Connect with us

TATTAUNAWA

Bara: Dacin Gaskiya Ya Fi Na Madaci, Zakinta Ya Fi Zuma – Usmaniyya

Published

on

A yanzun haka gwamnatoci musamman a arewacin kasar nan suna ta ribibin kafa dokar hana bara ta almajirai da sauran mabarata nakasassu, wanda hakan ke haifar da zazzafar mahawara daga sassa daban-daban. A kan hakan, LEADERSHIP A YAU, ta zanta da, shahararren dan kasuwar nan na man Fetur, kuma Malamin Addinin Musulunci, Abubakar Usman Sharif Usmaniyya, inda ya yi mana karin bayani a kan sarkakiyar da ke tattare da wannan batun. Wakilinmu Umar A Hunkuyi ne ya zanta da shi, a sha karatu Lafiya:

 

Ya zuwa yanzun, Jihar Kano da Jihar Nasarawa sun kafa dokar hana yin bara, bara ta nakasassu da bara ta almajiran allo, rahotanni suna nuna cewa yawancin Jihohin arewa duk suna da nufin kafa irin wannan dokar, to ko me Malam yake gani a kan hakan?

Abubuwa irin wannan a kasa irin Nijeriya suna da wahala, domin in ba mu manta ba a lokacin Gwamnan Jihar ta Kano, AVM Hamza Abdullahi, ya yi kokarin kafa irin wannan dokar, amma abin ya gagara. Ba wai ya gagara hakanan kawai ba, domin an tura Sojoji da ‘yansanda sun kama duk masu baran da suka gani musamman a wajen kwaryar birnin na Kano, amma bayan an kama su din an kai su wajen da aka tanada domin ajiye su sai ya kasance wadanda suka kama su din ba su da abincin da za su ba su. Ba a yi masu tanadin ababen bukata na lalurorinsu ba. A karshe bayan an tara su din, su kansu masu tsaron na su suke cewa ku fito ku je ku nemi abin da za ku ciyar da kanku, domin ba a kai masu abincin ba, in kuwa za a tsare mutum ko da mai laifi ne tilas ne a tanada masa ababen bukatunsa na yau da kullum, kama daga abinci, wurin kwana, bahaya da sauran bukatunsa. Amma sai ya kasance a wancan karon duk ba a yi hakan ba, wanda ya sanya a karshe dole aka sake su maganar an hana bara a Kano ta sha ruwa.

Shi ma Gwamnan Legos, ina zaton zamanin Tinubu ne, a wata shekara ya kafa irin wannan dokar, inda aka kamo almajirai da mabarata dubbai aka sako su a cikin Jirgin kasa wasu a cikin mota aka zarto da su Kano, gidan Sarki, zamanin Ado Bayero, inda ya yi masu marhabin ya karbe su yana mai cewa mun san ba dukkansu ne mutanan Kano ba, amma dai ‘yan’uwanmu ne, domin duk mutumin da ya fito daga arewacin kasar nan dan’uwanmu ne in ji Ado Bayero. Sai bayan ‘yan kwanaki aka bi ana tantancewa aka kuma kai kowa garinsu, duk Sarki Ado Bayero din ne ya dauki nauyin wannan. Amma a bayan lokaci kadan sai ya kasance ko’ina ka zaga a Legos din za ka taras da mabaratan, sai ya kasance abin ba ta sake zani ba.

To misali in yanzun Kaduna, Nasarawa ko ma duk wata Jaha ta ce ta kafa dokar hana bara, me ta tanadar wa mabaratan da za a kama? Wannan shi ne abubuwan da jama’a suke dubawa.

 

A takaice dai za mu iya cewa shirin hana baran ya dace, amma ya zamana an yi masu tanadi na musamman ta yanda harkokin rayuwarsu nay au da kullum za su gudana kamar kowa kenan?

Madalla! Hakane, masu iya magana suna cewa, “in an bi ta barawo a bi ta mabi sawu,” dalilin fadin hakan kuwa shi ne, yawancin almajiran nan fa masu yin barar Malamansu suke yi wa hidima kawai, domin ba na mantawa, a kasa da kwanki goma na karanta a cikin wata Jarida inda Malami ya kama hannun almajirinsa ya daure har sai da hannuwan yaron nan suka rube, wai sabili da bai kawo ma shi naira Arba’in ba. To ina imani, ina tausayi a nan, wane Addini ne ya ce a aikata makamancin hakan?

Ba kuma wani abu ne ya sanya mutane suke daukan ‘ya’yayensu suna kaiwa irin wadannan malaman ba mu a nan arewa face saboda talauci ne, mu yi hakuri fa, domin ita gaskiya daci gareta, wanda dacinta ya fi madaci daci, zakinta kuma ya fi zuma zaki.

 

Gafarta Malam barar nan ta shafi kamar kaso biyu ne, akwai bara ta mabarata wacce wannan ya shafi kamar mutanan da suke da wata nakasa ce a jikinsu, akwai kuma bara ta almajiran allo, wanda yawanci su ne yaran da muke gani suna zuwa domin karatun allo na Alkur’ani Mai Girma, to kamar a dokar da gwamnatin Jihar Kano ta kafa, su na farkon masu nakasa an hana ne an kuma kore su, su kuma kaso na biyun almajiran allo, an umurci iyayensu ne da su zo su tafi da ‘ya’yan nan nasu, to ya Malam yake gani da hakan?

Wannan tsarin da dama-dama, amma in gwamnati ta kama yaro an mayar da shi garinsu ko an kira mahaifinsa ya zo ya tafi da shi, akwai mai sanya ido ne domin ya tabbatar daga can ba wani wajen ne ya nufa ba kuma? Domin babban abin da ake gudu a nan shi ne daga karshe ma a zo a canza wannan barar a mayar da ita ta zama kamar Addini, wanda kuma duk wanda daga baya ma ya so ya soki hakan sai a canza ana ma shi ma kallon kamar shi ba Musulmi ne ba, domin ka nuna kishinka da tausayinka a bisa azabtarwar da ake yi wa irin wadannan yaran.

 

Kila shi ya sanya a wannan karon a halin yanzun dai Jihohin Kano da Nasarawa sun fara, amma kamar yanda rahotanni suke nunawa ilahirin Jihohin arewa ko ma Jihohin kasar nan za su kafa irin wannan dokar ta yanda in an kama yaronka an dawo maka da shi babu kuma inda za ka dauke shi ka kai shi. Ko Malam yana ganin hakan zai bayar da fa’ida kuwa?

Doka fa irin tamu wannan in an shigo da ita jama’a suna yabawa, sai dai ba ta dorewa ne. Kamar yanda wadancan Jihohi misali Legos da Kano suka fara a wancan lokacin, wasu ma a lokacin mulkin Soja ne, amma daga bisani abin ya zo ya wargaje, tilas abin ya zamana abin nazari ne sosai a kai.

 

Amma idan har a wannan lokacin gwamnatocin da gaske suke yi, abin zai dore na a kama wadannan yara a mayar da su gaban iyayensu, Malam yana ganin hakan daidai ne?

Madalla! Kamar kai a yanzun da ka fito daga garinku, Malam Ibrahim ma ya fito daga garinsu, ni ma na fito daga garinmu, ai duk mun yi karatun na Islamiyya daidai gwargwado, amma ai ba mu je tsangaya ba. To don me sai ka dauki yaronka ka bai wa wani Malami ya tafi da shi wani gari da sunan tsangaya? Shi ya sanya na ce maka gaskiya tana da dadi, amma dacinta ya fi yawa. Da yawan wasu abubuwan barna da ake aikatawa ta hanyar hakan ne yaran nan suke shiga cikin su. Ka tura yaro ya je yana zuwa gidan ‘yan Daudu yana bara, daga wanke mana kwanonin nan in ba a yi sa’a ba sai su janye shi ka ga shi ma ya koma daudun. Ta nan ne kuma yana zuwa bara a tashar mota, barayin da suke a tashar motan in ba hankali ba, sai ka ga sun janye shi ya zama daya daga cikinsu. To a nan me aka yi? Ka ga garin gyaran gira, an cire idanu kenan baki-daya.

To ko a bangaren mabarata masu nakasa akwai wata shawara da Malam zai bayar na abin da ya kamata a yi masu?

To a kan maganar yaran nan dai kamata ya yi a kafa doka, duk wanda ya dauki yaronsa ya bayar yana bara idan aka kama shi, to ba dan za a hukunta ba uban ne za a hukunta. Wannan shi ne na farko game da iyaye da suke aikewa da yaransu wasu garuruwa da sunan karatu.

Na biyu, nakasassun nan duk Duniya ai ba inda babu su, na je Ingila na je Indiya na je kasashen Duniya masu yawa ko’ina akwai talakawa, amma su suna da tsari, za ka ga idan an ce ga mahaukaci nan, za a je a shawo kanshi da mota a kama shi a tafi da shi gidan da aka tanada musamman na mahaukata, inda kuma ake kula da su yanda ya kamata. Amma mu a nan fa, babu wannan tanadin, da kanka za ka kama, da kanka kuma za ka sake shi domin babu tanadin kulawa da su.

 

Kenan gwamnati ya kamata ta yi shiri na musamman na wajen kulawa da su yanda ya kamata watakila ma har da koya masu sana’o’i?

Lallai a yi mu su tanadi har da koya masu sana’a, sannan kuma bayan an koya masu sana’ar ma a sama masu jarin ci gaba da sana’ar na su ta yanda za su zama masu dogaro da kansu kowa ya huta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: