Connect with us

LABARAI

A Rika Wanke Hannu Don Kaucewa Kamuwa Da ‘Coronavirus’, Inji Ministan Lafiya

Published

on

Karamin Ministan kiwon lafiya, Adeleke Mamora, ya yi magana game da cutar nan ta Coronavirus da ta barke a duniya a farkon shekarar nan.

Ministan ya bayyana cewa wanke hannu da ruwa da kuma sabulu zai taimaka sosai wajen kare jama’a daga kamuwa da wannan mugun ciwo da ke yawo.

Adeleke Mamora ya ba jama’a su tsabtace hannuwansu domin gudun kamuwa da cutar. Ministan ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi dazu.

Da ya ke magana a gidan talabijin Channels TV a Ranar Litinin, 2 ga Watan Maris, Ministan ya ce gwamnatin Nijeriya ta na bakin kokarinta game da cutar.

Mamora ya shaidawa manema labarai cewa amfani da ruwa da sabulu a cuda hannu, shi ne babbar hanyar da za a bi wajen rigakafin kamuwa da wannan cuta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: