Connect with us

ADON GARI

Ina Bakin Cikin Na Ga Masoyin Annabi Ba Ya Koyi Da Halin Annabi – Fatima Aminu

Published

on

Bakuwarmu ta Adon Gari na wannan makon, Sha’ira ce mai begen Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (SAW). Ta bayyana cewa ita fa a duniyar nan babban abin da ke sa ta bakin ciki shi ne ta ga mutumin da yake ikirarin shi Masoyin Annabi (SAW) ne amma kuma ba ya koyi da halin Annabin. Hirar da aka yi da ita cike take da darussa tun daga farkon fara begenta har zuwa lokacin da muka zanta da ita a wannan makon. Ga hirar:

 

Da farko za ki fada wa masu karatu cikakken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi..

Sunana Fatima Aminu Abdurra’uf wadda aka fi sani da Fatima Ludufi.

 

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

To ni dai an haifeni a Dala na yi firamare na a Dala sannan na yi sakandare dina a Gwammaja daga karshe na yi School of health technology (Makarantar nazarin fasahar kiwon lafiya). Bangaren islamiyya kuma na yi makarantu daban-daban wanda har yanzu ban daina karatun addini ba.

Da kyau! Sai dai ba ki fada wa masu karatu shekarunki ba.

A yanzu ina da shekara ashirin

 

Shin malama Fatima tana da aure?

A’a, ba ni da aure

 

A yanzu kina aiki ne ko Kuma sana’a kike?

Gaskiya ban fara aiki ba sai dai sana’a, da kuma waka da nake yi.

 

Kamar wacce irin sana’a kike yi?

Sana’ar Dinki

 

Masha’Allah, kice madinkiya muke tare da ita kuma sha’ira, bari mu shiga kan abin da ya shafi waka, me ya ja hankalinki kika tsunduma cikin harkar waka?

Ni dai na taso na ji ana yabon Manzon Allah SAW a gidanmu. Hakan ne ya sa ni ma na taso cikin shaukin yin yabon har Allah ya kawo ni wannan lokacin.

 

Kamar wanne irin wakoki kike yi?

Wakokin yabo nake.

 

Za ki kamar shekara nawa kina waka?

Shekarata bakwai da farawa.

 

Lokacin da za ki fara wacce hanya kika bi wajen ganin kin fara din?

Na samu mahaifina na ce masa ina so na fara buga kaseeda ya ce min to Allah ya yi jagora. Sai na samu malaminmu na islamiyya na gaya masa cewa ina so ya rubuta min. To daga lokacin na fara bugawa.

 

Da wacce waka kika fara a wancen lokacin?

Na fara da

Ludufi.

 

Ya karbuwar kasidar ta kasance a wajen Jama’a?

Gaskiya kasidar ta karbu sosai har wata jihar ta je abin dai Masha Allah

 

Gaskiya ne, nawa ne adadin wakokin da kika yi?

Za su kai ashirin da biyar

 

Ke kike rubutawa ko kuwa rubuta miki ake?

Ina rubutawa sannan ana rubuta min.

 

Nawa ne adadin wanda kika rubuta Kuma ya sunansu?

Wanda Na rubuta za su kai guda goma. Akwai: Garkuwata, Shugaban Annabawa, Nabi Ma’aiki, Annabina, Karima. Sauran Su Ne: Tsokar Annabi, Mukarrama, Nabi Annabi, Mauludi Da Kuma Ta Nana Amina wadda ita ce cikin ta goma

 

Masha’Allah cikin wadan nan wakokin da kika rubuta wacce kika fi so?

Duk ina sonsu domin kuwa ina farin ciki da alfahari da su.

 

Me yasa kike son su duka?

Ina so saboda ina farin ciki da Allah ya bani dama na rubuta.

 

Da kyau! A cikin wakokin da kika rubuta wacce waka ce ta fi baki wuya wajen rubutawa?

Garkuwata ta ba ni wahala sosai.

 

Me ya ba ki wahala wajen rubutawa?

Baitukan ne suka ba ni wahala.

 

Mu dan dada komawa baya kadan, lokacin da za ki fara rubutawa da kanki shin kin nemi taimakon wani ko wata ta koya miki, ko kuwa da kanki kika ji kina kirkira kina rubutawa, ya abin ya kasance?

Akwai taimakon mahaifiyata domin idan na kakare ita take dorani a kan hanya, bayan na gama rubutawa sai na kaiwa malamina ya duba min.

 

Toh ya farkon fara wakarki ya kasance lokacin da kika fara shiga ‘studio’ ta ya kika fara kuma wa ya kai ki?

Lokacin da na fara shiga ‘studio’ ban ji wani abuba har abin ya bawa masu studion mamaki domin na yi kasidata hankali kwance ban ji wata damuwaba. Kuma malamina shi ya kai ni na yi.

 

Idan na fahimceki kina so kice matsalolin da ake samu ga wasu musamman wajen dora waka a ce murya ta ki doruwa ko a ce ta yi kankanta ai ta shan wahala ko makamantan haka, duk ke ba ki samu hakan ba?

Wallahi ban samu matsala ko daya ba.

 

Da kyau! Bayan wakokin yabo da kike shin kikan hada dana fina-finai ko siyasa, ko na biki ko kuwa ya abin yake?

Iya yabo kawai nake yi.

 

Ko za ki fadawa masu karatu sauran wakokin da kika rera dan su dada fahimtar wadda muke tare da ita?

Na yi: Ludufi, Jasadi, Son Annabi Ne –Mafita, Ya Fadima, Suffar Ma’aiki, Shauki, Kaunar Daha,Maji Roko, Gaskiya, Ya Rasullah, Nan Amina. Akwai Kuma: Sayyidi Abdallah, Nana Khadija, Sayyidi Ali Da Gaskiyar Ma’aiki.

 

Masha Allah, idan za ki rubuta waka kamar wanne lokaci kike samun damar rubutawa, yaushe ne kika fi jin dadin rubutawa?

Koda wanne lokaci ina rubutawa in dai kari ya zo min.

 

A cikin wadan nan wakokin naki idan aka ce ki dauki guda daya ki rerawa masu karatu Koda baiti guda ne wacce za ki dauka kiyi musu?

Zan rera Ya Fadima. Ga kadan daga ciki:

“Akwana a tashi wataran nana zatai kirana

Don arziki da buwayar abbanki inje madeena

Inje ni rauda fadar ma’aiki nima Na zauna

In roki aljannah itace mafita ba duniyaba dake da rana”

Sallama

Sai Dai Shiru

 

Da kyau! Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta a harkar waka?

Ban taba fuskantar kalubale ba.

 

Wanne irin nasarori kika samu a harkar waka?

Na samu nasarori kala-kala domin na gamu da ‘yan uwana sha’irai wanda suka shahara kuma suna nuna min kauna sun maida ni ‘yar uwarsu ta jini. Kuma sanadin yabo na samu alkhairai

Da kyau, idan aka ce ki fadi su waye iyayen gidanki kamar su wa za ki fada?

Akwai ‘yan biyun ma’aiki da kuma Jama’ar ambato

 

Tarurrukan mawaka kin halarci taro kamar guda nawa?

Na harci taruka da dama wanda ban san adadiba.

 

Ya mu’alumarki da sauran mawaka take?

Muna mutunta juna yanda ya kamata.

 

Wace ce babbar kawarki a mawaka?

Kowacce na dauketa babbar kawa domin kowacce muna da fahimtar juna tsakaninmu.

 

Ya kike iya hada sana’ar dinkin ki da kuma waka?

Ko wanne ina yinsa yanda ya kamata.

 

Me ya fi sa ki farin ciki, me kuma ya fi sa ki bacin rai?

Babban farin cikina na ga masoyin Manzon Allah (SAW). Bakin cikina kuma na ga masoyin Annabi ba ya koyi da halin Annabi.

 

Gaskiya ne, menene burinki a rayuwa nan gaba?

Babban burina bai wuce na je Madina ba na ziyarci Manzon Allah SAW.

 

Allah ya nufa, toh ya batun karatu fa shin za ki ci gaba ko kuwa iya haka za ki tsaya ?

idan Allah ya nufa zan cigaba.

 

Idan kika yi aure kika haifi ‘ya ta taso tana son ta yi waka shin za ki barta tayi ko kuwa ya abin yake?

Zan barta tayi domin ni ma iyayena sun bar ni ina yi.

 

Wacce shawara za ki bawa ‘yan uwa mata na gida wanda suke zaune ba tare da sana’a ba, da kuma mata masu jiran miji?

Shawara ta gare su ita ce su farka su kama sana’a kar su Jira sai an basu, domin duk wadda ba ta sana’a to wallah abar tausayice. Don haka mu farka muma mu tsaya da kafarmu. Mata masu jiran miji kuma su yi ta addu’a Allah ya kawo musu miji masoyin Annabi na hakika.

 

Ko akwai abin da ya taba faruwa da ke wanda ba za ki taba mantawa da shi ba a harkar waka ba?

Abin da ya faru da ni wanda ba zan mantaba shi ne, na je zan yi kasida kawai sai muryata ta rike na kasa furta komai sai dawowa gida na yi

 

A sauran mawaka wanne mawaki ne ko mawakiya ce wakarta tafi ko yafi birgeki, Kuma me ya sa?

Kowanne mawaki ina jin dadin wakarsa, kuma duk suna burgeni

 

Za ki ga wasu mawakan sukan bi wani salo na wakar wani ko wata, shin ke ma naki wakokin kikan yi amfani da salon wani ne ko wata, ya za ki bawa masu karatu labari?

Gaskiya ba na yin salon kowa, nawa nake yi.

 

Wasu mawakan mata za ki ga idan sunyi aure suna ci gaba da yin wakokinsu musamman masu yin na yabo, shin ke ma kina da wannan burin a zuciyarki ko kuwa ya abin yake?

Ina da burin haka sosai ma kuwa.

 

Wanne irin namiji kike son aura?

Ina son mai ilimin addini kuma masoyin Annabi (SAW)

 

Me za ki ce da wannan shafi na Adon Gari?

Ba abinda zance da su sai fatan alkhairi kuma Allah ya daukakaku ku fi haka, Allah ya kare ku daga sharrin masu sharri.

 

Amin, me za ki ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a?

Gaskiya muna jin dadin jariďar LEADERSHIP musamman wannan shafi na Adon Gari

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina gaishe da masoya Annabi (SAW). Sannan ina gaishe da mahaifana da kuma kannena.

 

Madallah, muna godiya da b amu lokacinki da kika yi.

Ina mai farin ciki da kasancewata a cikin wannan shiri.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: