Connect with us

LABARAI

Wanda Ake Zargi Da Cutar Coronavirus A Nijeriya Ba A Same Shi Da Cutar Ba

Published

on

Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da cewa wanda aka zarga yana da cutar coronavirus bayan an yi bincike an yi masa gwaji a dakin gwaje-gwaje na asibiti gwajin ya tabbatar da cewa ba shi da cutar  ta COVID-19.

Abayomi ya tabbatar da hakan ne a ranar Alhamis da safe a garin Legas, inda ya tabbatarwa da mazauna garin cewa tabbas babu wani da ya kamu da cutar ta Coronavirus a kafatanin jihar.

Ya kuma kara da cewa; suna sanya ido sosai wajen ganin sun kare kowa a jihar daga kamuwa da wannan cuta. Farfesa Abayomi, a sanarwar ya ce hankalin ma’aikatarsa ta lafiya ya karkata ne a yayin da ake zargin wani da kamuwa da cutar a asibitin Reddington Hospital dake Ikeja.

Sai dai ya ce a binciken da suka tattara wanda ake zargin wanda yake dan Chana ne, wanda ya zo Nijeriya daga Chana makonnin bakwai da suka gabata, ya gabatar da kansa ne a asibitin Reddington a ranar Laraba akan zazzabi da yake fama da shi.

Ya ce daga nan asibitin suka killace shi, sakamakon shawarwarin da ma’aikatarsa ta bayar, inda su kuma ma’aikatar ta shi suka dauke zuwa asibitin Mainland domin yi masa gwaji. Inda ya ce an debi jininsa, inda aka kai dakin gwajin jini na ‘Virology laboratory’ domin duba wa, wanda a karshe ba a same shi da cutar ba.

Farfesa Abayomi ya nemi al’umma da su daina yada labarin da ba shi ne ba, wand aka iya jawo damuwa ga al’umma.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: