Connect with us

ADABI

Karimci Da Kimar Shata Sun Sa Ya Wuce Darajar Dan’uwa A Gidan Mu -Zannan Katsina

Published

on

Sunan Zannan Katsina, Alhaji Lawal Musa Bindawa, suna ne da ya kada karaurawa a Lardin Katsina, da sauran sassan jihohin Arewa. Zanna, babban ma’aikaci ne kuma Dan siyasa, sannan kuma mai rike da sarauta. A kwanakin baya, Zannan na Katsina ya tattauna da Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, fitaccen marubuci, kuma mawallafin littafin tarihin rayuwar marigayi Dokta Mamman Shata Katsina. Ya bayyana masa irin kaurin alakar mahaifin sa da Dodon mawakan. Ya kuma yi masa korafin yanda tun bayan rasuwar mahaifin nasa cikin Disambar 1978 babu wani daga cikin dangin su da ya dauki dawainiyar hidimar gidan su sai Shata. Ga dai yanda hirar ta su ta kasance:

Ranka ya dade, muna so mu ji wanene Zannan Katsina?

A’uzu billahi minashshaidanirrajim, bismillahirrahmanirrahim. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki.

Sunana Alhaji Lawal Musa Bindawa. An haife ni a cikin shekarar 1966. Na yi firamare a Katsina. Na halarci makarantar kwalejin gwamnati ta Kaduna, daga 1978 zuwa 1983. Sannan na wuce Jami’ar Bayero ta Kano na yi karatun digiri a fannin nazarin Kimiyyar Siyasa.

Mahaifi na, Alhaji Musa Bindawa, babban akawu ne, mai biyan albashi a ma’aikatar Ilimi ta tsohuwar jihar Kaduna. Wurin zaman sa na karshe shi ne Kwalejin Horas da Malamai Mata da ke Katsina. Sunan mahaifin sa Malam Sani, malamin Hakimin Bindawa Dan Yusufa Bello (Dangoggo) Saboda alakar Sani da Dan Yusufa ta sanya ya ba shi mukami a masarautar sa. Don haka sai ya tura shi Shibdawa. Sani ya yi tarayya, ko babban abokin ‘Yandaka Lawal, watau Hakimin Dutsin-Ma ne, da kuma Kaura Mammodu na Rimi.

Bangaren mahaifin Musa Bindawa ke nan. Ta wajen mahaifiyar sa fa?

Ta wajen uwa kuma , mahaifiyar Musa Bindawa t a fito daga yankin Bakori. Ita diyar Dangi Bagudu Muhammadu ce. Kuma ita kanwar Bakori Salihu ce, mahaifin su daya. Idan ba a manta ba, zuriyar su ne suka kafa Bakori, kuma sune mafarin sarautar garin. Sunan ta Hajiya Balaraba.

Akwai Sa’adu da Iro, dukan su kannen ta ne, Don haka Musa Bindawa jikan Dangi Muhammadu ne. Za ka ji ma Shatan yana ambaton haka a cikin daya daga cikin wakokin da ya yi ma mahaifi na, yana cewa: A gaishe ka dan Sa’adu da Iro, Musa Uban Lawal Dan Dangi. Yana kuma cewa : Jikan Bagudu Dan Salmanu…’, / Jikan Salihu mai Bakori, Musa Uban Lawal Dan Dangi. Dukan su ukun ‘ya’yan Dangi Bagudu ne.

Bakori Salihu shi ne mahaifin Bakori Ibrahim. Shi kuma Bakori Ibrahim shi ya haifi Bakori Garba ko Abubakar, wanda a yanzu shi ne Maigarin Bakori.

Minene alakar kakar ku da Dangawa na ‘Yantumaki, da kuma mutanen Keffi, su Guruf Kyaftin Usman Jibrin ?

Dukan su dangin mu ne. Ai zuriyar mu fadadda ce.

Ina alakar Shata da Musa Bindawa?

Na tashi na ga mahaifina tare da Shata. Kaka ta ta wajen uba tana zaune a Bakori. Sunan ta Hajiya Balaraba. Da ya ke duk ranar Juma’a, in dai Shata yana a gari bai yi tafiya ba, ya kan je can Bakori wajen kakar tawa ya gaishe ta. Za ya kawo alheri mai yawa ya bata. Duk dan uwa ko dangi da ya taras za ya kawo kudi ya ba shi, duk don albarkacin Musa Bindawa mahaifi na. A takaice ya mayar da kaka ta kamar mahaifiyar sa. To sai aka kai ni yaye ni a Bakori a hannun ta, lokacin ina da shekara biyu, watau a tsakanin 1967 ko farkon 1968.

Kawai, rannan sai ga Shata ya zo Bakori, shi da wata amaryar sa Hajiya Yalwa don su gaishe da kaka ta. Sai ya dauke ni ya saka ni a mota suka tafi da ni. Daga ni sai wata guntuwar taguwa a jiki na. Muka wuce zuwa Maradi. Daga Maradi muka wuce zuwa Yamai. Shata ne da matar sa Yalwa, ba su maido ni gida ba sai bayan wata shida (6). Rananr da suka maido ni Shata ya saya mani kaya, masu sunan kaya, sai da aka cika akwati goma sha biyu (12) Tun a wannan lokaci Shatan ke kira na da ‘Mamman’ don ba ya ce ma ni Lawal. Ai, a amshin daya daga cikin wakokin da ya yi ma mahaifin mu, da ya ke cewa: ‘Musa Bindawa Uban Mamman’, ai nine Mamman din.

Don haka, na zauna a hannun Yalwa na tsawon wata 6 a tsakanin Maradi da Yamai da Funtuwa. Kullum za ta yi mani wanka, ta yi mani kwalliya. Ta mayar da ni kamar dan ta na cikin ta. Har gobe idan ta gan ni ‘da na’ ta ke ce ma ni.

Lokacin da na fara wayau, na san Shata yana yawan zuwa gidan mu tare da baba na. Wani lokaci ma da kimanin karfe daya, ko biyu na dare za ya zo ya buga kofa. Watau idan yana wasa a otel a Katsina. Sai ya dauko mota ya zo gidan mu. Idan ya buga kofa, mahaifiya ta za ta bude kofa. Za ya shigo ya zauna. Sai uwa ta ta hau saman bene ta tayar da baba na daga barci, ta ce masa : ‘Shata ne fa ya zo’.Sai ya ce mata : ‘rabi da shi ba zan sauko ba, babu ruwa na da shi’. Sai ta sauko kasa, inda falon mu ya ke. Ta ce ma Shata: ‘ya ce ba za ya zo ba’. Sai ya ce mata : Dije akwai abinci?’ Ta kan ce masa ‘babu’. Amma sai ta tashi ta dafa masa. Nan za ya zauna a falo, har ya kai asuba. Wani lokaci har barci ya dauke shi, ita uwa ta tana can tana dafa masa abinci. Idan ya ci, da asuba sai ya tashi ya koma otel. To idan ya zo, ya kan tashe ni in zo in zauna tare da shi muna hira. Idan na fahimci ya yi barci sai in tafi in kwanta. Ya kan zo da kudi masu yawa. Shi Shata, har ya gama cin abinci ya tafi Musa Bindawa ba za ya sauko su gaisa ba.

Ina dalilin, ya zo gidan mutum, amma sai mai gidan ya ce ba za ya fito ba, ko akwai sabani ne?

E, sai daga baya na rika tambayon mahaifiya ta. Sai ta ke fada ma ni cewa ashe shi mahaifi na yana gayyatar sa buki, na aminan sa, to sai ya noke ya ki zuwa. Don an ga irin amanar da ke a tsakanin su, sai a rika rabawa ana goyawa da mahaifi na wajen gayyato Shatan buki. Shi kuma baba na sai ya yi fushi. To shi ne idan ya zo da tsakar dare shi kuma sai ya ki saukowa su gaisa, saboda ya yi fushi. Ke nan an bata. Ashe ke nan Shatan na zuwa a matsayin ya zo bikon Musa Bindawa.

Amma dangantakar su ta kai har Shibdawa Shatan ke zuwa yana gaishe da mahaifin Musa Bindawa a lokacin da ya ke da rai.

Wannan ne kurum zaman da ka yi a hannun Shata, ko ka kara zama a wajen sa a wani lokaci?

Wata rana Yunusa sarkin mota, direban Sarkin Katsina ya tafi ya gaishe da mahaifiya ta a gida. Ina tammanin cikin 1980 ne, domin a lokacin mahaifi na ya rasu da kimanin shekara biyu. Sai ya ce mata jiya da dare Shata ya kwana yana wasa a otel a cikin garin Katsina. To a gabana aka yi maganar. Sai na dauki keke na na tafi inda yake sauka, wani gidan Sa’I a kusa da makarantar firamare ta Garama. Na tarar da shi a kofar gidan zaune suna hira shi da wasu mutane. Yana gani na sai ya ce ‘Mamman daga ina ka ke?’ Na ce masa ‘daga gida’. Sai na ga ya yi shiru, yana kallo na, fuskar da cike da tausayi, kamar za ya yi kuka.

Ali Kankara tare da ‘yan uwan Shata a tsakiyar Shata tare da diyar sa marigayiya Hajjajo, a cikin falon sa gidan su Shatan,a Musawa, Mayu 1997

Don wannan ne ganin sa da ni na farko bayan rasuwar mahaifi na. Sai ya ce ma mutanen da suke tare: ‘shi ya sanya bana son zuwa Katsina. Saboda a cikin shekara biyu na rasa aminai biyu, da Musa Bindawa da Sani Audi.

Ya tashi ya shiga cikin daki. Ya fiddo kudi, ya ba wani mutum ya ce ya tafi gidan mu ya kai ma mahaifiya ta, a kuma shaida mata cewa ya tafi da ni Funtuwa, yana son in yi masa hutu can. Keken ma saidai aka kai mata. Shata ya saka ni a mota muka tafi Funtuwa, ko gida bai bari na biya ba, ballantana in dauki sutura. Da muka isa Jikamshi, mun fita daga garin da kimanin tafiyar rabin kilomita, sai ya saki hanya ya ratse. Muka nufi daji. Mun yi tafiya ta kimanin mintina goma sha biyar (15) sai ya ja burki a gab da wata katuwar itaciya ta kuka. Ina ma tammanin kukkuki ne, watau namijin kuka, saboda a duk wurin iccen ya fi kowanne iccen kuka girma. Muka fito. Ga wurin an yi rowan sama, don a lokacin, da damina ne, amma inda katuwar kukar nan ta ke babu lema babu alamar ta. Amma kuma sauran farfajiyar wurin akwai ruwa kwance, ko’ina.

Sai ya nuna kukar nan ya ce ma ni: ‘Mamman, ka ga gida na nan’. Saidai kawai na gyada kai. Ya shiga cikin kogon kukar. Ya zauna, ya yi kimanin mintuna 15, sannan ya fito.

Muka shiga mota muka wuce zuwa Funtuwa. Muna isa, sai ya kai ni wajen wani tela. Ya sanya aka gwada ni, aka dunka ma ni kaya har kala 25.

Nan na zauna gidan sa a Funtuwa har hutu ya kare. Da hutu ya kare ya kawo kudi naira 500 ya ba ni, ladar hutun da na yi masa. Sannan ya saya ma ni mashin ko babur sabo, samfurin Suzuki ya ba ni. Ya sanya ni a mota, aka maido ni Katsina. A lokacin ban fi shekara 14 a Duniya ba. Amma Shata ya nuna ma ni wannan gatanci.

An ce Shata na da kyauta. Kai ka zauna tare da shi. Ka tabbatar da hakan ke nan. A cikin alherin Shata, mi ya fi ba ka mamaki?

Dokta Kankara, tun da na ke da Shata, bai taba ce ma ni ‘zo ga kudi’, ko ‘zo ka amshi kudi’ ba. Wallahi summa tallahi, saidai ya bude ma ni aljihun rigar sa ko taguwar sa, ya ce in dauki iya abin da na ke so. Idan kuma na zura hannu na dauki kudin, sai ya ce ‘saura miliyan 17’ Watau ma’anar wannan furuci, shi ne irin alherin da mahaifi na ya rika yi masa, da amanar da ke tsakanin su. Duk abin da ya ba ni, daga cikin alherin da ubana ya yi masa ne. Da na dauki kudi daga aljihun sa sai ya ce ‘saura miliyan kaza’.

Wannan ya tabbatar ma Duniya cewa Shata ba ya mance alheri, kuma mutum da ke son a kullum ya rama alherin da aka yi masa.

Za mu ci gaba sati mai zuwa idan Allah Ya amince.

(An tsakuro wannan hira daga cikin kundin tarihin Shata na littafin Shata: Mahadi Mai Dogon Zamani)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: