Connect with us

RAHOTANNI

‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Jingina Musu Fashi A Dambam

Published

on

Shalkwatan ‘yan sandan jihar Bauchi ta samu nasarar cafke Bala Mato mai shekaru 57 da ya jingina musu laifin fashi da makami ta hanyar tabbatar wa gidan rediyon Muryar Amurka cewar ‘yan sandan ne suka yi fashi wa matafiya a kan hanyar Dambam da ke karamar hukumar Dambam a jihar Bauchi ranar 18 ga watan Biyu.

Bayan mai shaida wa gidan rediyon labarin, ‘yan sandan sun kuma cafke mutum uku daga cikin mutum 10 da suke zargi da fashin da aka jingina musu da fari, kana sun kuma cafke wani matashin da ya bayyana ra’ayinsa a Facebook da ya tabbatar da cewar sune suka yi fadi da makamin ga matafiyan.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Phillip S. Maku, shine ya baje wa ‘yan jarida mutum biyar din da suka cafken a jiya, a cewarshi, tun da fari an shafa wa jami’ansu laifin fashi da makamin wanda kuma hakan babban cin mutumci ne.

Sai ya shaida cewar sun samu nasarar cafke uku daga cikin wadanda suke zargi da yin fashin, inda ya bayar da sunayensu da Shehu Abdullahi dan shekara 20; Babawuro Jauro Sani mai shekaru 27 da kuma Wada Wakili Musa.

A cewar shi; “Sauran mutum bakwai din da muke zargi da hada hannu wajen yin fashin nan ta ranar 18/2/2020 za mu tabbatar mun cafko su,” A cewar Kwamishinan.

Idan za ku iya tunawa dai, an yada wani faifayin bidiyo da ke nuna cewar ‘yan sandan ne suka yi fashi wa jama’an, kana daga bisani ‘yan sandan suka karyata. Sai dai kwamishinan ya ce, tun faruwar lamarin suka tashi tsaye domin gano hakikanin lamari da cafko wadanda suke da hannu a cikin lamarin. kana CP din ya ce labarin karya aka yada a faifayin bidiyon da aka tura a kafafen sadarwa zamani a kansu.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labaru da bakinsa, Bala Mato da ‘yan sanda suka cafke bisa zargin ya tabbatar wa gidan rediyon Muryar Amurka abin da baida masaniya a kai dangane da fashin wanda har hakan ya jawo musu bakin jini daga wajen jama’a, Mato ya shaida cewar ya ji jama’a su na fada ne shi kuma ya tabbatar wa dan jarida.

 

Dan shekara 50 a duniya, “Mun je Fadar Hakimin Dambam muka samu motar ‘yan sanda da aka kawo dauke da kaya aka ce ‘yan sanda ne suka yi wa jama’a fashi. Ni kuma sai na yi hira da dan jarida na ce masa ‘yan sanda ne suka yi fashin nan. Daga baya aka zo aka tabbatar da cewar ba ‘yan sanda ne suka yi fashin ba.

“Da yake ina da lambobin ‘yan jarida da yawa a hannuna, kwatsam sai na danna na kira dan jarida na shaida masa cewar ga abin da muka wayi gari da shi. Muna gama hirar da shi ya je ya sanya a gidan rediyonsu,” A cewar Mato.

Da ya ke shaida dalilinsa na kiran dan jaridar Muryar Amurka ya shaida masa batun shine, “Kowa a lokacin ma abin da yake fada kenan. Muna waya tun da ana fada nima sai na tabbatar wa dan jarida,” A cewar shi.

Ko a kan idonka aka yi fashin da har ka ce ‘yan sanda ne? Sai ya amsa da cewa,“Ni dai ba na a wajen da aka yi fashin ba; amma na je wurin da aka kawo kaya da wadanda aka jikkata,”

Ya ce da ya tabbatar da abun da ya fada wa dan jaridar babu gaskiya a ciki ya kuma sake kiranshi domin neman gafarar wadanda abun ya shafa, “Na sake kiranshi na nemi gafarar shugaban ‘yan sanda na kasa, kwamishinan ‘yan sanda, DC, AC da DPO na Dambam. A gaban kwamishinan ma na nemi gafara don haka ina neman su min yafiya,” A fadin shi.

Shi kuma Muhammae Bappa Yarima da ‘yan sandan suka cafke kan bata musu suna da bayyana karerayi a kansu a soshal midiya, ya shaida cewar ya nemi gafararsu bayan da ya tabbatar da kuskure ya fadi, inda ya kuma kara da cewa ya dauki darasi sosai kan hakan.

A cewar Yarima mai shekaru 29 a duniya; “Na ga rubutu ne a facebook aka ce ‘yan sanda ne suka yi fashi a Dambam. Nan da nan na fadi ra’ayina a kai (comment) na ce; ‘Tirkashi masu kare rayuka da dukiyar al’umma a ce sun zama masu salwantarwa? To, Allah ya kyauta. Washegarima na sake cewa; ‘An yi Burum-burum an kulle akuya da fatar kura,”

“Amma daga baya na je na janye ra’ayina da na wallafa kan zargin na kuma baiwa kwamishina da dukkanin ‘yan sanda hakuri bisa hakan,”

Daga bisani mai bayyana ra’ayin nasa a Facebook ya tabbatar da cewar yayi nadama don haka ya nemi yafiyar wadanda abin ya shafa.

Da yake amsa tambayoyin LEADERSHIP A YAU, daya daga cikin wadanda ‘yan sanda suka cafke da zargin fashi da makamin Dambam da aka jigina wa ‘yan sandan, Shehu Abdullahi mai shekaru 20 dan kauyen Gare a karamar hukumar Dambam, ya tabbatar da cewar sune suka yi fadin a karkashin jagorancin wani mai suna Dan Jauro da ya arce ba a kai ga kamo shi ba kawo yanzu.

Ya ce; “Fashi muka yi wa jama’a, amma gaskiya wannan shine na farko. Ina gida sai dan Jauro ya kirani ya ce na zo za mu yi fashi, na ce masa ni fa ban taba yi ba, ya ce min dai na zo. Tun kafin na zo na samu sun kwaso itatuwa sai muka je muka rufe kan hanya. Mota Sharon tana zuwa muka tareta, bayan direban ya fito sai shi dan Jauro ya jawo wata mata a a cikin motar da karfi da danta guda.

“Mun kwace musu kayyaki da kudade, muka bude bayan motar muka kwashi akwatina uku jaka guda hudu, da sauran kayyaki sai muka gudu,” A cewar shi.

Shehun ya kuma nemi ‘yan sandan da su ragan musu bisa wannan aika-aikatar da suka yi. Ya kuma yi nadamar abin da yayi, sai yake mai shaida cewar tsautsayi ce ta ja shi shiga harkar fashi, kana ya nemi

Su ma Babawuro da Wada Wakili da ake zargi duk sun tabbatar wa ‘yan jarida cewar lallai sun yi fashin amma sun ce Dan Jauro wanda har yanzu ba kai ga kameshi ba ne ya sanya su yin fashin.

Kwamishinan CP Maku dai ya gabatar wa ‘yan jarida kayyakin da ‘yan fashin suka sace da aka cafko daga hannunsa hadi da makaman da suka yi amfani da su wurin fashin Dambam din, inda ya tabbatar da cewar za su gurfanar da su a gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: