Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Gaskiya Dokin karfe: Tsakure A Kan Ci Gaban NIS Da Ba A Taba Gani Ba Tun Kafuwarta

Published

on

Nade-naden mukamai a Gwamnatin Tarayya lamari ne da aka bai wa Shugaban kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan kasar nan wuka da nama a kai, don haka shugaban yake darjewa ya zabi wanda yake ganin shi ne mafi cancanta a wani mukami don samun nasarar aiwatar da ayyukan ci gaba. Bayan Shugaban kasa ya zaba ya nada, sai nauyi ya koma kan wanda aka zaba na tabbatar da kawo ci gaban da aka tasa a gaba. Bisa al’ada, Jami’in da aka nada kan tantance hanyoyin da zai bi wajen samun nasarar, inda a karkashin haka zai nada tawagar zakakuran ma’aikata masu kwazo, da tsara kudurorin da za su taimaka wajen kaiwa ga gaci.

Tun daga lokacin da Shugaba Buhari ya nada Muhammad Babandede a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), a shekarar 2016, masu lura da al’amuran yau da kullum sun zuba ido su ga me zai yi musamman a karkashin gwamnatin da ‘Yan Nijeriya suka zaba ta kawo masu canji mai ma’ana. Amma tafiya ba ta yi nisa ba sai suka fahimci cewa tabbas Shugaban kasa bai yi zaben tumun-dare ba saboda tsare-tsaren da Babandede ya fara shimfidawa na kawo sauyi da ci gaba daidai da zamani a NIS. Wannan ba abin mamaki ba ne, kasancewar Juma’ar da za ta yi kyau; tun daga Laraba ake gane ta.
A cikin shekara 57 da kafuwar NIS, ba a taba samun manyan ayyuka da aka gudanar birjik kamar lokacin da shugabanta na yanzu, CGI Muhammad Babandede ya karbi ragamarta ba. A karon farko a duk tsawon wadannan shekarun, Hukumar ta gina gidajen Manyan Jami’anta na Shiyya da Kwanturololinta, ta gina sansanonin Jami’anta da ke sintiri da tsaron kan iyakokin kasa domin kyautata yanayin ayyukansu da kara musu kaimi tare da daga martabarsu a idon sauran takwarorinsu na kasashe rainon Faransa da suke aiki kusa da juna.
Haka nan NIS ta yi nasarar gina ofisoshinta na shiyya da jihohi a sassan kasar nan, lamarin da ya magance tarnakin da Jami’in NIS ke fama da shi wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata. Bugu da kari, tanadin muhimman abubuwan da ake bukata na aiki da ya zama kamar cin-kwan-makauniya a baya, daga lokacin da Shugaba Buhari ya tabbatar da CGI Muhammad Babandede a matsayin Shugaban NIS,an samu karin ofisoshi da sansanonin hukumar da ke gudanar da ayyuka na musamman a kan-tudu, da gabar-teku, da tashoshin jiragen sama daga guda Takwas (8) zuwa Ashirin da Takwas (28). Bayan haka, an samar da karin ofisoshin da ke bayar da Fasfon tafiye-tafiye zuwa waje musamman a Biranen da suka fi hada-hadar kasuwanci kamar Legas, Kano, Fatakwal, Ibadan inda tuni suka dukufa ga aiki domin biyan bukatun dimbin ‘Yan Nijeriya masu neman Fasfo. A karkashin wannan yunkuri, NIS ta inganta tsarin neman Fasfon ta hanyar intanet domin saukaka wa masu nema matakan da ake bi ta yadda a ta nan za su aika da bukatarsu, a ta nan za su biya kudin suna kwance a gidansu ba sai sun nemi mai-shiga-tsakani ba kamar yadda ake yi a baya.
Wannan ya saukaka wa ‘Yan Nijeriya bin dogayen layuka na neman Fasfo da sauran abubuwan da NIS ke bayarwa, da kawar da kumbiya-kumbiya da biyan kudin komai yadda yake ba tare da caje-caje na ba-gaira-ba-dalili ba.


Wani aiki abin alfahari da NIS ta samu nasarar aiwatarwa shi ne kaddamar da aikin yi wa daukacin baki ‘yan kasashen waje da ke kasar nan rajista ta shafin intanet wanda Shugaba Buhari ya kaddamar a watan Yulin 2019. Wannan aiki ya nuna baro-baro a fili irin kokarin da NIS ke yi wajen tattara sahihan bayanan bakin da ke cikin kasar nan ba tare da cin-hanci da rashawa ba. Afuwan da Shugaba Buhari ya yi wa bakin wajen ta lallai kowa ya tabbatar ya yi rajista cikin wata shida kuma kyauta, ta taimaka wajen sanin adadin bakin da bayanansu, inda hakan ya zama wani kyakkyawan yunkuri na kara inganta tsaron kasa da kuma sanya idanu a kan abubuwan da bakin ke aiwatarwa a cikin kasa.
Bayan haka, samar da sabon tsarin Biza na shekarar 2020 wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar a hukumance a ranar 4 ga Fabarairun 2020, wani namijin kokari ne da NIS a karkashin CGI Babandede ta yi domin daukan matakan inganta kula da shige da ficen kasa. A baya NIS tana da Biza hawa-hawa ne guda shida kacal, amma bisa sabon tsarin da aka kaddamar, an kara yawansu zuwa Saba’in da tara (79) bisa la’akari da karuwar bukatar kungiyoyi da daidaikun baki daga kasashen duniya ta shigowa cikin kasa. Ko ba a fada ba, kowa ya san wannan yana bukatar a inganta matakan Bizar Nijeriya domin inganta tsaro, da bunkasa tattalin arzikin kasa da tabbatar da gaskiya da rikon amana. Alfanun sabon tsarin Bizar na 2020 bai tsaya nan ba, har ila yau ya kara yaukaka zumuncin Nijeriya da wasu kasashe wajen kyautata wa juna ta fannin bayar da Biza a tsakaninsu, da kara wa’adin aikin Biza da irin wadda ake bayarwa, wadanda a baya ‘Yan Nijeriya suna shan wuya a kansu a wurin kasashen kafin bullo da sabon tsarin Bizar.
Wakazalika, domin nuna kwarewar aiki, NIS a karkashin CGI Babandede ta gabatar da Kundin Matakan Kula da Iyakokin kasa da za a yi aiki da shi a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023. Babandede ya kawo tsarin samar da kundin aiki da hukumar za ta rika amfani da shi ne a tsakanin wasu shekaru domin sha’anin kula da shige da ficen Nijeriya ya kasance yana tafiya da zamani. La’alla tsarin da ya yi tasiri a cikin wasu shekaru ba zai gamsar ba a wasu shekaru na gaba, don haka shugaban hukumar ya ce za a rika bitar kundin da hukumar ke aiki da shi lokaci-zuwa-lokaci domin tabbatar da cewa ba-a-cin-tuwo-da-miyar-bara.
Sannan an yi la’akari da irin rawar da kundin zai taka wajen tabbatar da tsaron kasa, domin matukar tsaron kan-iyakokin kasa ya inganta, kasa za ta kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A jawabinsa yayin kaddamar da kundin, CGI Babandede ya ce kundin ya yi tanadin magance matsalar tsaron kasa, da tsaurara tsaron iyakoki da kuma tsara kan-iyakoki su zama hanyoyin hada-hadar kasuwanci da kasa za ta karu da su.


“Kundin zai kuma tabbatar da gudanar da aiki cikin gaskiya da rikon amana, zai rage cin hanci da rashawa, zai taimaka wajen tabbatar da cewa ana kare hakkin dan Adam, sannan za mu yi tsayin-dakar ganin mun hana masu fasa-kwauri da safarar bil’adama cin karensu ba babbaka wajen shiga ko fita cikin kasar nan”.
Manyan shugabanni da suka halarci taron, irin su Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna, da shugaban kwamitin kula da al’amuran cikin gida na Majalisar Wakilai ta kasa, Nasir Daura da Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Bakin Waje da Mutane Masu Neman Mafaka, Basheer Mohammed, sun yaba da samar da kundin, kana suka tabbatar da cewa Kundin zai agaza wa kokarin Nijeriya na shawo kan karuwar aikata miyagun laifuka a tsakanin iyakokin kasa, da shige da ficen baki ta haramtacciyar hanya, da safarar bil’adama kamar yadda aka tsara a manufofin bunkasa ci gaban kasa da ke kunshe a cikin shirin Farfado da Tattalin Arziki na Gwamnatin Tarayya.
Hatta ita kanta Babbar Jami’ar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya, Misis Ukamaka Osigwe wadanda suka taimaka wajen aikin tsara kundin, ta ce babban dalilin da ya sa aka tsara kundin shi ne fito da kwararan hanyoyin da za a inganta kula da shige da ficen baki a Nijeriya a karkashin ayyukan hukumar da ke jagorantar lamarin, wato NIS.
Sabon Kundin na matakan inganta kula da iyakokin kasa; daya ne daga cikin sauye-sauyen da hukumar NIS ke aiwatarwa bisa shugabancin Muhammad Babandede domin tabbatar da tsaron kasa, bunkasa tattalin arziki da yin aiki cikin gaskiya da rikon amana, kamar yadda yake kunshe a cikin kudurorin gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Ta fuskar yaki da cin-hanci da rashawa kuwa, NIS ta zama jagaba kuma abar koyi ga sauran hukumomin gwamnati, kasancewar Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta ICPC da knata ba sako ba, ta yi kira ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati a daukacin fadin kasar nan su yi koyi da Hukumar wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa a cikin ayyukansu.
Shugaban Hukumar, Farfesa Bolaji Owasanoye ya yi kiran, sa’ilin da CGI Muhammad Babandede ya gayyaci hukumar ta zo ta sanya ido yayin da ya kira Kwanturololi na jihohi da shugabannin manyan shiyyoyin hukumar su gabatar da bayanan ayyukan kwangiloli da NIS ta bayar a sassan kasar nan.
ICPC ta bayyana cewa ba a taba samun wata hukuma ko ma’aikatar gwamnati da ta gayyaci hukumar na musamman domin ta sanya ido a kan yadda ake gabatar da bayanan irin kwangilolin da aka bayar a karkashinta ba, sai NIS.
Da yake jawabi a lokacin taron, CGI Muhammad Babandede ya yi bayanin cewa bisa kudirin gwamnati mai ci yanzu na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da ayyukan gwamnati, ya sa sukan gayyaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa zuwa taronsu na bayyana yadda hukumar ta bayar da kwangilolin ayyukanta domin fitar da komai a fili babu kumbiya-kumbiya.
A yayin taron dai, kowane Kwanturola an kira shi ya yi bayani dalla-dalla a kan kudin aikin da aka bayar da kuma yanayin da aikin da ake yi ya kai. Wannan zai sa a gane shin aikin da aka yi ya yi daidai da kudin da aka fitar ko akwai lauje cikin nadi. Kuma domin komai ya fito fili baro-baro, CGI Babandede ya ce da zarar an samu wani abu da ba a gane kansa ba, ICPC za ta gudanar bincike, shi ya sa ma suke bai wa hukumar kwafen takardun bayanan kwangilolin nasu domin bin ba’asi idan bukatar hakan ta taso.
Babandede ya ci gaba da bayanin cewa shirya taron bitar ayyukan da NIS ke gudanarwa ya taimaka wajen warware wasu mishkiloli da ka iya tasowa musamman wurin takaddamar abin da ya shafi adadin kudin da aka bayar na aiki da kuma yanayin matsayin da aiki ya kai wajen kammalawa.
“Duk abin da muke yi a nan a bayyane yake, mun magance mishkilolin da ka iya tasowa na cewa kaza muka bayar na aiki, kuma wadanda ake bayar da aikin bisa kulawarsu su ce abin ba haka ba ne. Idan mun hadu wuri daya sai a yi keke-da-keke. Tun da aka nada ni Kwanturola Janar na NIS (shugaban hukumar) ban taba kiran wani Kwanturo na jiha na neme shi ya rattaba hannu a kan takardar shaidar kammala aiki ba saboda na san shi (don neman alfarma). Ban taba ce wa wani ya sanya hannu a takardar shaidar kammala aiki alhali ba a kai ga kammalawa ba sam. Ku ne za ku je ku duba ayyukan da kanku sannan ku tabbatar da cewa kun gamsu da aikin da aka yi, daga bisani ku rattaba hannu kuma daga nan duk abin da zai biyo baya ku za ku dauki alhakinsa. Haka muke gudanar da ayyukanmu,” a wani bangare na jawabin CGI Babandede ranar da aka gudanar da taron.
Bisa wadannan dimbin manya ayyuka na ci gaba daidai da zamani, kima, daraja da martabatar NIS ta karu ba a cikin gida ba kawai har da kasashen ketare inda har wasu kasashen sun fara garzayowa Nijeriya domin neman koyi da hukumar.
A karshen watan Fabarairun 2020, Hukumar Shige da Fice ta Gambiya ta yo takakkiya daga kasarta zuwa shalkwatar NIS domin karin sani da neman hanyoyin kyautata tsaron kan-iyakokin kasa. A jawabinsa, shugaban tawagar ta Gambiya, babban sakataren ma’aikatar cikin gida ta kasar, Moussier Assan Tangara, ya lura da cewar Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta zama abar alfahari ga Nahiyar Afirka, kana ya yaba wa NIS a bisa tsare-tsare da sauye-sauyen aiki masu ma’ana da hukumar take amfani da su a halin yanzu.

Wakilinmu ya nakalto cewar, a karon farko jami’an hukumar shige da fice na kasar Gambia sun samu horo da dabarun aiki a makarantar horar da jami’ai na NIS da ke Jihar Kano.
Sauran wasu muhimman ayyuka da suka kara wa NIS tagomashi tare da tsere-wa-tsara a karkashin CGI Babandede sun hada da bullo da tsarin bayar Biza nan-take a kan iyakar da bako ya shigo cikin kasa ga ‘Yan Afirka wanda a halin yanzu aka takaita yi in ba a filayen jiragen saman da aka zaba ba saboda tsaro. Wakazalika, Katafaren ginin fasahar zamani da aka kaddamar a shalkwatar NIS manuniya ce da irin yadda NIS ke tafiya kafada-da-kafada da zamani a karkashin CGI Babandede. Musamman an samar da ginin ne domin ya zama Babbar Ma’ajiyar Adana dukkan bayanan Biza, Fasfo, Rajistar Bakin Waje, Izinin Zama a Cikin kasa da sauran bayanan da suka shafi shige da fice. Ba NIS kadai ba, hatta sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su ci gajiyar wannan musamman wajen samun bayanai don tsara manufofin gwamnati da suka shaifi kai-komon jama’a, da shaidar mutum da bibiyar tarihin tafiye-tafiyen mutum wadanda suke zama ginshikai ta fuskar tsaurara tsaron kasa.
Wadannan abubuwa da muka tsakuro kadan ne daga cikin nasarorin da NIS ta samu a karkashin CGI Babandede, domin a tsakanin shekaru biyu zuwa uku baya, Hukumar ta NIS ta samu sauyin da ba a taba gani bat un kafuwarta kimanin shekaru 57 da suka gabata. Sirrin wannan nasara kuma shi ne riko gaskiya wanda masu iya magana kan yi wa kirari da “dokin karfe”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: