Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Bai Dace A Sanya Siyasa A Batun Matsalar Kiwon Lafiya Ba

Published

on

Ya zuwa tsakar ranar biyu ga watan Maris, an gano bullar cutar numfashi ta Covid-19 a kasashen duniya sama da 60. A sa’i daya kuma, kasar Sin a matsayinta na kasar da ta samu gagarumin ci gaba wajen tinkarar cutar, tana iyakacin kokarin taimakawa sauran kasashe, inda ta samar da gudummawar kayayyakin kare cututtuka ga kasashen Koriya ta kudu da Japan da Iran.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha jaddadawa cewa, dukkan ‘yan Adam makomarsu daya ce, kuma hadin kansu shi ne makami mafi inganci a gare su. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka a kan kare lafiyar al’ummomin kasashen duniya, tana kuma kokarin samar da gudummawa gwarwadon karfinta ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar duniya.
Duk da haka, wasu ‘yan siyasa na kasashen yammaci, suna yayata jita-jita tare da bata sunan kasar Sin, ba tare da yin la’akari da ainihin gaskiyar abin da ya faru ba, don cimma muradunsu na siyasa, kuma babu abin da zai haifar illa lahanta hadin gwiwar kasa da kasa a kokarin da ake yi na dakile cutar, kuma hakan zai haifar da illa ga daukacin bil- Adam da suka hada da al’ummar Amurka.
Kamar yadda jaridar Washington Post ta bayyana a bayanin da ta wallafa, tun bayan da gwamnatin Amurka mai ci ta kama aiki, an dakatar da hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin kasashen Sin da Amurka, wanda hakan ya kuma haifar da babbar hasara ga ita kanta Amurka. Bayanin ya yi nuni da cewa, a yayin da jama’ar duniya ke dada karuwa, tabbas ne sabbin cututtuka za su bulla, don haka, ya kamata kasashen biyu su inganta hadin gwiwarsu a fannonin nazarin kimiyya da kiwon lafiya.
A hakika, ya kamata a mai da batun da ya shafi matsalar kiwon lafiya da ke damun al’ummar duniya a matsayin wata dama ta karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, a maimakon sanya batun siyasa.(Lubabatu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: