Connect with us

LABARAI

Kaciyar Mata Ya Ragu Cikin Shekaru Biyar – Kwararriya

Published

on

Binciken hukumar lafiya ta NDHS ya bayyana cewa yawan matan da ake yi wa kaciya ya ragu da kasha 25 a shekarar 2013 ya zuwa kashi 20 a shekarar 2018.

Kwararriya a kan sanya ido, Uwargida Maureen Zubie-Okolo, ce ta fadi hakan a Fatakwal wajen wani taron tattaunawa da manema labarai na Editoci da masu dauko rahotanni.

Ta ce, al’adar ta yi wa mata kaciya abu ce da yawancin kasashen Duniya suke daukarsa a matsayin take wa mata hakkinsu, wanda ya samo asali daga al’ada da fahimta na addini a tsawon zamani.

Al’adar ta kunshi ragewa ne ko kuma yankewar baki-dayan wani sashe na al’aurar mata domin al’ada ko kuma wata manufar ta daban.

A cewar Zubie-Okolo, binciken ya nuna al’adar kaciyar ta mata ta ragu a cikin kasar nan, amma dai har yanzun akwai ta a wasu Jihohin kamar Jihohin Kudu maso gabashin kasar nan (Ebonyi da Imo), Kudu maso yammaci (Ekiti) da arewa maso yamma (Kaduna).

Ebonyi tana da kashi 53, Imo tana da kashi 62, Ekiti tana da kashi 56 sa’ilin da Kaduna ke da kashi 49, in ji ta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: