Connect with us

LABARAI

Gwamntin Kwara Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Shugaban APC Na Jihar

Published

on

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya yi tir da harin da ake zargin an kawai shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bashiru Bolarinwa.

Gwamnan ya yi wannan tir din ne a sanarwar da Sakataren watsa labarai na gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar a garin Ilorin a ranar Alhamis.

Gwamnan ya ce yana Allah-wadai da babban murya bisa harin da aka kai wa; “Shugaban APC, Hon. Bashiru Omolaja Bolarinwa, da ake zargin wasu zauna gari banza sun kai masa a karamar hukumar Moro. Wannan abin damuwa ne.” in ji shi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; gwamnan yana alfahari da zaman lafiyar jihar, tare da tir da duk wasu nau’in jama’a da ke son kawo fitina a jihar. A don haka ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi bincike domin cafko wadanda suka kai wannan harin domin su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: