Connect with us

RA'AYINMU

Batun Zabuka Da Hukunce-Hukuncen Kotun Koli

Published

on

A makon da ya gabata, Kotun Koli ta ya yi wani hukunci na ban mamaki, wanda ya girgiza al’ummar wannan kasa baki-daya, wannan hukunci kuwa shi ne, na kwace kujerar Gwamnan Jihar Bayelsa, Dabid Lyon na Jam’iyyar APC tare da umartar Hukumar INEC ta kasa, ta gaggauta baiwa dan takarar da ke biye da wannan Jam’iyyar ta APC a yawan kuri’u. Kazalika, Lyon din shi ne wanda aka ayyana za a rantsar a matsayin Gwamnan Jihar ta Bayelsa, ranar Juma’a 14 ga watan Febrairu, kwatsam sai ga shi kuma wannan Kotu ta zartar da wannan hukunci kwana daya tak kafin rantsuwar.

Manyan Alkalan wannan Kotu biyar, bisa jagorancin Mai Shari’a Mary Odili ne suka yanke hukuncin cewa, an samu Degi-Eremienyo da laifin gabatar da takardar shedar karatu na boge ga Hukumar INEC.

Jam’iyyar PDP ce dai ta shigar da wannan kara ta hanyar kalubalantar shedar karatun na Degi-Eremienyo a gaban Kotu.

Ko shakka babu dai, wannan hukunci na Jihar Bayelsa ya zo da matukar ban mamaki, domin kuwa shi ne irinsa na farko da aka taba yi a tarihin wannan kasa. Haka zalika, hukuncin ya matukar haifar da cece-kuce kan cewa, ta yaya laifin Mataimakin Gwamna kai tsaye zai shafi zababben Gwamna har ta kai ga ya rasa kujerar dungurungun?

Har wa yau, akwai shigen wannan hukunci wanda manyan Alkalan Kotunan suka aiwatar mai ban mamakin gaske, na karbe kujerar Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha sakamakon rashin samun kuri’u masu rinjaye da ya yi a zaben Gwamnan da aka gabatar a ranar 9 ga watan Mayun 2019.

Sannan ba tare da wani bata lokaci, Kotun ta bayar da umarnin rantsayar da dan tarar Jam’iyyar APC, Sanata Hope Uzodinma, a matsayin wanda ya samu nasara a zaben Gwamnan Jihar ta Imo, na 9 ga watan Mayun 2019.

Haka nan, wannan gidan Jarida ba zai manta da hukuncin da manyan Alkalan irin wannan Kotu suka yi a ranar 24 ga watan Mayun 2019 ba, wato na karbe dukkanin kujerun Jam’iyyar APC, na babban zaben da aiwatar a shekarar 2019 na Jihar Zamfara. Inda Kotun ta yanke hukuncin cewa, kwata-kwata Jam’iyya mai mulki a jihar, ba ta gudanar da zabenta na cikin gida ba.

Manyan Alkalan Kotun guda biyar sun ayyana cewa, “dukkanin Jam’iyyar da ba ta gudanar da sahihin zaben cikin gida ba, babu yadda za a yi ta samu nasarar lashe babban zabe na du-gari”.

Ire-iren wadannan hukunce-hukunce da ke faruwa, na matukar harfar da cece-kuce na ganin cewa, kamar sannu a hankali Alkalai na neman karbe ragamar ayyuka tare da hurumin da Hukumar INEC ke da shi da kuma su kansu masu jefa kuri’a. Baki-dayan abubuwan da aka ambata a sama, sun sabawa tunani, domin kuwa Hukumar INEC, ta shirya zabubbuka su kuma masu yin zabe ko jefa kuri’u, sun fito sun tsaya tsayin-daka sun zabi abinda ransu ke so, amma tashi guda kuma Kotu ta ayyana wani daban a matsayi wanda ya lashe zaben, wanda hakan ko shakka babu ya ci karo da dokar da aka tanadarwa wadannan zabubbuka.

A nan ba wai ana cewa, ka da Kotu ta yi hukunci ba ne, ko kuma ba ta da hurumi ko wani abu makamancin haka ba, a’a, amma magana ta gaskiya ita ce, ire-iren wadannan shari’u da Kotuna ke yi, kan iya haifar da rigingimu ko tashin hankali a tsakanin al’umma, musamman ganin cewa Kotuna kadai ke da iko akansu, wannan shi ne hikimar kafa Kotunan korafe-korafen zabe, bayan kammala zabubbuka. Don haka, muna sake fada da babbar murya cewa, ire-iren wadannan hukunce-hukunce, zai yi matukar wuya a samu masu inganci ko na gaskiya.

Hakan kuwa, a fili yake musamman idan muka dubi zaben Jihar Bayelsa da na Zamfara, inda Jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerunta, amma aka yi amfani da wasu abubuwa daban aka kwace kafatanin kujerun, wanda ko shakka babu son zuciya ne kawai na wadannan Alkalai.

Musamman idan aka yi la’akari da Jihar ta Zamfara, wadda tun shekarar 1999, Jam’iyya daya ce ke yin mulki, ba su taba canza wata Jam’iyya ba sai a wannan karon da Alkalai suka kakaba musu, domin kuwa Jam’iyyar PDP ba ta taba samun nasarar lashe kujerar Gwamna ba a wannan jiha ba. Sannan a Jihar Bayelsa, sai da ‘yan asalin jihar masu kada kuri’u, suka fito suka yi zanga-zanga bisa zargin tsohon Gwamnan, Seriake Dickson da kakaba musu dan Jam’iyyarsa ta PDP a matsayin Gwamnan Jihar.

Saboda haka, wannan gidan Jarida na da ra’ayin cewa, rika kakaba wa al’ummar Nijeriya Shugaban da ba shi ne zabinsu ba, ko kadan wannan ba demokradiyya ba ne, ya fi kama da mulkin kama-karya na Soja. Babu yadda za a yi a cewa, mutane guda biyar kacal su zauna su yanke shawarar wanda zai mulki jiha baki-dayanta, wannan ba karamin nakasu ne ga demokradiyyar wannan kasa ba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: