Connect with us

ADABI

Daga Littafin Bakar Guguwa (25)

Published

on

“Mommy ni fa babu abinda yake tsakanina da ya Nauman” cikin rud’ani da rashin fahimta Hajjiya Usaina take kallonta, Zarah ta ci gaba da magana “kuma ni ban san wani Sagir ba, kum… ” tun kan ta k’arasa maganar da take k’ok’arin furtawa Hajjiya Usaina ta katse ta da cewa “ke dakata! Karki maida ni k’aramar yarinya mana wadda bata san me take ba, kullum kina cikin k’unci idan na tambaye ki kice babu komai shi ne yanzu ma kike son maida ni sha-sha-sha? Har yaushe kika zo duniyar da zaki nunan kin fini saninta? Ko kin manta da cewar ni na haifeki? to idan kin manta yanzu ni na tuna miki. Bari kinji na fad’a miki duk wani shige da ficen da kike na sani na kuma san me kike” da sauri Zarah ta d’ago kanta ta kalli Mummy cikin tsananin mamaki tare da taraddadin kada ace mummy tasan komai tsakaninta da Sagir zuciyarta cike da fargabar abinda zai je ya zo yayin da Hajjiya usaina taci gaba da magana “Naji idan ma babu abinda ke tsakaninki da Sagir shi kuma Nauman fa? duk sintirin da yake wajanki cewa kike ban sani ba ko kuwa ni makauniyace da ban san komai ba, kina tunanin ba zan gane ba ko?” ajjiyar zuciya Zarah ta saki kad’an Hajjiya taci gaba da magana “sauna kika maida ni? Har da Zaki wani ce kefa babu abinda yake tsakaninki da shi? Idan babu komai tsakaninku me yake kawo shi wajen ki, Alhanin da can ba zuwa yake ba?” Wani masifaffen zafi ta runk’a ji daga can cikin k’irjinta ji take kamar zuciyarta zata fashe me yasa mommy ta kasa fahimtata? Zuciyarta ke sak’a mata hakan ji take kamar tace ba haka bane sai dai ba zata iya ba, zuciyarta taci gaba da raya mata cewa Mummy ta kasa fahimta ta da ace zata saurare ni dana yi mata bayanin komai, me yasa ba zata tambaye ni ba? To ma idan ta tambayeni zan iya fad’a mata komai?. Ganin tayi shuru bata ce k’ala ba yasa Hajjiya Usaina ci gaba da maganar da take tare da saukar da murya k’asa “ni ba zuwa nayi dan wasa ba, nazo ne ki sanar da ni wanda kike so idan ma wani abun ne ya shiga tsakaninku kike b’oyewa sai kiyi magana asan yadda za’a gyara matsalar ba wai ki zauna cikin k’unci ba” Hajjiya na fad’ar hakan Zarah ta d’ago da sauri ta kalleta bata san lokacin da kwalla ta fara gangarowa kan kuncin ta ba ta rasa me yasa Hajjiya ta kasa fahimtar cewa ba Nauman bane?, tayi k’asa da kanta na ba yadda zata yi taci gaba da sauraren Hajjiya yayin da zuciyarta take ci gaba da sak’a mata wasu abubuwan da bata fatan faruwarsu, ba komai ne yasa ta zubda kwalla ba face tuna abinda ya shiga tsakaninta da Najib gashi kuma basu sasanta ba balle ta gabatar da shi yanzu” taci gaba da kukan takaici Hajjiya ta k’ara da cewa “ki fad’a mun wanda kike so cikinsu domin kuwa mahaifinki ya gaji da zaryar da ake wajenki idan kuma ni ba zaki iya sanar da ni ba, shi kya sanar masa” da sauri ta sake d’ago fuskar da ta cika da kwalla ta kalli Hajjiya tana k’ok’arin sharewa cikin muryar kuka tace “wallahi mommy duk cikin su babu wanda nake so” mamaki ne ya k’ara kama Hajjiya Usaina cikin rashin fahimta tace “ban gane babu wanda kike so ba, kina nufin sansu ne ba kya yi yanzu sabida kinji maganar aure ko kuwa me kike nufi?” shuru Zarah tayi ta kasa magana sai wasu hawaye masu zafi da rad’ad’i da suke kwaranyo mata daga cikin idanuwanta zuwa kan kuncinta, ganin tak’i magana yasa Hajjiya daka mata tsawa tare da fad’in “ba da ke nake ba kinyi shuru kina kuka dukanki nayi?” girgiza kai Zarah tayi alamar a’a sannan Hajjiya ta kuma cewa “ina saurarenki” a hankali Zarah take magana cikin muryar kuka tace “babu wanda muka yi magana da shi cikin su gaisawa kawai muke” mamaki ne ya k’ara kama Hajjiya Usaina “har shi Nauman d’in da yake zaryar zuwa wajen naki?” da sauri Zarah tace “ba shi bane Mummy” cikin tsananin mamaki Hajjiya Usaina tace “To in ba shi bane wanene, kuma me yake zuwa yi wajenki?” ba yadda Zarah ta iya ala dole tace “Sagir ne” sosai Hajjiya ta kalle ta sai a lokacin ta gane cewa wanda yake zuwa wajen Zarah ba Nauman bane ashe Sagir ne, ta kuma tambayarta “kika ce babu abinda yake tsakaninki da shi, sabida kin maida ni abokiyar wasanki ko? To bari ni naje in yaso shi ya tambayeki da kansa” mik’ewa tayi tsaye tana shirin fucewa daga d’akin, da sauri Zarah tace “Dan Allah Mummy karki je, wallahi ni bana sonsa” tausayin Zarah ne ya kama Hajjiya Usaina ganin yadda fuskarta tayi jawur kamar gauta yasa ta dawo ta zauna bayan data d’anyi shuru na ‘yan wasu dak’ik’u daga bisa ni tace “ina sauraranki wa kike so?
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: