nijeriya na shekarar 2020, a ofisoshin jakandancin kasar da ke kasashen waje.

Taron wanda ya gudana tare da manyan mahukuntan ma’aikatar kamar Karamin Ministan Harkokin Waje, Jakada Zubairu Dada, Babban Sakataren Ma’aikatar, Jakada Sulaiman Mustapha Lawal da sauran Daraktoci, ya zurfafa tattaunawa a kan ka’idoji da matakan bayar da sabon bizar, da saka ihsanin da wasu kasashe suke wa Nijeriya da sauransu. Wakazalika, taron ya tabo bukatar yaukaka zumunci a tsakanin jami’an difilomasiyya da Nijeriya bisa la’akari da tsare-tsare da manufofin gwamnati da suka jibanci bangaren shige da fice da kuma difilomasiyya.

A jawabinsa, Shugaban NIS, Muhammad Babandede ya bayyana cewa, Ma’aikatar Harkokin Waje babban jigo ce wajen tabbatar da samun nasarar aiwatar da sabon tsarin bizar na Nijeriya na 2020, domin shiga sahun cigaban da ake samu na dunkulewar duniya wuri guda, da kuma samun bizar da zai taimaka wa yaye damuwar ‘Yan Nijeriya ta fuskar shige da fice da kawo wa kasar abubuwan da za su kara mata albarka.

Shi kuwa a nashi bangaren, Karamin Ministan Harkokin Wajen, Jakada Zubairu Dada, yayin da yake nuna muhimmancin bukatar duba sahihiyar hanyar difilomasiyya wajen warware batutuwan da suka shafi sha’anin biza da saka ihsanin da ake yi idan hakan ta taso a inda ake wa ‘Yan Nijeriya ba dai-dai ba, ya taya Shugaban NIS Babandede murnar wannan gagarumin aiki da ya gudanar wanda zai taimaka wa habaka tattalin arziki, bunkasa walwala da zuba jari a cikin kasa, ta hanyar samar da matakan biza dai-da-dai har 79 domin cimma muradun mutanen da suke son shigowa Nijeriya.

A jawabinsa, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen, Jakada Sulaiman Mustapha Lawal, ya jinjina wa Shugaban NIS Babandede bisa kawo mafita ga sassan da suka shafi ma’aikatar da jami’anta kai-tsaye a cikin gida da waje, kana ya tabbatar da samun hadin kai da goyon baya a kan dukkan batutuwan da ke bukatar a yi musu taron dangi wajen warwarewa.

Jami’in yada labarai na NIS, DCI Sunday James ya fitar da sanarwar manema labarai a karshen taron wanda LEADERSHIP A Yau ta sami kwafi daga wurinsa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: