Connect with us

RA'AYINMU

Tsaro: Akwai Bukatar Sake Zage Damtse

Published

on

A kwanan nan ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kasha mutane guda 48 ciki har da ma’aikatan kamfanin NNPC a wajen hakar mai fetur da ke yankin Lake Chad Basi. Wannan ma ban da wadanda su ke kashe wa a kullum musamman ma a babban hanyan Maiduguri zuwa Damaturu.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe Dala miliyan 2.6 domin dakile matsalolin Boko Haram.

Da ya ke bayani a wajen wani taro a Washington D.C na kasar Amerika, shugaban ma’aikatan tsaro na Nijeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonishaki, ya bayyana cewa, “gwamnatin Nijeriya ta kashe sama da dala miliyan 2.6 a shekarar 2016, domin gyara barnar da mayakan Boko Haram suka yi a wasu yankuna.”

Ya kara da cewa, “mafi yawancin mutanen da su ke wannan taro sun tallafa ma na wajen dakile lamarin. Hadin kai shi ne ya fi muhimmanci.”

Idan a ka canza Dala miliyan 2.6 zuwa Naira zai kai tiriliyoyi masu yawa, wanda masana tattalin arziki suka bayyana cewa, wannan kuda za a iya rage radadin talauci a Nijeriya. Amma dai ba kudi ba ne masu yawa idan aka gwatanta irin barnar da mayakan Boko Haram suke yi, a kowani kasafin kudi na shekara wanda a ke ware naira tiriliyon, a na ware kudade masu yawa ta harkar tsaro saboda mayakan Boko haram.

Wata kungiya mai suna Network of Cibil Society Organisations, NECSO, ta bayar da rahoto cewa, an kashe ‘yan Nijeriya sama da mutum 25,000 tun lokacin da rikicin Boko Haram ya barke a Nijeriya. Sannan an raba mutum miliyan 2.15 da gidajensu sakamakon wannan rikici da ya barke a yankin Arewa- maso Gabashin Nijeriya. Haka kuma an bayar da wannan adadi a wajen babban taron majalisar dinkin duniya.

Hakazalika, jami’an kungiyar malamai na Nijeriya (NUT) ta bayyana cewa, ‘yan ta’adda sun halaka sama da malamai 600, sannan 19,000 an raba su da matsuguninsu a yankin Arewa. Kaungiyar ta bayar da bayanan farmakin da aka kai kamar haka an samu guda 308 a Jihar Borno, an samu 75 a Jihar Adamawa, an samu 18 a Jihar Yobe, an samu 25 a Jihar Kaduna, an samu 120 a Jihar Filato, an samu 63 a Jihar Kano, an samu guda 2 a Jihar Gombe.

Idan a ka duba wadannan alkaluma za a ga cewa, mayakan nan su na da hatsari kuma makiyan kasar nan ne, domin a na ta barnatar da dukiyar kasa a kan barnar da su ke yi. Amma dai daga bayanan da shugaban ma’aikatan tsaro akwai alamar tambaya a kan yadda ake yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewacin Nijeriya.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa, ta karya lagon mayakar Boko Haram tare da sauran kunyiyoyin ‘yan ta’adda ta ke kai farmaki a Jihar Borno. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa a cikin kwanan nan ya zargi shugabannin gargajiya kan ba sa aiki yadda ya kamata wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Ra’ayin wannan jarida dai shi ne, akwai bukatar a kara daukan wasu matakai wajen yaki da masu tayar da kayan baya a Nijeriya.

Mu na kira ga gwamnati da ta kafa dokar tabaci a yankunan da ke fama da rikice-rikice, domin samun karfin lakile lamarin yadda ya kamata. Ba sai dole an cire gwamna ba za a iya bin wasu matakai.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kokarin hakan. Ya kamata gwamnati ta kara ta shi tsaye wajen kare rayukan mutane a hijohin da ke fama da rashin tsaro.

Haka kuma, muna bukatan gwamnati da sojoji su canya hanyoyin yadda su ke yaki da wadannan ‘yan ta’adda, sannan a yi wa jami’an sojojin garanbawul ta yadda za a kawo kan lamarin gabadaya.

Akwai bukatar a bai wa sojojin da ke fagen yaki horo ta musammam tare da kayan aiki da kuma ba su hakkokinsu yadda ya kamata, domin tukarar masu kai farmaki.

An yi asarar sojoji da dama a wannan shekara wanda ba a san adadinsu ba kuma wadannan sojoji da su ka mutu a fagen yaki ba tallafa wa iyalansu.

Akwai maganganu bayan an kwato dajin Sambisa da shalkwatan masu tayar da kayar baya da ‘yan matan Chibok. ‘Yan Nijeriya sun bayyana cewa, mayakan Boko Haram sun shiga cikin sojoji da wasu kungiyoyi masu kwantar da tarzoma, akwai bukatar a bincikja su na ciki ko ba sa ciki.

Duk da sake dawowar masu tayar da kayan baya, akwai bukatar a san yadda a ke rarraba kayayyaki da kuma yadda gwamnati ke kashe kudade wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda, domin kar a samu damfara a cikinsa, kamar yadda gwamnatin shugaba Buhari ta yi wajen shigo da kungiyoyin masu yaki da cin hanci cikin lamarin. A ra’ayinmu, yadda ake gudanar da yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram akwai alamar tambaya, yana da kyau a samu hadin kai a tsanin sashen jami’an tsaro masu fasaha da ‘yan siyasa da kuma manyen jami’an gwamnati wajen dakile wannan lamari.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: