Connect with us

LABARAI

Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Bauchi Wa’adin Kwana 21

Published

on

Kungiyar Kwadago ‘Nigeria Labour Congress’ (NLC) reshen jihar Bauchi, ta baiwa gwamnatin jihar Bauchi wa’adin kwanaki 21 da ta zo su ci gaba da tattaunawa kan sabon tsarin albashi mafi karanci na dubu 30 ko kuma ta ci gaba da fuskantar tirjiyarta.

A wani taron manema labaru da suka kira da tsakar ranar Yau Juma’a, hadakar kungiyoyin Kwadagon sun ce sun cimma matsayar gargadin gwamnatin jihar ne lura da jan kafar aiwatar da sabon tsarin da suke fuskanta, don haka ne suka nemi a dawo tuburin tattaunawa domin kaiwa ga cimma matsayar da suke muradin a cimma.

Danjuma Saleh, Shugaban kungiyar NLC reshen jihar Bauchi, shine ya jagoranci taron manema labarun, ya bayyana cewar sabon tsarin albashi mafi karanci na dubu 30 ya jima da zama doka a kasar nan, don haka ne suke neman gwamnatin jihar ta amince su dawo kan teburin tattaunawa domin fahimtar juna yadda ya kamata.

LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar a kwanakin baya dai gwamnatin jihar da kungiyar kwadagon sun cimma matsaya a tsakaninsu don aiwatar da sabon tsarin albashin daga kan ma’aikatan da suke matakin albashi na 1 zuwa na 6, inda suka tashi da zimmar za su ci gaba da tattaunawa kan albashin ma’aikata daga 7 zuwa sama zaman da ya gagara ci gaba da iyuwa.

Shugaban NLC ya ce; “Mun tattauna a matsayinmu na masu wakiltar jama’a muka kuma dauki mataki da tsaida matsaya. Dangane ne da aiwatar da sabon tsarin albashi mafi karanci na kasa na dubu 30, wanda a gaskiyar magana har zuwa wannan lokacin jihar Bauchi ba ta aiwatar da wannan sabon tsarin ba, kuma muna fuskantar maganganu daga mambobinmu wanda sun amince da mu ne domin mu wakilcesu.

“Kan haka mun tsaida matsayar cewar wadanda suke wakiltar gwamnati akwai sakaci ta bangarensu wajen ganin an hanzarta wannan tattaunawa don ganin an kai ga cimma matsaya kan lamarin wanda a zahirin gaskiya ya kamata ne a ce an yi tattaunawar kan lokacin da ya kamata don tabbatar da aiwatar da sabon tsarin. A bisa hakan ma’aikata sun zaku matuka.

“Don haka hadaddiyar kungiyar kwadago tana kira da babban murya wa gwamnatin jihar Bauchi da ta amince a gaggautawa wajen ci gaba da tattaunawa domin aiwatar da sabon tsarin albashi da gwamnati ta sanya shi ya zama doka kafin a kai ga yin dokar ya ce sai an tattauna a tsakanin bangarorin da abin ya shafa, da fari an fara amma abin ya zo ya tsaya, don haka muna kiran gwamnatin da ta zo mu zauna mu ci gaba da tattaunawar nan cikin gaggawa. Rashin yin hakan ba zai sanya mu tabbatar da ko za a samu zaman kyakkyawar dangantaka tsakanin kungiyar kwadago da gwamnati ba; domin mu kanmu muna shan matsi daga mambobinmu wanda aikinmu ne duk ahin da ya taso na hakkinsu mu tabbatar mun nemo musu an kuma ba su shi,” A cewar Shugaban.

Don haka Danjuma Saleh ya shelanta cewar sun baiwa Gwamnatin jihar wa’adin kwanali 21 da ta tabbatar ta dawo sun ci gaba da tattaunawar ko ta fuskaci tirjiya daga garesu, “Kan hakan, mun baiwa gwamnati wa’adin kwanaki 21 da muke so a dawo a ciki gaban da tattaunawar nan kafin karewar wa’adin kwanaki 21 a samu a kai ga tsaida matsaya domin aiwatar da sabon tsarin biyan albashi mafi karanci na dubu 30. Da kare-karen da ya dace a yi daga mataki na 7 zuwa na sha 14,” A cewar NLC.

Daga bisani ya nemi mambobin kungiyar da su kwantar da hankulansu, yana mai nanata cewar kungiyoyin kwadago a tsaye suke wajen tabbatar da sun nemo musu hakkokinsu cikin lumana da bin doka.

Daga bisani Alhaji Saleh ya gargadi gwamnatin da cewar da zarar wa’adin ya zarce ba tare da yin abin da suke so ba, tabbas gwamnatin za ta fuskanci fushinsu sai dai bai bayyana taka-maimai matakin da za su dauka ba idan wa’adin kwanaki 21 ya kare ba tare da ci gaba da tattaunawar tasu ba. “Ku fara kirgawa idan nan da kwana 21 ba abinda ya sauya za ku ga matakin da za mu dauka,” A cewar shi.

Ya ce tilas ta hanyar tattaunawar ne za su fahimci gwamnati idan tana da wani korafi a kan lamarin, sai yake ba daidai ne wasu jahohin sun jima da aiwatar da sabon tsarin amma su suna zaman jiran tsammani ba, don haka ne suka ce dole kawai gwamnatin ya zo ta zauna da su domin kammala.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: