Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Matar Makwabci’

Published

on

Suna: Matar Makwabci

Tsara Labari: Bashir Y. dan Rimi
Kamfani: Sai Na Dawo Film Production
Shiryawa: Yahuza Sai Na Dawo
Umarni: Kamal S. Alkali
Jarumai: Ali Nuhu, Shu’aibu Lawan, Jamila Umar, Fati Washa, Al’amin Buhari, Hajara Usman, Abdul Abbas, A. S Muhammad da sauransu.
Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Habib (Ali Nuhu) ya dawo cikin dare daga wajen aiki yayin da matarsa Maryam (Jamila Nagudu) take yi masa korafin bai dawo da wuri kamar yadda ya saba ba, yayin da daga bisani ya tambayi kayan sa marasa nauyi da ya sanya ta wanke ma sa, amma ta nuna bata wanke ba. Haka Habib ya debi kayan a cikin daren ya fita harabar gidan ya wanke gami da shanyawa a saman katanga.
Sai dai kuma washe gari da safe bayan ya fito dibar kayan sai ya tarar iska tayi masa jifa da wasu daga cikin fararen rigunan nasa, hakan ne yasa ya fita waje ya zagaya cikin wani kango dake jikin gidan sa don tsonto kayan sa da suka fada wajen. Sai dai kuma cikin rashin tsammani sai yaci karo da gawar dan makociyar sa a kwance cikin jini a wajen. Ganin hakan ne ya tsorata shi kuma yayi gaggawar kiran jami’an tsaro ya sanar da su.
Kafin dan wani lokaci jami’an tsaro su ka je su ka duba gawar yaron da a ka kashe gami da tafiya wajensu da shi, yayin da daga bisani su ka nemi sanin iyayen yaron tare kuma da soma binciken su akan Habib wanda ya kira su ya sanar musu da labarin gawar yaron. Ganin yadda jami’an tsaro suka matsawa Habib da son sanin wani abu game dashi ne yasanya shi kosawa gami da tunanin ko sun fara zargin sa akan mutuwar dan makociyar sa ne, haka itama matar sa Maryam abin ya soma bata mamaki musamman da taji Habib ya amsa cewar Sadiya wato mahaifiyar yaron da aka kashe ‘yar uwar sa ce, duk da kuma ita tasan cewa bashi da wata alaka ta jini da Sadiya.
Hakan ne yasa itama matar sa Maryam suka soma samun sabani dashi mijin nata, musamman da Inspector (Al’amin Buhari) yazo gidan Habib don neman izinin sa akan gwajin kwayoyin halittar yaron da aka kashe da kuma na Habib din. Hakan ya sake haifar da rikici a tsakanin su duk da Habib bai amince a gwada shi ba. Cikin lokaci kadan labarin zargin da ake wa Habib ya soma yaduwa har a gidajen rediyo, kuma hakan ne ya tashi hankalin mahaifiyar sa (Hajara Usman) wadda daga karshe suma suka yanke shawarar daukar wani dan uwan su lauya don kare Habib daga halin da ake neman saka shi.
Sai dai kuma bayan Habib ya amince a gwada jinin sa sai likitoci suka gano cewar shine mahaifin Amir yaron da aka kashe, nan suka tsananta bincike har aka gano cewar yayi amfani da matar makwabcin sa Sadiya (Fati Washa) wadda mijinta Abbas (Shu’aibu Lawan) ya kasance soja kuma mai azabtar da ita gami da kin bata hakin ta na aure, dalilin hakan yasa Habib ya biye mata a sakamakon shima tashi matar Maryam ta kaurace masa har zuwa sanda shaidan ya rinjaye sa wajen haikewa matar makwabcin sa.
Bayan an gane hakan ne sai aka zurfafa bincike akan Abbas soja mijin Sadiya wanda ya jima sa gane cewar Amir ba dan sa bane amma yake zaune da ita. Daga bisani ne aka gane cewar babu sa hannun Abbas a mutuwar Amir. Maryam matar Habib ce tasa aka kashe yaron saboda ta gane cewar dan mijin ta ne da aka same sa ta haramtacciyar hanya.

Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa sakon da ake son isarwa, kuma an yi nasarar rike me kallo har zuwa kan darasin da ake son nuna masa.
2- Daraktan fim din yayi kokari don ganin labarin fim din ya tafi yadda ya dace, kuma yayi kokari wajen ganin jarumar sun isar da sakon da ake bukata, domin jaruman sun yi kokari sosai.
3- Hoto ya fita radau kuma an yi amfani da salon daukar hoton da ya gamsar.
4- An yi kokarin samar da wuraren da suka dace da labarin wato (locations)

Kurakurai:
1- Tun daga farkon fim din har zuwa karshe babban rubutun ‘Prebiew Copy’ ya bayyana baro-baro, wanda ya dace tun kafin fim din ya fita kasuwa ya zamto an cire shi amma sai aka bar sa har zuwa lokacin da fim din ya isa ga masu kallo, shin ba’a yi yunkurin cire sa bane kafin a watsa fim din a kasuwa ko kuma mancewa akayi dashi?
2- Me kallo yaga Inspector (Al’amin Buhari) ya shiga gidan Habib shi kadai tare da bukatar suna son gwada kwan halittar sa, sai dai kuma bai je da wani likita wanda zai yi gwajin ba, kuma bai nuna cewar za suje asibiti ko kuma tare sukazo da likitan ba, ya dace ace sun je tare da likitan don tabbatar da zahirin abinda Inspector din ya fada.
3- Lokacin da aka fara nuna Habib yaje wajen mahaifiyar sa (Hajara Usman) don sanar mata da matsalar da yake ciki a bisa tuhumar sa da laifin kisan kai, sa’ilin da take magana a wajen, muryarta bata daidaitu ba, domin sauti yana karuwa ne gami da raguwa.
4- Lokacin da dan jarida (Abbas Sadik) ya biyo Habib gida akan mashin don tambayar sa dalilin da yasa jami’an tsaro suka gayyace sa zuwa ofishin su, me kallon yaji dan jaridar a karon farko ya kira sunan Habib (Ali Nuhu) da suna malam KABIR, a madadin Habib. Kafin daga bisani kuma da ya cigaba da kiran sa da Habib, shin dan jaridar bai san ainahin sunan Habib bane? Duk da kuma, a nunowa ta gaba an ga dan jaridar yana bayanin cewa sunan sa Kabir wanda hakan na nufin sunan shi ya manta har ya danbarawa Habib.
5- Lokacin da jami’an tsaro suka gane cewar Maryam (Jamila Nagudu) ce ta kashe yaron da Habib ya haifa ta kazamar hanya, me kallo yaji Maryam ta bada hujjar cewa ta kashe Amir ne saboda jin cewar dan da mijinta Habib ya haifa ne ta haramtacciyar hanya, alhalin kuma duk ba’a gane cewar yaron dan Habib bane har sai bayan an kashe shi sa’in da aka soma bincike. Ya dace a samar da wata gamsasshiyar hujjar da Maryam zata fada akan batun kashe yaron amma ba wannan ba.
8- An nuna cewar jami’an tsaron sun rike gawar Amir basu bayar an yi masa suttura an binnesa ba saboda suna bincike akan gawar, sai dai kuma lokacin da aka kawo karshen matsalar ba’a ji an yi maganar gawar yaron da take hannun jami’an tsaron ba, ya dace ko Sadiya mahaifiyar yaron ta bukaci a basu gawar dan ta idan ma shi Inspector bai furta cewar su tsaya don tafiya da gawar yaron su ba.

karkarewa:
Fim din ya fadakar domin an nuna illar cin amana gami da laifin wasu matayen masu kauracewa mazajensu yayin da a karshe kuma sanadin hakan ya haifar da matsala wadda suma matan zata share su. Sai dai kuma akwai wasu abubuwan wanda ya dace a kara inganta su a gaba. Wallahu a’alamu!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: