Connect with us

NOMA

Za Mu Cigaba Da Tallafa Wa Manoman Kashu – Nanono

Published

on

Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya koka kan rashin shigar manoman kasar nan da dama wajen noman na Cashew, inda Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya yi nuni da cewa, fannin tuni ya jima wajen zama babba wajen bunkasa tattalin arziki fiye da dogaro da fannin samar da man fetur.

Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya bai wa manoman na Cashew da ke kasar nan goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma na masu zuba jarin su a fannin na noman Cashew.

Ya numa sanar da cewa, fannin noman Cashew, ya tarawa Nijeriya sama da naira biliyan 280 a hada-hadar musayar kudaden kasar waje daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2017.

Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya sanar da hakan ne ta hanyar wata Darakta a Ma’aikatar Gona da Rayar Uwargida Karima Babaginda a wani taron ma su ruwa da tsaki ada kuma kwararru afannin na noman Cashew da kungiyar manoman Cashew da sarrafa shi ta kasa ta gudanar a babban birnin tarayyar Abuja.

A cewar Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya bayyana, fannin na noman Cashew da a yanzu muke yin magana akai, ya na daya daga cikin amfanin gona da Nijeriya take yin amfani da damar shi, wajen fitar dashi zuwa kasashen duniya don tarawa Nijeriya kudaden shiga, inda kuma Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya koka kan rashin cin gajiyar fannin yadda ta kamata a kasar nan.

Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewa, mahimmancin Cashew a Nijeriya ya na kara karuwa, musamman wsjen fitar dashi zuwa kasashen ketare, kusan tun daga shekarar 1990.

Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya bayuana ya kuma yi nuni da cewa, gudunmawar da fannin na noman Cashew ya bayar wajen tarawa kasar nan kudaden shiga tun daga shekarar 2015, har yanzu ta na tafiya yadda ya kamata.

Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewa, Nijeriya ta tara kimanin dala miliyan 813, daidai da kimanin naira biliyan 284.5 daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2017 na musayar kudaden waje wajen fitar da Cashew daga kasar nan zuwa kasuwannin duniya.

A wata sabuwa kuwa, wasu masu yin fashin baki akan tattalin arzinin kasar nan sun sanar da cewa, ana ci gaba da kukan tsadar rayuwa a fadin kasar nan, har ta kai ana kiran da halin kuncin da jama’a.

Akwai masu ganin cewa rufe kan iyakoki da ahugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, yawan korar matasa masu kananan sana’o’i, kamar hayar baburan acaba da Keke Napep, ya kara haifar da korafe-korafen tsadar rayuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: