Connect with us

LABARAI

Dalilin Karin Farashin Doya, Tumatir Da Sauransu – Hukumar Kididdiga

Published

on

Hukumar kula da Kididdiga ta kasa NBS, ta fayyace dalilin da ya sanya aka samu karin hauhawar farashin mai, nama mai kitse, kifi, tumatir, doya biredi da suran su a cikkn kasar nan.

Hukumar a cikin wani rahoton data gitar ta sanar da cewa, an samu karin hauhawar farashin mai, nama mai kitse, kifi, tumatir, doya biredi da suran su.

Har ila yau, hukumar tabkuma sanar da cewa, tsadar rayuwa ta karu daga kashi 11.98 a ciikn a watan Disamba, zuwa kashi 12.13 cikin dari cikin watan Janairu.

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin wani rahoton data fitar, inda ta kara da cewa, ta ce ta na auna tsadar rayuwar ce da hauhawar farashin kayayyaki.

Hukumar ta ce daga Disamba zuwa Janairu, kusan kowane nau’in kayan masarufi sai da ya fuskanci karin farashi.

A cewar hukumar, tashin gwaron zabon da kayan masarufi suka rika yi daha watan Janariru 2019 zuwa Disamba, 2019, ya kai kashi 11.83 a cikin dari, amma kuma zuwa Janairu sai da ya kai 11.98 bisa dari.

Kididdigar ta ci gaba da bayyana cewa tsadar rayuwa a birni ta kai gejin kashi 12.78% a watan Janairu, sai dai, kafin nan, a Janairu ba ta wuce kashi 12.62a cikin dari ba.

A cikin yankunan karkara kuwa, tsadar rayuwa ta tashi daga kashi 11.41% a watan Disamba, zuwa kashi 11.54 cikin Janairu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: