Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din Asiya

Published

on

Suna: Asiya.

Labari: Jazuli Muhammad

Kamfani: Global Time.

Shiryawa: Abdulaziz Dan Small.

Bada Umarni: Ali Gumzak.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Abba El-Mustafa, Aminu Sharif Momo, Baballe Hatatu, Nuhu Abdullahi, Salisu S. Fulani, Garzali Miko, lawan Ahmad, Hadizan Saima, Aisha Jos da sauransu.

 

Shi dai wannan fim mai suna Asiya, an gina shi, a kan wata mai suna Asiya. A farkon fim din dai, an haskota ne su na zaune su na hira da Salisu S. Fulani. A nan take fada masa cewa za su yi tafiya. Daga nan sai a ka koma kuma labarin Asiya a gidan mijinta mai suna Nura.

 

Asiya ta zaune da mijinta lafiya a zahiri, amma kuma a badini hankalinta ya na kan tsohon saurayinta wato Khalifa. Duk da cewa Asiya matar aure ce, amma sai ta zabi yin sharholiya da tsohon saurayinta, domin kuwa su na haduwa duk sanda kike so kuma a inda su ke so, A sanadiyar wannan dabi’ar ne Asiya ta rasa ranta.

 

Watarana Asiya ta cewa mijinta Nura ta na so za ta je wani biki na danginsu. A nan take ya amince mata, kuma har ya bata wasu kudade domin ta kai a matsayin gudunmawar biki. Ranar da za ta tafi, Nura ne ya dauke ta da kansa ya kai ta har tasha domin ta hau motar da za ta tafi. Bayan ta shiga mota ta na jiran fasinjoji, sai su ka yi sallama ya juya ya tafi. Bayan Asiya ta tabbatar da Nura ya tafi ne, sai ta fito daga motar ta dakko kayanta ta ce wa masu kula da tashar cewa ta yi mantuwa, saboda haka za ta koma gida ta dakko abinda ta manta.

 

Ashe ita daman ta baro gida ne saboda su hadu da saurayinta Khalifa a Otel. Sai dai ta gamu da gamonta, domin kuwa bayan ta je Otel din ta na jiran isowar Khalifa. Sai dai da isowar Khalifa Otel din, sai ya riske ta ta mutu. Nan ya samu kansa cikin tashin hankali, kuma ya yi sauri ya fice daga dakin. A nan a ka shigo da ‘yan sanda kuma su ka ci-gaba da gabatar da bincike.

 

ABUBUWAN YABAWA

  1. An samu kwararrun jarumai a cikin wannan fim din.

  2. Sunan fim din ya dace da fim din.

  3. Hotuna da sauti sun fita rangadadau.

 

KURAKURAI

 

  1. A farkon fim din an nuno Asiya tare da Salisu S Fulani su na hirar su ta soyayya, bayan nan sai a ka rubuto shekara daya da ta wuce, sannan sai a ka koma labarin Asiya a gidan mijinta. A cikin labarin an nuna ta mutu, to idan har ta mutu ya a ka yi su ka hadu da Salisu har su ke soyayya?

  2. A lokacin da ‘yan sanda su ka kirawo Nura, sun shaida masa cewa sun samu gawar matarshi a Otel, kuma ya gaggauta zuwa domin ganin halin da take ciki. Amma sai a ka hasko shi kuma ya tafi tashar motar wai ya na neman ta.

  3. A lokacin da a ka nuna Asiya za ta fito zance wajen. Khalifa, an nuno ta ta fito da wasu kaya daban, amma kuma kafun ta karaso kofar gida kuma sai a ka kayan jikinta sun chanja. Ya ya a ka yi ta chanja kaya a hanya, daga cikin gida zuwa waje?

 

KARKAREWA

 

Fim din Asiya ya samu nasarori da yawa da kuma kalubale masu yawa. Amma dai an yi kokari sosai a aikin fim din.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: