Connect with us

RAHOTANNI

An Kama Wata Da Laifin Yin Garkuwa Da Mahaifiyar Kawarta A Nasarawa

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta sanar da kama wata mata ’yar shekara 29 mai suna Paulina Santos, wacce ta hada baki da wasu miyagun mutane su ka yi garkuwa da mahaifiyar kawarta.

Kamar yadda labari ya tabbata cewa, mijin kawar Paulina ma’aikaci ne a kamfanin man fetir na Najeriya, wato NNPC, a yayin da ’yan sanda su ka yi holen Paulina a babban ofishinsu da ke garin Lafiya, babban birnin jihar ta Nasarawa, inda Kwamishinan ’yan sanda, Mista Bola Longe, ne ya yi wa manema labarai wannan jawabi.

Kwamishinan Longe ya ce, a ranar 11 ga Fabrairu su ka kama Paulina Santos, kwararrun jami’an ’yan sanda daga sashen yaki da sata tare da garkuwa da mutane ne su ka yi nasarar cafke ta.

Babban dan sandan ya ce, Paulina, wacce ta fito daga karamar hukumar Ogbadigbo ta jihar Benuwe, ta na zaune ne a unguwar Azuba Bashayi cikin karamar hukumar Lafiya a yankin raya kasa na Arewacin Lafia da ke Jihar Nassarawa kuma ta na aiki da wata cibiyar karbar magani.

“Wacce a ke zargi ta hada kai da wasu miyagu ne, domin sace matar, kuma tuni ta amsa laifinta, mu kuma za mu gurfanar da ita gaban kotu da zarar mun kammala gudanar da bincike,” in ji shi.

Ita ma Paulina ta bayyana wa manema labarai cewa ta aikata laifin, amma ta na neman gafara a kan cewa ba za ta sake aikata irin wannan aika-aika ba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: