Connect with us

NOMA

Gwamna Ganduje Ya Kaddamar Da Aikin Bunkasa Noma Na Dala Miliyan 95

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a hukumance ya kaddamar da aikin noma na hukumar bunkasa aikin noma ta (KSADP) da ya kai na dala miliyan 95.

Ganduje ya sanar da hakan ne a yayin taron kaddamarwar da ya guda a otel din Tahir Guest Palace dake a cikin jihar Kano, inda ya byyana cewa, manufar aikin shine, don a kara samar da abinci mai yawa da kuma bunkasa fannin aikin noma a jihar, inda kuma za’a dinga samar da kayan aikin noma, bayar da bashi ga manoma, samar da kasuwa da kuma tura amfanin gona zuwa kaauwanni.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, bankin Musulunchi na IDB da kuma shirin Gidauniyar (LLF), da kuma sauran kungiyoyi ne zasu zuba kudi a cikin aikin.

A cewar Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, har ila yau, manufar aikin shine, ana sa ran za’a wanzar dashi har zuwa tsawon shekaru biyar, inda ya kara da cewa, ana kuma sa ran, ahirin zai taimaka wajen rage talauci, karfafa samar da abinci mai yawa a jihar ta Kano wadda ita ce take akan gaba wajen yawan alumma a kasar nan.

Ganduje ya kara da cewa, hukumar ta KSADP zata kuma taimaka wajen magance yawan rikici a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya a jihar.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, ina da imanin cewa, irin wadannan ayyukan ne kawaibzasu kawo karshen rikici a tsakanain manoma da Fulani Makiyaya, kara samar da fanin gona mai dimbin yawa, habaka kiwo ta hanyar rungimar yin amfani da hanya ta zamani da kuma karfafawa kananan manoma gwaiwa a jihar.

A cewar Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje aikin zai kuma taimaka wajen kara samar da madara da Fulani Makiyaya ke samarwa da kuma sarrafa madarar ingantacciya.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, mun yi amannar cewa, aikin zai taimaka matuka wajen magance yawan rikice-rikicen dake aukuwa a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya a jihar, inda kuma Gandujeya kara da cewa, mun yake shawarar samar da wuraren da za’a kafa Ruga a Dazuzzukan mu kamar na Dansoshiya ta hanyar taimakon aikin na bankin IDB.

A cewarsa, na fahimci cewa koda yake wannan aikin na Kasuwar garin Dawanau ta kasa da kasa da ake sayar da hatsi, ta kasance babbar Kasuwa ce a Afrika ta Yamma wadda kuma za’a daga matsayin ta hanyar samar da kayan aiki na zamani.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa, hakan yana daya daga cikkn kudurin mu na habaka fannin aikin gona, kara samar da abinci mai yawa da kuma samar da kasuwa ga manoman mu.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kuma bayar da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta tabbatar da an fitar da nata kudin na daukin dala miliyan 5 dain wanzar da aikin a cikin nasara

A nasa jawabin tunda farko, Manajan Bankin na IDB reshen Mista Mayoro Niang ya sanar da cewa, aikin yana daya daga cikin shirin shugaban Bankin na shekara biyar da zai hada kai da kuma shirin Gwamnatin Tarayya na farfado da tattalin arziki da rage talauci EEPRS.

Manajan Bankin na IDB reshen Mista Mayoro Niang ya ce, wannan aikin na tsawon ahekaru biyar, zai taimaka matuka wajwn kara samar da abinci mai yawa da kuma rage talauci ga dimbin alummar jihar Kano.

Da ya ke yin tsokaci kan taron Manajan Bankin na IDB reshen Mista Mayoro Niang ya ya sanar da cewa, an ahirya shine bisa nufin gudanar da aiki mai inganci da kuma kara wayar da kan mahalarta taron kan aikin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: