Connect with us

JAKAR MAGORI

Kotu Ta Garkame Mahaifi Shekara 14 Bisa Yunkurin Yi Wa Diyarsa Fyade

Published

on

Wata babbar kotu da ke garin Ado Ekiti ta garkame wani mahaifi mai suna Bashiru Adeyanju a gidan yari har na tsawan shekara 14 bisa yunkurin yi wa diyarsa mai shekaru 17 fyade.

Da ta ke yanke hukuncin, alkami mai sharia Monisola Abodunde, ba ta bayar da daman biyan tar aba ga wanda aka yankewa hukunci. Abodunde, ta samu wanda ake tuhuma da laifin yunkurin yi wa diyarsa fyade, sakamakon bayann da ya gabatar wa kotu da kuma shaidu da ya gabatar wa kotu. Alkami mai sharia ta bayyana cewa, masu gabatar da kara ba su nazarta lamarin yadda ya kamata ba na yunkurin lamarin yin fyade. Kotu ta samu wanda ake tuhuma da laifi. Bisa hujjoji da masu kare wanda ake tuhuma suka gabatar, sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko da ya taba aikata irin wannan lamari, domin haka, an kotu ta yanke masa hukuncin zama a gidan yari na tsawan shekara 14, in ji ta.
Ta bayyana cewa, an cire shekara uku a cikin wannan hukunci, saboda hukuncin zai fara ne tun lokacin da aka fara shariar.
Tun da farko dai lauya mai gabatar da kara Mista Wale Fapohunda, babban alkali na garin Ado Ekiti, ya bayyana wa kotu cewa, wanda ake tuhuma ya aikata wannan laifin ne a ranar 10 ga watan Satumbar shekarar 2017 a gida mai lamba 30 da ke kan titin Irona Street cikin garin Ado Ekiti. Ya kara da cewa, a wannan rana wanda ake tuhuma ya yi yunkurin yin lalata da diyarsa mai shekaru 17 da haihuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: