Connect with us

JAKAR MAGORI

Matashi Ya Yi Wa Kakarsa Mai Shekara 66 Ciki

Published

on

Wani matsashi mai shekaru 24 ya yi wa kakarsa mai shekara 66 ciki. Matashin tare da kakarsa sun dade suka yin lalata a boye ba tare da wani ya sani ba. An dai gano wannan mummunam lamari ne lokacin da kakar mai shekara 66 ta dauki ciki.

Wani mutum mai suna Normore Mudabanhu da ke zaune a yankin Dube, shi ya fara fallasa lamarin. Ya kara da cewa, shi bai ji mamakin faruwar lamarin ba, saboda sun dade suna yin lalata a boye. Mutane da dama suna fama da irin wannan lamari. Na dade ina ganin wannan lamari, saboda haka ba na jin mamakin faruwar lamarin, in ji shi.
Nan take iyalansu suka kira ganawa ta gaggawa, inda suka bayyana cewa, wannan lamari ya zubar musu da kima a idon mutane. Matashin tare da kakarsa sun nemi a yafe musu daga wannan laifin da ya faru, inda suka bayyana cewa, aikin shedan ne.
A yanzu dai kakar tana da ciki na tsawan wata uku wanda jikanta ya yi mata.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: