Connect with us

NOMA

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Biliyan N6.9 Don Inganta Noman Rani A Shonga

Published

on

Wani Kwamitin zartarwa dake a karkashin Gwamnatin Tarayya ya sanar da cewa, gwamnatin ta amince ta kara naira biliyan 6.9 akan naira biliyan 3.263 domin samun isassun kudaden kammala ayyukan inganta noman rani da aka fara a yankin Shonga dake a cikin jihar a Kwara.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu a yayin da ya tattauna da manema labarai a babban birintarayyar Abuja jim kadanda kammala taron kwamitin.

A cewar Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu, an fara ayyukan inganta aiyukkan noma a yankin na Shonga tun a shekarar 2010 da naira biliyan 3.263 domin kammala aikin amma sai aiki ya tsaya.

Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu ya ci gaba da cewa, ma’aikatar ruwa ta gano ci gaban da wannan aiki zai kawo wa kasa Nijeriya idan da an kammla wannan hakan ya sa ma’aikatar ta dawo da maganar a taron kwamitin zantaswa ta kasa.

Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu ya kara da cewa, mun kara yawan filin da za a yi amfani da su wajen noman rani daga hekta 1500 zuwa 2,300 sannan mun canja tsarin amfani da janareta zuwa amfani da na’uran wutan lantarki dake amfani da rana.

Ministan Admu Suleiman ya ce, “ Mun kara yawan filin da za a yi amfani da su wajen noman rani daga hekta 1500 zuwa 2,300 sannan mun canja tsarin amfani da janareta zuwa amfani da na’uran wutan lantarki dake amfani da rana.”

A cewar Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu, wadannan canje-canjen da suka yi zai taimaka wa kasa wajen cimma burinta na inganta rayukan mutanen a kasar nan da hakan ya sa gwamnati ta kara naira biliyan 6.9 akan ayyukan da za ayi.

Ya ce, “wadannan canje-canjen da suka yi zai taimaka wa kasa wajen cimma burinta na inganta rayukan mutanen a kasar nan da hakan ya sa gwamnati ta kara naira biliyan 6.9 akan ayyukan da za a yi.”

Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu Adamu yace za a kammala wannan ayyuka ne a cikin watanni 36, inda kuma Ministan Ma’aikatar ruwa Alhaji Suleiman Adamu ya ce ma’aikatar ruwa za ta yi amfani da hekta 1.8 domin noman rani a kasar nan sannan tana shirin samun goyan bayan hukumomi masu zaman kansu domin a hada hannu a ga cewa an samu nasara akan wannan aiki da aka sa a gaba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: