Connect with us

RIGAR 'YANCI

‘Da Kudaden Haraji Da Gwamnatin Kano Ke Gudanar Da Ayyukan Cigaban Al’umma’

Published

on

Mai ba Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Shawara a kan tattara Haraji Hon. Alhaji Habibu Saleh Mailemo ya bayyana cewa ana tattara haraji na sama da Naira Miliyan daya da Naira 500 ko 600 ko 700 harma wani lokacin akan sami Biliyan biyu a duk wata a jihar Kano wanda ake gudanar da ayyuka dasu basai an saurari jiran kaso daga Gwamnatin tarayya ba.

Ya yi nuni da cewa ko Gwamnatin baya da Gwamna Ganduje ya gada ta tafi tabar wasu manyan ayyuka da bata karasa ba irinsu gadar sama data taso daga Fagge zuwa Kan titin Murtala da gadojin kasa da Gwamnatin Kwankwaso ta kaddamar guda Biyu wancan lokacin akwai  akwai ayyuka da suka rage ba a yi ba da suka hada da fitilu, rela-rela da sauran abubuwa amma saboda kyakkyawan kudurin Gwamnatin Ganduje kar aiki ya tsaya dan kar’a sani tsaiko na tafiyar da aikin sama da N450,000,000 Gwamna ya ware daga kudaden haraji da ake tarawa a jihar Kano aka cigaba da ayyuka.

Hon. Alhaji Habibu Saleh Mailemo ya yi nuni da cewa kowane watan Duniya akan sami kudin haraji a jihar Kano kuma wadannan kudade su suke zamewa Gwamnatin Kano wukar kugu  na cigaba da tafiyar da  Gwamnati kafin kudin yazo daga kason wata-wata na Gwamnatin tarayya.

Mashawarcin Gwamnan Kano akan tattara harajin Hon. Habibu Saleh Mailemo ya ce, Gwamnatin Kano tana gudanar da ayyuka da dama na kyautata cigaban al’umma a vangarori da dama. Ko a baya lokacin yana shugaban karamar hukumar Fagge da irin ku daden haraji da ake tattarawa Gwamnati ta rika basu dan gudanar da ayyuka wanda ba dan irin wannan dauki da ake basu ba da yawanci kananab hukumomi sun kasa tafiyarda ma’aikatansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: