Connect with us

ADABI

Cikar Kungiyar Marubuta Mata Zalla Ta Mace Mutum Shekara Bakwai Da Kafuwa 

Published

on

Zinariyar Kungiyar Marubuta Ta Mata Zalla Mai Suna Mace Mutum Ta Shekara Bakwai

Ranar 3 watan 3 ne na shekarar 2020 ‘yayan kungiyar mace mutum ke nuna jin dadi da murna a kafofin sadarwa don nuna jin dadinsu da godiyar Allah da cikar kungiyar da ta zamo zakaran gwajin dafin kungiyoyin marubuta shekara bakwai cur da kafuwa. Abin murnar kuwa tun daga kafa kungiyar zuwa yau har yanzu ‘yan kungiyar suna nan rike da kambunsu na adabi suna alfahari da kayansu.

 

Tarihin kafuwarta

Mace mutum kungiya ce ta mata marubuta zalla wadanda suka hadu domin inganta rubutunsu da kasuwancin littattafanasu da suke zargin wasu na ci-da-guminsu. An bude wannan zaure na wannan ƙungiya a Fesbuk kuma aka yi mata suna da cewa “Mace Mutum” an kafa kungiyar ne a ranar 3/3/2003.

Kafa kungiyar ya taso ne ta hannun shahararriyar marubuciyar nan Rahma A. Majid. Tunanin ya faro daga wani (Post) da marubuta maza suka dinga yi akan mata marubuta sun lalata adabi suna fitar da littafai marasa kangado, daga nan Rahma Abdulmajid ta yi wani rubutu mai taken akuyar marubuta mata tayi kuka, daga nan sai mata marubuta suka fara tattaunawa akan neman mafita.

Abu na farko na samun mafitar shi ne tattara kan marubuta mata kasancewar Rahma Abdulmajid bata san mata marubuta da yawa ba. Don haka sai aka dorawa Sadiya Garba Yakasai da Fauziyya D Sulaiman alhakin tattara marubuta mata, daga nan aka tsayar da rana aka yi taron farko gidan Sadiya Garba yakasai. Tafiyar ta tabbata kungiya bayan zaman mahalartan farko don ganawa a gidan marubuciya Sadiya Garba Yakasai. Cikin mutanen da suka hau suka kafa wannan kungiya akwai:

Sadiya Garba Yakasai

Rahma Abdulmajid

Fauziyya D Sulaiman

Bilkisu Yusuf Ali

Hauwa Husaini Hashim

Hauwa Lawan Maiturare

Lubabatu Yau

Hadiza Nuhu Gudaji

Kilima Abba Abdulkadir ( 33)

Umma Sulaiman ‘Yan’awaki ( Anty Baby)

Maimuna Idris Sani Beli

Mami Yusuf Yakasai

Zahra’u Baba Yakasai

Zuwaira Isa Danlami

Nafisa Tasiu

Alawiyya Wada Isa

Ummulkhairi Kabir

Farida Ghaci

Bilkisu H. Muhammad.

Wadannan su ne suka zo taron farko don kafa kungiyar mace mutum.bayan muhawara kan sunan da kungiyar da ya dace Bilkisu Yusuf Ali ta kawo shawara a nadawa kungiyar sunan Mace Mutum kuma ‘yan kungiya suka amince.

An bude gidaje daban-daban a Facebook wanda mallakar mace mutum ne kuma kowanne da manufar bude shi kuma kashin bayan nasarar ci gaban mace mutum duk ya taso daga wannan gidaje. Daga cikinsu akwai:-

 

Mace Mutum Marubuta (Wannan na Mata zalla ne marubuta ‘yan kungiya)

Mace mutum Kowa ( Na kowa da kowa maza da Mata marubuta da masu nazari Marubutan da suka raya mace mutum kowa suna da yawa, sai dai kaan daga cikinsu, akwai Sadiya Garba Yakasai da Rahma Abdulmajid da Maimuna Idris Sani beli da Hauwa’u Hussein Hasheem da Malam Nasir G Ahmad Hamza Dawaki da Danladi Haruna da Malam Bashir Na’iya Gwammaja da sauransu da dama.

 

Mace mutum Sababbin marubuta (wannan kuma an ware Sababbin marubuta ne don yi musu bita da tattauna matsalolinsu)

MAMSHOS wannan kuma an ware shi ne aka ware wasu marubuta aka yi musu seminer ta wata wata guda Online aka yi training aka ba da certificate

(EDCO group) shi kuma Ana tattauna ci gaban kungiya da taimakon yayanta amma EDCO ne kadai a wajen

(MM MULTIPLE purpose) Shi kuma an kirkire shi ne don samawa kungiya ayyukan yi da kudin shiga

 

Manufofin Mace Mutum

Babbar manufar wannan ungiya ta Mace Mutum ita ce assasa samar da litattafai na kagaggun labarai na Hausa, musamman wadanda suka shafi mata marubuta. Sannnan a samar da wata kungiya da za ta hada kai tare da sanya wa mata marubuta su rinka magana da murya guda.

Manufofin mace mutum akwai, farfado da adabi da gyaransa da gyara harkar rubutun da ma marubutan sannan da karbawa marubuta mata ‘yancinsu da zamar da su mutanen ta hanyar gyara musu rubutu da daukar nauyin buga shi da ma sanya musu shi a kasuwa ta sayar mu su ta basu kudadensu.

Cikin manufofin wannan kungiya akwai bayar da horo ga sabbin marubuta musamman mata domin a ji amonsu a duniya. Da kuma koyawa marubuta hanyar iya zama da gindinsu da da dabbaka zumunci da kuma marubatan su zauna a inuwa daya.

Wata manufar kuma ita ce taskacewa tare da raya adabin Hausa da kuma inganta su ta hanyar zamanantar da shi wato amfani da shi a kafafen sada zumunta musamman Fesbuk (Facebook).

 

Ayyukan Mace Mutum

An yi wa kungiyar rijista da hukumar CAC a matsayin Kungiyar da ba ta gwamnati ba (NGO). Kuma sun gabatar da wasu ayyukan nasu ta kafafen sada zumunta na Fesbuk. A cikin wannan lokacin ma sun rubuta littafai hudu sun kuwa hada da; Hannu da Yawa, da kuma Tatsuniyoyin Yara na 1-3. Tuni an wallafa litttafan kuma an kaddamar da su a 2014 inda aka tara kudi sama da naira miliyan 5.

Kungiyar mace mutum ta samu nasarar canza tunani da alkaluman marubuta a kan yin rubutu na batsa da yin rubutu marasa ma’ana zuwa yin rubutu masu cike da ma’ana da tsari wanda duniyar adabi ta sauya.

Cikin irin ayyukan wannan kungiya akwai misali, a “Mace Mutum Kowa, akwai shirin “Ina Gwanayenmu Suke?” Shiri ne da ke hada muhawara da mutanen da ke mabambantan jihohi da ke cikin gidan na Mace Mutum Kowa, akan zabo batutuwa guda biyu walau a kan kiwon lafiya ne ko zamantakewa da dai sauransu. Akan hada jihohi biyu a yi muhawara a kansu, a dukkanin ranar asabar ake gabatar da shirin zuwa lahadi da safe sai a fadi sakamakon, akan bawa zakaran jihar kyauta ta katin waya a kowane mako.

Cikin nasarorin da wannan kungiya ta samu an yaye sabbin marubuta matasa da kara fadada tunaninsu domin samar da ayyukan adabi masu tsafta. Akwai Mitin (Meeting)

da a ke gudanarwa ranar litinin duk mako kuma a na tattaunawa ne don ci gaban kungiya kuma aga wanda suke shiga don inganta kungiya. A nan a ke fiddo matsalolin kungiya ko ci gabanta.

Har ila yau, akwai filin su Aunty Gudaji fili da a ke gudanarwa lokaci zuwa lokaci da ake kawo gajerun labarai don gogewar sababbin Marubuta da kuma masu son a gyara musu da sauransu da dama.

Cikin nasarorin an kai kayan tallafi a gidajen marayu na Nasarawa da hukumar Hisba da taimakawa daidaikun marubuta ko iyalansu da ke bukatar tallafi.

 

Babbar Nasara

Gasar Hikayata da gidan Radiyon BBC ke gudanarwa halastattun ‘yan kungiyar mace mutum sun dau kambu har sau biyu.

A shekarar 2016 Amina Hassan Abdussalam ta zo ta biyu a gasar

A shekarar 2017 Maimuna Idris Sani Beli ta lashe gasar da kambu na Farko.

Bilkisu Yusuf Ali ta zama a cikin alkalan na gasar Hikayata na shekarar 2018 da 2019 wannan babbar nasara ce da kungiyar mace mutum take alfahari da shi.

Kasancewar ‘yar Kungiyar Mace mutum Fauziyya D Sulaiman cikin marubutan wasan kwaikwayo na gidan talabijin din Arewa 24 na Dadin Kowa da kwana dasa’in ita da Maimuna Beli ya nuna nuna irin ingancin rubutun ‘ya’yan mace mutum a idon Duniya.

 

Matsaloli

Babu inda nasara ta taba tabbata ba tare da matsaloli ba. Babbar matsala da mace mutum ta fuskanta ta tadewa da yarfe da kun-ji-kun-ji da burin kar ta kai labari duk kungiyar ta tsallake su don haka ma ta lullube su da karin maganar nan ta dattin gora a ciki a ke shanye shi.

 

A Karshe

Bahaushe yana cewa idan rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta. Muryar Mace Mutum a na jin amonta za a ci gaba da jin amonta, amonta da ayyukanta da hadin kanta zai cigaba da wanzuwa har abada muna fata! Allah ya raya Mace Mutum!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: