Connect with us

LABARAI

Har Yanzu Mutum Guda Ke Da Cutar Coronavirus a Nijeriya- NCDC

Published

on

An tabbatar da cewa cikin Mutum 23 Da Nijeriya ta yiwa gwajin cutar coronavirus har yanzu mutum guda ne ke dauke da cutar.

Cibiyar dake dakile cututtuka a Nijeriya, wato NCDC ta bayyana cewa: cikin mutum 23 da aka zarga suna da cutar kuma aka yi musu gaji a ihohin hudu na Nijeriya da suka hada da Edo, Ogun, Legas, Abuja da Kano, mutum guda aka samu yana duke da cutar kuma shima har yanzu yana nan bai mutu ba.

Babban Daraktan Cibiyar, Dr. Chikwe Ihekweazu, shi ne ya bayyanawa Kamfanin dillancin labarai hakan a Abuja a ranar Lahadi.

Inda ya jaddada cewa: har zuwa 7 ga watan Maris ba wanda aka gano yana da cutar COVID-19 a kasarnan. Sannan ya ce cikin hanyoyi 219 da suka bayar domin bada rahoto kan ko an samu masu cutar, ba a samu rahoto ko guda dake nuna cewa akwai sabbin jama’ar da suka kamu da cutar ba a Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: