Connect with us

TATTAUNAWA

Dambarwar Shari’o’in Zaben Da Ke Gaban Kotun koli, Asalinsu Da Dalilansu

Published

on

Dangane da dambarwar da ake ta yi a gaban kotun koli, musamman a kan abin da ya shafi shari’o’in siyasa da kotun ta yanke, daga baya kuma Jam’iyyun siyasa suke ta ribibin sake komawa gaban kotun domin neman kotun ta sake duba wadannan hukunce-hukncen da ta zartas. LEADERSHIP A YAU LAHADI ta zanta da kwararren Lauya, Aminu Abdurrashid, Lauya mai zaman kanshi, shugaban kamfanin Lauyoyi na Yahaya Mahmud, Arewa Chambers dake Kaduna, domin yi wa masu karatunmu karin haske a kan ma’anar ita kanta kotun kolin da kuma dambarwar da ake ta yi a gabanta. Wakilinmu Umar A Hunkuyi ne ya zanta da shi. A sha karatu lafiya:
Mene ne Ma’anar Kotun koli?
Tsarin mulkin kasar nan ya shirya kotuna daki-daki, kama daga kanana har ya zuwa ga kotun koli. Da farko akwai kotunan da ake cewa kotun majistare, sannan akwai kotunan da ake kira da manyan kotuna, sai kuma kotunan daukaka kara a can karshe kuma shi ne sai kotun koli.
Kila mutane suna yin wannan tambayar ne kasantuwar abubuwan da suka rika faruwa a kwanan nan, inda bayan kotun kolin ta yanke hukunci sai kuma ga Jam’iyyun siyasa suna ta ribibin komawa kotun kolin don neman kotun ta sake duba wasu shari’o’in da ta yanke, to ko daman akwai damar yin hakn ne?
Tun farko akan saurari kararrakin zabe ne a kotunan musamman da ake warewa na wucin gadi, wannan a matakin farko kenan, daganan wanda bai gamsu ba zai daukaka kara, wanda shi kuma a nan an kasa abin ne kashi biyu, akwai shari’o’in da kan kai har ya zuwa ga kotun koli, amma wannan ya shafi shari’un zaben Shugaban kasa ne da kuma na Gwamnoni. A daya bangaren kuma abin da ya shafi shari’un ‘Yan majalisar Dattijai, ‘yan majalisar wakilai na tarayya da ‘yan majalisar wakilai na Jihohi, su kuma shari’unsu suna tukewa ne a kotunan daukaka kara, wanda daganan babu damar wucewa zuwa kotun koli, duk abin da suka yanke shi ne karshe.
To idan aka yanke hukunci a kotun koli, wanda wannan shi ne duk dambarwar da ake yi, to wannan hukuncin kotun shi ne karshe, hukuncin kuma ya zama doka daga cikin dokokin kasa wanda dole ne a bi. To amma kundin tsarin mulki da kuma dokokin da suke tafiyar da su wadannan kotunan sun bayar da wasu kafofi na cewa idan kotun koli ta yi wani hukunci a bisa rashin hurumi, to akwai damar da za a iya sake komawa domin ta duba ta yi gyare-gyare. Sannan kuma abu na biyu aka ce idan ta yi hukunci wanda aka sami tuntuben alkalami wanda ya iya haifar da rudamin da ya sa aka kasa gane ko mai suke nufi a hukuncin su, to za a iya mayar da shi su gyara, wanda wannan kuma ba warware hukunci ne ba. Idan da hurumi kuma ba hurumi wannan yana warware hukunci, domin duk abin da aka yi babu hurumi wannan abin batacce ne.
Hakanan kuma, idan an yaudare su (su alkalan kotun kolin) suka bayar da wani hukunci, to shi ma daga baya in an gano za su iya duba hukuncin domin gyara.
Da wadannan hujojojin ne su Jam’iyyun duka (PDP da APC) suka sake komawa gaban kotun kolin domin ta sake duba wadansu hukunce-hukunce da ta yanke a baya, a bisa dogaro da irin wadannan hujjoji da na lissafo a baya.
Dangane da hukunce-hukuncen da kotun koli ta yanke a kwanan nan, ya abin yake ne?
A hukunce-hukuncen da kotun ta yi, ta ce hujjojin da aka kawo mata ba su da tushe, don haka ne suka yi watsi da su. misali a hukuncin da kotun ta yi a shari’ar Bayelsa, sai kotun ta ce ta ma caji Lauyoyin da suka shigar da karan duk da cewa manyan Lauyoyi ne, amma kotun ta ce ta ci tarar su naira milyan Goma-goma kowannen su da za su bai wa wadanda suka gurfanar a gaban kotun. A na Zamfara kuwa, sai kotun ta dage sauraron domin ta bai wa Lauyoyi daman sauraron hujjojin da za su gabatar. Domin abin da ya faru a ranar da aka kai karan sai ya kasance akwai wadansu da aka shigar a cikin karar wadanda ba a sada su da kwafin karar da aka shigar a kansu ba, wadanda tilas ne a shari’a idan kana karan mutum sai ka sanar da shi domin ya zo ya kare kansa. To da wannan dalilin ne ya sanya aka dage sauraron na Zamfara din domin a ba su daman su zo su gabatar da hujjojin su.
Amma a na Imo da aka gabatar a baya-bayan nan, kotun ta zauna amma ta sake koran karan a bisa shigen irin dalilan da ta bayar a na Bayelsa. Cewa su kotun karshe ne don haka ba za su sake zama su warware hukuncin da suka yi ba tun a karon farko, don haka, rokon da aka je masu da shi ba shi ma da wani tasiri. Sai dai abin da ya bambance shi da na Bayelsa shi ne, daya daga cikin alkalan da suka zauna suka rubuta hukuncin, shi na shi hukuncin ya sha bamban da na sauran alkalan kotun. Domin a shari’a idan ta tafi kotun koli ko kotun daukaka kara, kowane alkali da ke zama a kan shari’ar zai rubuto hukuncin sa ne, amma a karshe in an zauna sai a tattara hukunce-hukuncen sannan a fitar da hukuncin da ya kasance mafi rinjaye.
To a nan abin da ya bambanta shari’ar Imo da ta Bayelsa shi ne kamar yanda na fada shi wannan alkalin ba shi cikin alkalan da suka yanke hukunci a wancan lokacin, daya daga cikin alkalan da suka saurari shari’ar a wancan karon ya yi ritaya, ana ce ma shi Mai Shari’a Amiru Sanusi, shekarun ajiye aikinsa sun kai. Da haka sai aka sami gibi, don haka sai aka cike da shi wannan sabon alkalin wanda daman yana cikin alkalan kotun ta kolin, sai dai ba shi a cikin wadanda suka saurari shari’ar a wancan karon, ana ce masa Mai Shari’a Wizi.
To shi a na shi hukuncin da ya rubuta sai ya ce ya soke wancan hukuncin da kotun ta yi na farko, domin a cewarsa, hujjojin da aka gabatar da su a kan cewa an yaudari kotu shi ya gamsu da su. Don haka, shi sai ya yi hukunci da cewa a mayar wa da Ihedioha, na Jam’iyyar PDP da kujerarsa ta gwamna. Sannan ya ce ya kori Uzodinma na Jam’iyyar APC daga kujerar ta gwamna, to wannan shi ya bambanta shari’ar Jihar Imo daga ta Bayelsa.
Domin a wancan an sami rijaye na alkali biyu, wannan ne kuma ya sanya ake sa alkalan kamar su Biyar ko ma Bakwai, ta yanda za a sami hukuncin da zai yi rinjaye, wanda shi ne zai zama hukunci. A takaice wannan shi ne abubuwan da suke kewaye da dambarwar da ta rika faruwa a gaban kotun. Amma kasantuwar shi kadai ne hukuncinsa ya sha bamban da na sauran alkalan, hukuncinsa ba zai yi tasiri ba, amma dai za a rubuta wannan hukuncin na shi a matsayin wani bangare na hukunci a taskace shi.
Asalin inda matsalar ta Jihar Imo ta samo asali shi ne, akwai tsarin da ake shigar da shari’a, kowace kotu daga cikin kotunan da na ambata a baya, akwai tsari a kan shari’ar da za a shigar a gabansu, wanda kuma shi ne abin da za su duba kenan. Idan aka shigar da shari’a a kotun farko a kan korafin zabe, akan bayar da kwanaki Casa’in saboda a cikin wadannan kwanakin za a gabatar da shaidu da hujjoji, alkalan za su saurara su yanke hukunci. Wanda bai gamsu ba, idan ya tafi kotu ta gaba da zai daukaka kara ya rasa wata damar da zai kara gabatar da wata shaida ko wata sabuwar hujja ta shigar da wata sabuwar shaidar. Abin da ita kotun daukaka karan za ta duba shi ne hukuncin da ita kotun da ta saurari karar ta zartas ya bi tsarin shari’a an yi adalci ko ba a yi ba? abin da kawai za ta duba kenan, ba ruwanta da komawa ta bayar da dama a sake jin shaidu.
Shi ya sanya abin da ake kaiwa a gaban ita wannan kotun abubuwa guda biyu ne kawai, su ne kuwa rahoton duk abin da ya faru a gaban kotun ta kasa, sai kuma hukuncin da kotun ta zartas, sai kuma Lauyoyi su yi dan takaitaccen bayanansu a kan abin da ya sanya suke ganin waccan kotun ba ta yi adalci ba a hukuncin da ta yanke. Shi kuma wanda yake kare karar zai bayar da na shi dalilan da suke tabbatar da hukuncin da waccan kotun ta yanke, amma dukkansu babu dama a sake sauraron wasu shaidu daga garesu.
A nan ma idan ba a gamsu ba aka kai gaba zuwa kotun koli, abin da kotun kolin za ta duba kawai shi ne, wadannan abubuwa guda biyu, an yi adalci an bi tsarin shari’a ko ba a bi ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: