Connect with us

RIGAR 'YANCI

Buhari Zai Gina Masaka A Funtuwa Don Magance Shigo Da Tufafi Nijeriya

Published

on

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari za ta gina katafariyar masaka a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina, domin magance matsalar shigowa da tufafin sanyawa daga kasashen ketare da kuma inganta harkokin noman auduga a jihar Katsina dama kasa baki daya.

Karamar Minista a Ma’aikatar Masana’antu da Zuba Jari ta Tarayya Nijeriya, Hajiya Maryam Yalwaji Katagum, ce ta bayyana haka jim kadan bayan kammala wata ganawa da ta yi da jami’an gwamnatin jihar Katsina a gidan gwamnati da ke Katsina, karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu.

Hajia Maryam Katagum ta wara da cewa, “wannan Masaka da a ke niyyar fara ginawa a shekara mai zuwa, wato 2021, na cikin ayyukan da majalisar kasa ta amince a gina guda shidda a duk fadin kasar nan.

Ministan ta cigaba da cewa jami’an maaikatar ta da kuma na Gwamnatin Jihar sun duba fili mai tsawon kadada dari da arbain da Gwamnatin Jihar ta bada domin fara aikin gina wannan Masaka. Saboda Muna son maido da martabar shuka auduga da kuma samun masu zuba hannun jari domin sarrafa ta, kuma tuni ma’aikatar masanaantu da zuba jari ta fara tattaunawa da masu zuba jari da manyan manoma a kokarinta na nemo masu zuba jari a wannan Masaka ta Funtua.

Hajia Maryam Katagum ta ce jami’an maaikatar sun je rangadi a Funtua, domin yin nazari yadda zaa gina masakar da yadda zaa shigo da manoma da kuma yan kasuwa cikin harkar tafiyar da masana’antar.

Shima da yake na shi jawabi mataimakin Gwamna jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu Wanda shi ya jagorancin tattaunawar da jami’an maaikatar masanaantu ya ce yanzu haka Gwamnatin Jihar Katsina ta bada fili mai girman murabba’i dari da arbain. Kuma idan aka kammala gina wannan masakar za ta taimaka wajen habbaka tattalin arzikin jihohin da ke shiyyar arewa maso yamma, musamman jihar Katsina da ta yi fice wajen noman auduga.

Shi kuwa babban Sakatare a ma’aikatar masanaantu da zuba jari ta kasa Dr. Nasiru Sani Gwarzo ya ce idan aka kammala gina wannan Katafariyar Masaka za ta bunkasa rayuwar manoma 800,000 a arewacin Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: