Connect with us

LABARAI

Bidiyon Zargin Jami’anmu Sun Yi Kokarin Karbar Na Goro A Wurin ‘Yar Switzerland Karya Ne, In Ji NIS

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya su yi watsi da wani hoton bidiyo da wasu ‘yan baranda ke wallafawa a shafin Youtube, inda a ciki ake zargin jami’an hukumar ta NIS da kokarin karbar na goro a hannun wata ‘Yar Switzerland.

A wata sanarwar manema labarai da shugaban na NIS ya fitar ta hannun jami’in yada labaran hukumar DCI Sunday James, ta bayanin cewa tun a shekarar 2017 aka fara wallafa hoton bidiyon.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “an jawo hankalin Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede game da wani hoton bidiyo da aka sake wallafawa na wata mace ‘Yar Kasar Switzerland, Kibacho, inda a ciki take zargin jami’an kula da shige da fice sun nemi su kwakule kudi a hannunta a tashar filin jirgin saman Legas.

“Wannan bidiyon da farko an fara wallafa shi ne a shafin Youtube ranar 1 ga watan Satumban 2017, an yi masa suna da “Swiss Lady Vs Nigeria Immigration” ma’ana “Tsakanin ‘Yar Kasar Swiss da Hukumar Kula da Shige da Ficen Nijeriya” kuma ba tare da wani bata lokaci ba aka bincika lamarin aka gano abin karya ne. A ranar 5 ga Fabarairun 2019 bidiyon ya sake bayyana tare da sunan “Swiss Woman Exposes Sharp Practices Of Nigerian Immigration Officials At Airport, ma’ana ‘Yar Kasar Swiss ta tona asirin kumbiya-kumbiyar jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya a filin jirgin sama”.

Shugaban NIS, ya sake jaddada kira ga ‘Yan Nijeriya su yi watsi da bidiyon wanda aka sake wallafawa, kana ya bukace su a koyaushe su rika kai rahoton duk wani abu da suka ga ana yi da gaske ba shaci-fadi ba ga hukumar ta sahihan hanyoyin sadarwarta da suka hada da: Lambar waya 07080607900, ko adireshinta na shafin intanet nis.servicom@nigeriaimmigration.gov.ng, ko a @nigimmigration da kuma shafin nis.pro@immigration.gov.ng.

 

 

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: