Connect with us

TATTAUNAWA

Samar Da Ilimin Alkur’ani Ga Mata Ne Burina – Sayyada Hafsat

Published

on

Wakilin LEADERSHIP A YAU, ISA ABDULLAHI GIDAN BAKKO, ya sami zantawa da ’yar fitaccen masanin hadisi na duniya, Shekh Ibrahim Saleh Maiduguri, wato SAYYADA HAFSAT IBRAHIM SALEH, jim kadan bayan kammala walimar saukar haddar Alkur’ani da makarantar Taskiyya ta shirya a Zariya, wanda wannan makaranta ta karrama ta kan yadda ta jajirce wajen kafa makarantun haddar Alkur’ani a sassan duniya, ba Nijeriya kawai ba.

Da farko ta fara da nuna godiya da karramawar da wannan makaranta ta yi ma ta, kuma ta amsa tambayoyin wakilinmu kan makarantun haddar Alkur’ani da ta bude. Ga dai yadda tattaunawarsu ta kasance:

 

Ya ki ka dubi wannan karramawa da a ka yi ma ki a Zariya?

Babu ko shakka, wannan karramawa da aka yi ma ni na ji dadi fiye da tunanin dan adam, ina godiya ga wannan makaranta da mahukumtan makarantar suka ga dacewa tad a a ba ni wannan kyauta ta karramawa. Kuma ina addu’a ta musamman ga mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, Allah ya kara ma sa lafiya, da hikima domin ya sami saukin sauke nauyin da Allah ya dora ma san a sarki a wannan babbar kasa ta Zazzau, da kuma ayyukan day a ke yi wa addinin Musulunci.

An karramaki a yau a dalilin bude makarantun haddar Alkur’ani mai girma, wani karin haske za ki yi ma na, kan wadannan makarantu?

Lallal Allah ya ba ni ikon bude makarantun haddar Alkur’ani mai girma ba a nan Nijeriya kadai ba, domin zuwa yau da mu ke zantawa da kai, mun bude a Cadi da Kamaru da kuma Sudan.Kuma baya ga ilimin haddar Alkur’ani, mu na cusa ilimin addinin Musulunci fannoni da dama a wadannan makarantu.

 

Yaushe ki ka fara tunanin assasa wadannan makarantu?

Babu shakka, a shekara ta 2003, na yi tunanin samar da makarantu domin mata zalla da za a koyar da su ilimin Alkur’ani mai girma da sauran fannonin ilimi kamar yadda na bayyana ma ka a baya.

 

Zuwa yau, a kalla, kin a da dalibai nawa da suke wadannan makaratu a kasashen da ki ka bayyana?

To, fadin yawan daliban farar da garaje ba sauki, amma a kasasashen Kamaru da Sudan da Cadi, a kwanakin baya na ziyarci makarantun, wadanda na dora ma su aiwatar da ayyukan makarantun sun bayyana ma ni cewar daliban na karuwa daga lokaci zuwa lokaci, dalilin da ya sa ke nan b azan iya furta yawansu a halin yanzu ba, amma dalibanmu da su ke karatu a makarantunmu da suke Maiduguri sun kai kimanin 3750.

 

Bayan dalibai da suka kammala karatu a makarantun da ki ka kafa, wasu tsare – tsare aka yi ma sun a ci gaba da karatu?

Lallai mu na da kyawawan tsare-tsare na duk dalibar da ta haddace Alkur’ani, mu na shiga gaba mu nemar ma ta makarantar da za ta cigaba da karatu a ciki da wajen Nijeriya da kuma kasashen da na bayyana ma ka a baya. Kuma saboda mu na sa wasu darussan ilimin zamani a makarantun, wasu sun kammala babban digiri kan hada magunguna da sauran matakan ilimi daban-daban.

 

Me ma ya sa ki ka yi tunanin mata ne kawai za su shiga wadannan makarantu da ki ka kafa?

Bin day a san a fara wannan tunani na ilmantar da mata shi ne, domin kowa ya sani, in har mace tan a da ilimi, babu shakka iyalinta da sauran al’umma za su kasance ma su ilimi da kuma tarbiyya, kuma wadannan makarantu da na kafa tun farko mahaifi nay a fara bude ma na makaranta daya ta mata zalla, daga nan ne da kwarin gwiwar day a ke ba ni har zuwa yau na sami damar bude makarantun da na bayyana ma ka a baya da kuma kasashen da su ke.

 

A karshen za mu iya cewar, burin ki ya cika ke nan na bunkasa ilimin ma ta da ya shafi ilimin addini da na zamani, musamman ilimin Alkur’ani mai girma?

A gaskiya ya fara cika, amma fa akwai wasu tsare-tsaren bunkasa ilimin mata da na sa wa gaba, Ina dai addu’ar Allah ya cika ma ni buri idan har Ina raye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: