Connect with us

LABARAI

EFCC Ta Kama ’Yan ‘Yahoo Boys’ Shida A Ibadan

Published

on

Wani dan karamin akwatin mamata da ake kyautata zaton cewa kayayyakin tsumburkai ne a cikinsa da aka samu a wajen wani matashi mai shekarun haihuwa 38 wanda kuma ake kyautata zaton cewa yana cikin gungun ‘yan dandatsan nan da aka fi kira da Yahoo Boys, mai suna, Azeez Adebowale, ya shiga hannu a lokacin da jami’an hukumar EFCC suka kai mamaya a gidansa da ke Ibadan a ranar Litinin.

Adebowale, wanda yay i ikirarin yana amfani da akwatin mutuwar ne a matsayin ma’ajiyar sabulu, yana daya daga cikin mutane shida da hukumar ta EFCC ta kama a bayan ta shafe makwanni tana bin diddign su a lokacin da ta sami wasu rahotannin sirri a kan ayyukan harkalla na dandatsan da suke yi a yanar ta gizo.

Mutane shidan da ake tuhuma sun hada da wata budurwa mai suna, Toyinsola Bolumole, jami’an hukumar ta EFCC da ke Ibadan ne suka kama ta a wani waje da ke wajajen Anguwar Oluyole da Alao-Akala, na dadadden birnin na Ibadan.

Sauran sun hada da, Ifelowo Ololade, Sonuyi Ayodeji, Folarin Oladele Olayinka da Aluko Olawale.

Kayayyakin da aka samu a tare da su sun hada da, kananan motocin shiga guda hudu, manyan wayoyin hannu masu tsada kala daban-daban da kuma katunan ATM na ciran kudi a banki masu yawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: