Connect with us

LABARAI

Gwamnan Abiya Ya Zama Sabon Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

Published

on

Gwamnan Abiya Ya Zama Sabon Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu ya zama sabon mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin PDP bayan da jam’iyyar ta shi ta ayyana shi a matsayin haka.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal shi ne ya tabbatar da haka a yayin da yake ganawa da manema labarai a karshen zaman da suka yi a ranar Laraba a Abuja. Inda ya ce Ikpeazu an zabe shi a matsayin wanda zai rike mukamin mataimaki a kungiyar.

Tambuwal ya ce zaman wanda kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya shirya, sun tattauna ne kan yadda za su ci gabantar da jam’iyyarsu dama kasa baki daya.

Daga cikin wadanda suka samu halarta zaman sun hada da; gwamnonin Akwa Ibom, Abia, Bayelsa, Delta, Bauchi, Taraba, Adamawa da Sakkwato.

Sauran sun hada da shugaban jam’iyyar Uche Secondus da kuma Sakataren jam’iyyar Sanata Ibrahim Tsauri.

 

Secondus ya ce kwamitin gudanarwa na PDP sun halarci zaman ne domin tattaunawa da gwamnonin dangane da batutuwan da suka shafi kasa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: