Connect with us

ADABI

Karimci Da kimar Shata Sun Sa Ya Wuce Darajar dan’uwa A Gidan Mu -Zannan Katsina

Published

on

(Ci-gaba daga satin da ya gabata)
Sunan Zannan Katsina, Alhaji Lawal Musa Bindawa, suna ne da ya kada karaurawa a Lardin Katsina, da sauran sassan jihohin Arewa. Zanna, babban ma’aikaci ne kuma dan siyasa, sannan kuma mai rike da sarauta. A kwanakin baya, Zannan na Katsina ya tattauna da Dokta Aliyu Ibrahim kankara, fitaccen marubuci, kuma mawallafin littafin tarihin rayuwar marigayi Dokta Mamman Shata Katsina. Ya bayyana masa irin kaurin alakar mahaifin sa da Dodon mawakan. Ya kuma yi masa korafin yanda tun bayan rasuwar mahaifin nasa cikin Disambar 1978 babu wani daga cikin dangin su da ya dauki dawainiyar hidimar gidan su sai Shata. Ga dai yanda hirar ta su ta kasance:
Musa Bindawa na da alaka da Sani Audi kwastan?
Babu alaka ta jini, amma ajin su daya a makaranta. Sun halarci makarantar Midil ta Dutsin-Ma. Musa Bindawa ne shugaban dalibai a lokacin. Ajin su daya da su Ambasada Zakari Ibrahim da Mohammed Dikko (Mallamawa na yanzu) Don haka sun tashi a matsayin abokai, su duka da na lissafa. Duk abin da ake ciki, kowa na neman kowa a duk inda su ke. Don hakane da baban mu ya rasu, da kungiyar abokan su suka zo gaisuwa, sai Mohammed Dikko batagarawa, a lokacin yana shugaban kwalejin gwamnatiu ta Kaduna ya ce ina Lawal? Na ce ga ni. Ya nemi ya dauke ni ya kai ni wajen sa in yi karatun sakandare. Sai aka amince. Sai ya tafi da ni Kaduna. Wannan ne salar zuwa ne can na yi sakandare. Amma, duk lokacin da Shata ya je Kaduna sai ya neme ni ya ba ni alheri, har na gama makaranta. Sannan na wuce jami’ar Bayero ta Kano na yi karatun digiri. Can ma, a duk lokacin da Shata ya je Kano sai ya aika an kira ni ya yi ma ni alheri, saboda irin zaman amana da suka yi da mahaifi na.
Ka ga, wancan alkawari da mahaifi na ya yi ma ni, na cewa za ya kai ni Ingila karatu, to Allah Bai yi ba. Ingilar ba ta samu ba, saboda mutuwa ta raba, amma Allahn da Ya haddasa hakan, Ya aiko ma ni da Shata Ya tallafa ma ni.
Lokacin da Sani Audi ya auri Hajiya Nunu, diyar Sarkin fada Damale, Shata ya zo gidan Sani Audi ya yi wasa da dare.
Wace shekara ke nan?
Cikin 1976 ne.
Yaya za ka iya kwatanta dangantakar Shata da Malam Musa Bindawa?
kankara, lokacin da na dan taba zama gidan Shata, ka san cewa ba a tayar da shi barci? Amma ni ina shiga dakin sa in tayar da shi. Za ya kuma tashi. Ya tambaye ni ‘dan baba, Mamman mi aka yi ne?
Sannan kuma, Magaji, babban dan sa, wanda ake kira Lawal, ai a gidan mu ya dan taba zama. Mahaifiya ta ta rike shi. Lokacin da mahaifina ke da rai har kauyen su Shibdawa Shata ke zuwa yana gaishe da mahaifin sa. Watau, wata irin kauna ce da amana ke a tsakanin su, da sai Allah Ya san tsakanin su. Musa Bindawa yana kallon Shata ba a matsayin maroki ba, yana kallon sa a matsayin wani mutum da Allah Ya halitta daban, ta fuskar karimcin sa, da dattakun sa, da alherin sa, da jan hali, da dai sauran su. Wannan ya sanya suka rika girmama juna.
Ni kaina, ina gaisawa da wasu daga cikin ‘ya’yan Shatan a kai a kai. Na kan ce ma su Umma, ku, mahaifin ku ba maroki ba ne.
Sannan kuma, wani abu da ba ka sani ba kankara, bayan da mahaifin mu ya rasu, a duk ranar juma’a sai Shata ya tafi Bakori wajen Hajiya Balaraba, mahaifiyar sa ya kai mata kudi da za ta yi cefane. Sannan ya saya mata hatsin da za ta ci. Idan tana da bukatar sutura duk za ya dunka mata. Shata ya dauki dawainiyar gidan mu, tun daga abinci zuwa kudin kashewa.
Ka na nufin ban da kakar ku har da mahaifiyar ku ya ke taimako ?
kwarai kuwa kankara, a fadi ma kowa wannan maganar. Ba fada ma ni aka yi ba, a gaba na an sha yin haka. Shata shi ya rufa mana asiri ya yi mana hidima. Bayan rasuwar mahaifin mu babu wani daga cikin dangin mu da ya yi mana dawainiya kamar shi Shatan. Idan kuma akwai shi to ya zo ya ce ma ni ga shi.
Na fada ma ka, shin ai Daura ce karshen son Shata ko?
Haka ka fada.
To ko Daura ba ta kai ‘yan gidan mu son Shata ba, sabili da abin da ya yi mana. Duk cikin dangin mu ba wanda ya yi mana shi. Shata mutum ne, Shata karimi ne. Dalili? Duk zuriyar su Musa Bindawa, ba wanda ya rike gidan mu kamar Shata.
A ina da ina ya yi masa wakoki?
Akwai wani lambu na Alhaji Ali Usman a hanyar Daura, to a cikin 1975 can suka yi jerangiyar zuwa tare da Shatan. A nan suka sanya shi ya yi wakokin duka.
An ce daga cikin wakokin har da Bakandamiya, hakane?
E, haka ne. Na taba jin ta. Ya na cewa : Tare da Musa Bindawa na Shata uban waka baban Mammam/ Musa Badange na ainihi dan Dangi, jikan Dangi aminin Mamman/Gaya ma Musa Bindawa, tafi tsare N. A. da gwamnati, ka bar ni da ganga ta in waka/
Mu je zuwa, mu ji haduwar ku ta karshe da kai da shi.
Lokacin da Shata ya rasu cikin 1999 ina Amerika. Amma kafin rasuwar sa, na hadu da shi a Kazaure. Dalilin an baiwa danburan na Kazaure Suleiman Adamu mukamin ministan albarkatun ruwa. To a wurin bukin sa ne Shata yana wasa, ni kuma na je. Daga nesa Shatan ya hango ni. Sai ya sanya aka kira ni, na je na gaishe shi. Ya ba ni kudi ya ce in yi masa liko. Na ce masa ‘wallahi ba ni iyawa’. To a lokacin yana cikin yin wakar Haji Mamman danburan Bello, kuma. Sai yana fadi a waka: ‘ga Mamman, nai mai alheri, albarkar danburan Bello’.
Sai kuma lokacin da ya yi wata kwanciya a asibiti a Kano kafin ya rasu. Akwai wata kanwata, matar Abdulkarim Kaita. Ana kiranta Hajjajo. Ita ta je Kano buki, to a can sai ta samu labarin Shata na kwance a asibiti. Sai ta je gano shi. To sai ya ce mata ta shaida ma duk ‘ya’yan Musa Bindawa, cewa yana son ganin mu. A lokacin mun tafi ziyara kasar Sweden domin halartar taron dumamar Yanayi. Ta dawo gida Katsina, sai ta buga ma ni waya. Ganin da bai yi mana ba ken an. Allah Bai yi ba, ya rasu bayan ‘yan watanni.
Fada ma mai karatu rana da watan da Alhaji ya rasu.
Ya rasu ran 9/12/1978.
To Allah Ya gafarta masa.
Zanna: Amin amin, na gode kankara.
Mu kwana nan.
(An tsakuro wannan hira daga cikin kundin tarihin Shata na littafin Shata: Mahadi Mai Dogon Zamani)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: