Connect with us

NOMA

Noman Shinkafa: Gwamnatin Nasarawa Da Kamfanin Azman Sun Kulla Yarjejeniya

Published

on

Kamfanin sarrafa Shinkafa na Azman, Gwamnatin jihar Nasarawa da kuma alummar yankin Umaisha dake a cikin karamar hukumar Toto dake a cikin jihar ta Nasarawa, sun kulla yarjejeniya kan samar da kadada 14,000 don noman Shinkafa a jihar.

A jawabinsa bayan kulla yarjejeniyar Gwamnan jihar ta Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa, mafarkin shine don aga alummar dake jihar sun samu abin yi.

A cewar Gwamnan jihar ta Nasarawa Abdullahi Sule, wulla yarjejeniyar ta nuna irin dankon zumuncin dake a tsakanin Gwamnatin jihar Nasarwa da kamfanin na Azman da kuma alummar ta karamarhukumar Toto.

Gwamnan jihar ta Nasarawa Abdullahi Sule ya kuma jinjinawa daukacin wadanda suka taimaka wajen kulla yarjejeniyar, musamman Mai Martaba Ohimege Opanda, Alhaji Usman Abdullahi na Masarautar Toto.

Shi ma a nasa jawabin tunda farko, Atoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar ta Nasaraw Abdulkarim Abubakar Kana ya bayyana cewa, rattaba hannun yarjejeniyar anyi ne don a biya diyya ga alumomin dake da niyyar bayar da gonakan don a ayi akin.

Atoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar ta Nasaraw Abdulkarim Abubakar Kana ya kara da cewa, bayar da hayar ginakan zai kai tsawon shekaru 45, inda kuma za’a mikawa kamfanin na Azman bayan kamfanin ya biya kudin diyyar gonakan ga masu su.

Da ya ke yin bayanai a madadin masu zuba jari a fannin na noman Shinkafar a jihar ta Nasarawa, Shugaban Rukunonin kamfanin na Azman Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya sanar da cewa, sun zo jihar ta Nasarawa bisa gayyatar Gwamnan jihar Abdullahi Sule.

Shugaban Rukunonin kamfanin na Azman Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya kara da cewa, mun zo jihar ta Nasarawa ce don mu bayar da namu gudunmawar wajen samar da ayyukan yi ga alummar jihar

A cewar Shugaban Rukunonin kamfanin na Azman Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, kamfanin a shirye ya ke don ya fara aikin da zarar an samar da gonakan fara yin noman na Shinkafar.

Mataimakin Gwamnan jihar ta Nasarawa Emmanuel Akabe ne ya rattaba hannun madadin gwamnatin jihar ta Nasarawa, inda kuma Alhaji Sarina, ya rattaba hannu a.madadin kamfanin na Azman.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar ta Nasarawa Ibrahim Balarabe ne ya wakilci alummar ta karamar hukumar Toto a wurin yin yarjejeniyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: