Connect with us

ADABI

Sarki Sanusi Ya Albarkaci Taron kaddamar Da Litattafan Mariya Durumin Iya

Published

on

Taron kaddamar da littattafan Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya guda uku da a ka yi a birnin Kano ya yi armashi karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, CON, wanda shi ne ya albarkaci taron da kansa, ba sako ba.

Litattafan da a ka kaddamar sun hada da Rayuwar Mace Daga Haihuwa Zuwa Tsufa, Soyayya Da Rayuwar Aure A kasar Hausa da Almajiranci Da Bara.
Uban Taro Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kira ya yi ga matasa maza da mata masu sha’awar rubutu da su yi koyi da Hajiya Mariya wajen zama jigo na rubutu a kan al’amura da suke ci wa al’umma tuwo a kwarya. Hakan ta sa ya yaba wa Hajiya Mariya duk da karancin shekarunta, amma ta yi nazari mai zurfi a batutuwa da su ka sha kawunan jama’a.
Mai Martaba Sarki ya yi sharhi mai tsawo dangane da rayuwar mata da sha’anin aure a kasar Hausa, a wannan zamani, inda ya yi kira ga mazaje da su ji tsoron Allah da rike hakkokin mata wajen tarbiyyarsu da kuma zamantakewarsu ta aure. Dangane da sha’anin Bara, Mai Marataba Sarki kira ya yi ga gwamnatoci da su tashi tsaye wajen yaki da wannan mugunyar al’ada ta sanya dokoki kuma da tabbatar da an bi su.
A nasa jawabin, Mai Sharhin Littattafai, Malami daga Jami’ar Bayero da ke Kano, Sashin Nazarin Harsunan Nijeriya, Farfesa Isa Mukhtar, yaba wa marubuciyar littattafan Hajiya Mariya Inuwa ya yi saboda hikima da zalaka da sanin al’ummar da take cikinta. Ya yi nuni da cewa, littattafan za su fadakar kuma su zaburar da mutane musamman ma mata musulmi dangane da abin da ya shafi rayuwa a kasar Hausa. Farfesa Isa Mukhtar ya ce marubuciyar ta yi namijin kokari wajen fito da manyan al’amura da suka shafi rayuwa musamman ma rayuwa irin ta almajirci da kuma rayuwa irin ta zaman aure a gidan miji da rayuwa irin wadda ake so a ga mace mai tarbiyya a kasar Hausa da al’adu irin na musulunci da kyawawan al’adu na Hausawa.
Farfesa Isah Mukhtar ya yi kira ga marubuta irin su Hajiya Mariya da su rika kula da ka’idojin rubutu ta yadda adadin tartibin shafuka za su dinga dacewa da shafukan cikin matakin littafin. Bayan haka kuma akwai bukatar a rika sanya madogara a daidai gurin da a ka ambata kuma a rika kawo kammalawa da manazarta a karshen kowane babi wadannan abubuwa su ne za su bambanta littattafai na kagaggun labarai da littattafan da a ka rubuta na gyaran tarbiyya.
Tuntube dadin gushi, an tara kimanin naira miliyan biyu nan take, inda mai kaddamar da littafin almajiranci da bara, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, tsohon shugaban hukumar tatttara rarar man fetur, domin tallafawa ilimi, ya kaddamar a kan kudi naira dubu dari biyar, wato rabin miliyan, shi kuma mai kaddamar da littafi na biyu, Rayuwar Mace Daga Haihuwa Zuwa Tsufa, Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada, dan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai Wakiltar karamar Hukumar Birnin Kano ya kaddamar da nasa littafin a kan naira dubu dari uku. Dubu dari nasa na kashin kansa, naira dubu dari daya kuma a madadin Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Nijeriya Femi Gbajamiamila.
Mai kaddamar da littafin Soyayya Da Rayuwar Aure a kasar Hausa, Dakta Malam Ibrahim Shekarau CON, Sardaunan Kano, Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, ya kaddamar da nasa littafin a kan kudi naira dubu dari, inda kuma ya yi kira ga gwamnati da kuma mutane masu hannu da shuni da su sa yi littattafai irin na Hajiya Mariya Inuwa su raba su a makarantu da kuma dakunan karatu, wato laburare domin amfanin al’umma baki daya. Babban Mai Kula da Asusun Gwamnatin Nijeriya AlhajI Ahmad Idris, ya sayi littattafan a kan kudi Naira 2,000, ta hannun wanda ya wakilce shi a wajen taron.
Shugaban Kwalejin Ilmi ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Dr. Aliyu Idris Funtuwa ya sayi littattafan a kan kudi naira dubu dari sai dan’amu Foundation sun sayi littattafan a kan kudi naira dubu hamsin, Ali Muhaamd Imam sun sayi littattafan a kan kudi naira dubu hamsin, Ado Bayero Foundation sun sayi littattafan a kan kudi Naira 50,000, Umar Ibrahim El Yakub sun sayi littattafan a kan kudi Naira 50,000, Kabiru Muhammad Assada da jama’arsa sun sayi littattafan a kan kudi naira dubu hamsin.
Mutane sama da 500 ne su ka halarci taron kaddamar da litattafan daga ciki da wajen jihar Kano.
Takaitaccen tarihin marubuciyar littattafan, Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, ya yi nuni da cewa an haife ta a unguwar Durumin Iya a cikin birnin Kano a shekarar dubu daya da dari tara da tamanin (wato, 1980), ta kuma kammala karatun firamare a makarantar mata ta Gidan Galadima, sannan ta yi Makarantar Sakandare ta Turasul Islam, tana da shaidar karatun diploma a fannin Shari’a daga Kwalejin Aminu Kano, (wato Legal). Kuma ta samu shaidar karatun digiri na farko daga Jami’ar Yusuf Maitama Sule a fannin koyarwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: