Connect with us

LABARAI

PDP Ta Koma Kotun Koli… Neman Cire Buhari, Ganduje, Masari Da El-Rufai

Published

on

  • Rashin Aikin Yi Ne, Cewar APC

A ranar Litinin ne Jam’iyyar adawa a Nijeriya ta PDP ta ce, za ta koma Kotun Koli, domin neman kotun ta canza hukuncin da ta yi a kan zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin jam’aiyya mai mulki ta APC.

Babbar Jam’iyyar hamayyar ta kuma ce za ta kalubalanci hukuncin da Kotun Kolin ta yi a inda ta tabbatar da zaben Gwamnoni Nasir El-Rufai (Kaduna), Abdulahi Ganduje (Kano), Aminu Masari (Katsina) da Adegboyega Oyetola (Osun) – wadanda dukkaninsu na Jam’iyyar APC ne.

Amma Jam’iyyar ta APC ta yi watsi da wannan yunkurin na Jam’iyyar hamayyar inda ta kwatanta hakan da cewa, “ba abin mamaki ne ba,” Jam’iyyar ta APC ta kara da cewa, Jam’iyyar ta hamayya ta PDP taro ne na mutane marasa aikin yi, wadanda ya kamata su yi tunanin koma wa aiki a gonakin shinkafa.

Mai magana da yawun Jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbodiyan, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa, jam’iyyar za ta nemi Kotun Kolin ce da ta warware hukuncin da ta yi a baya.

PDP ta ce: “Kwamitin zartaswar jam’iyyarmu ya tattauna sosai a bisa da yanda Jam’iyyar APC ke tafiyar da lamurranta, inda PDP ta ga ba ta da wani zabi face ta koma kotun domin ta sake duba hukuncin da ta yi a kan zaben shugaban kasa, inda batun gabatar da takardar shaida ta bogi ta tabbata a kan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar ta APC.

“Hakan ma maganar ta ke a hukuncin da a ka yi a zaben Gwamna na Jihar Katsina, inda a can din ma lauyoyi su ka tabbatar da an gabatar da takardar shaidar bogi.

“Sannan kuma za mu nemi kotun kolin da ta sake duba hukuncin da ta yi a kan zabukan gwamnonin Jihohin Kano, Kaduna da Katsina, a bisa kasantuwar tashin rigingimu da kuma saba dokokin zabe.

“Za kuma mu nemi kotun kolin da ta sake duba hukuncin da ta yi a zaben gwamnan Jihar Osun, wanda ya gudana tare da saba wa dokokin zabe.”

Jam’iyyar ta PDP tana zargin Jam’iyyar ta APC ne da makancewa a kokarin da ta ke yin a ganin ko ta halin kaka ta tilasta wa kotun kolin a bisa hukuncin da kotun ta yi a kan Jihohin Zamfara da Bayelsa, wadanda duk na Jam’iyyar ta PDP ne.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: