Connect with us

RAHOTANNI

Samar Da Karin Malamai Zai Taimaka Wa Cigaban Ilimi – Barista Lawal

Published

on

Kwamishinan ma’aikatan gidaje da Sufuri na jihar Kano Barista M. A Lawal ya bayyana cewa daukar sabbin malamai guda 7,500 da Gwamnatin jihar Kano ta yi abu ne abin alfahari in a ka yi la’akari da matsaloli da ake dasu na rashin aikin yi a jihar Kano.

Ya ce, akwai dubban mutane sun yi karatu ba su da aikin yi basu da kuma yanda za su yi su sami aiki sai gashi Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan yunkuri babba na bada wannan dama ta aiki ga mutane 7,500 wannan zai taimaka sosai wajen bunkasa ilimi ta taimakawa wajen koyar da dalibai domin yanzu yawanci makarantu sai kaga suna da karancin malaman ga kuna yawan dalibai amma duk da yanayi na tattalin arziki aka yi wannan yunkuri aka samar da malaman.

Barista M.A Mahmud ya ce, wannan abin ayi godiya ne ga Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje bisa wannan abu daya faru.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: