Connect with us

JAKAR MAGORI

Dan Sanda Ya Shiga Hannu Bisa Laifin Garkuwa Da Mutane

Published

on

Wani dan sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sandar Jihar Kuros Ribas ya shiga hannu, bisa zargin sa da hannu wajen aikata garkuwa da mutane a cikin jihar.

Majiyarmu ta ruwaito ma na cewa, wanda a ke zargin ya na cikiin tawagar ‘yan bindiga guda biyar. Haka kuma an samu nasarar damke dukkan tawagar ‘yan bindigan guda biyar a garin Kalaba. An bayyana cewa, tawagar rundunar ‘yan sanda wanda a ke kira da suna Operation Skolombo su ne suka sami nasarar damke wanda a ke zargi.

Wani babban jami’an dan sanda ya bayyana cewa, tawagar ‘yan sanda sun sami nasarar cafke wani dan sanda tare da wasu wadanda ake zargi a ranar Litinin lokacuin da suka sami rahoton sirri.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, dan sandan yana da kudi sosai da kuma gidaje a garn Kalaba, inda yake zaune a barikin ‘yan sanda da ake kira da suna Eburutu da ke garin Kalabar. Ya tabbatar da cewa, ‘yan sanda suna kokarin ganin an saki Mista Maurice Archibong, akawun jaridar Nigeriya Chronicle wanda aka yi garkuwa da shi a cikin jihar a makon da ta gabata.

Lokacin da manema labarai suka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar jihar DSP Irene Igbo, ta bayyana cewa, ba ta da masaniya a kan kama wannan dan sanda, amma ta bayyana cewa, an kawo rahoton garkuwa da mutane a makon da ta gabata.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: