Connect with us

LABARAI

Kafa Kungiyoyin Matasa Zai Kawo Karshen Rikicin Makiyaya Da Manoma – Ardo Kogi

Published

on

Domin ganin an kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da kuma manoma da yaki ci yaki cinyewa,wanda hakan ya kai ga asarar rayuka da kuma dukiyoyi ne, ya sa a ka kawo shawarar kafa kungiyoyin matasa Fulani makiyaya da zummar shawo kan matsalar.

Sarkin Fulani (Ardo) na karamar hukumar Lokoja, wanda har ila yau shi ne Ardon ardodin jihar Kogi bakidaya, Alhaji Abubakar Muhammed Duni, ne ya bada shawarar a yayin da ya ke hira da wakilin LEADERSHIP A YAU jiya a birnin Lokoja.

Alhaji Abubakar Muhammed Duni ya ce, kafa kungiyoyin Fulani makiyayan ya na da muhimmancin gaske ganin cewa a lokuta da dama a na zargin matasan fulani makiyaya da kai hari ga manoma a al’ummomi dabam dabam, wanda a cewarsa, idan ma zargin gaskiya ne, to kenan kafa kungiyoyin matasan zai shawo kan lamarin, domin kuwa kungiyoyin za su iya gano wadanda me da hannu wajen kai harin Idan har su na cikinsu.

Ardon Fulanin, wanda ya kara da cewa, al’ummar Fulani mutane ne masu son zaman lafiya a duk inda su ka tsinci kansu, ya ce, tunda a ka nada shi a matsayin Ardon Fulanin karamar hukumar Lokoja, bai samu rahoton tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da masu masaukinsu a karamar hukumar ba.

Ardon Abubakar Duni zalika ya roki gwamnati  a matsayinta na hukuma da ta dullo da wata tsari da zai samarwa makiyaya Fulani wuraren kiwon dabbobinsu ba tare da sun rika kai ruwa rana da manoma ba. Ardon ya kuma yaba wa Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a bisa a kokarinsa na samar da tsaro a duk fadin jihar, sannan ya nanata samun goyon bayansa da na sauran al’ummar Fulani da ke fadin jihar.

Alhaji Abubakar Muhammed Duni wanda Mai Martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi ya nada a matsayin Ardon Fulanin karamar hukumar Lokoja a watan Satumbar 2019, saboda cancantarsa ya gode wa Sarkin na Lokoja a bisa nauyin da ya dora ma sa, sannan ya yi alkawarin ganin ya bai wa mara da kunya.

A karshe kuma Ardon na Fulani ya bayyana karamar hukumar Lokoja a matsayin karamar hukumar da ke kan gaba wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: