Connect with us

RA'AYINMU

Batun Hana Bara Kan Titina Da Gwamnatin Kano Ta Yi

Published

on

Yawan karuwar al’umma da a ke samu a Nijeriya ya sa a na ta samun karuwar mabarata a kan titina da kasuwanni da tashar mota da wurare daban-daban.

Wannan ne ya sa gwamnatin Jihar Kano ta yanke shawarar hana mutane barace-barace a cikin jihar. A kwanan nan ne Gwamna Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya saka dokar haka barace-barace a cikin jihar, inda ya yi gargadin cewa, duk yarai da a ka kama yana fara, to za a hukunta shi. Gwamnan ya sadar da hana barar ne a wajen kaddamar da aikin hukumar kula da ilimin bai daya da kuma rarraba takardun shaidar aiki na mukamai guda 7,500 wanda ya bayar na malamai sa-kai. Ya bayyana cewa, hana bara zai sa jihar ta samu bunkasa ilimi kyauta da kuma ilasta ilimin a cikin jihar. Gwamnan ya ayyanar da tsarin ilimi kyauta da tilastawa ilimin da kuma maida makarantan allo zuwa makarantun zamani wanda za a dunga karantar da darasin Ingilishi da lassafi a makarantun allo.

Ganduje ya kara da cewa, lokacin da Almajirai suke karatun alkur’ani, to za su dunga koyan darashin Ingilishi da kuma darasin Lissafi wanda zai sa su ci gaba da koyan karatu kamar yadda ake yi a makarantun sakandare ko kuma fiye da haka.

Mafi yawancin sassan Nijeriya, barace-barace a kan hanya ya zarce jinsi ko kabila ko kuma shekaru, lamarin bai tsaya kan yara kanaka ba kawai har ma da manya a cikin wannan mummunan kasuwanci. Muna fatan za a zantar da irin wannan lamarin ga dukkan karuruwa da kuma biranen da ke fadin kasar nan.

Ana danganta wannan lamari da talauci, amma akwai abubuwa masu yawa a cikin lamarin. Bayan matsaloli da ke damun muhalli, akwai rashin kyakykyawan lafiya da aikata muyagun laifuka da kuma barace-barace a kan hanya dukkan su suna daga cikin abubuwan da ke damun al’umma. Ana dauka wannan mummunan kasuwanci shi ke sa yara su sami ilimi tun suna kanana, amma shi ke sa yara su tashi suna aikata muyagun laifuka a cikin al’umma.

A wannan jaridar, muna yaba wa Gwamna Ganduje a kan wannan namijin kokari da ya yi. Mun tabbata da cewa, wannan zai rage yawan yaran da ba su da ilimi a yankin Arewa, mun tabbatar da cewa, wannan mugun dabi’a da ake danganta shi da addini zai ragu.

A wani rahoto na shekarar 2019, wanda hukumar kula da yara na majalisar dinkin duniya ta fitar ya bayyana cewa, akwai jihohi guda 10 cikin har da babban birnin tarayya wanda yara sama da miliyan takwas ba sa zuwa makaranta. Jihohin dai sun hada da Bauchi, Neja, Katsina, Kano, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Gombe, Adamawa da kuma Taraba.

Wannan alkaluma ya nuna akwai karacin ilimi a cikin al’umma, wannan jaridar tana kira da gwamnoni su samar da tsirin ilimi kyauta a cikin jihohinsu, wanda ya zo dai-dai da dokar hukumar bayar da ilimi bai daya ta shekarar 2004. Dokar hukumar ta bayyana cewa, a samar da ilimi kyauta ga dukkan yaran da ke makarantar firamare da na karamar sakandare a fadin kasar nan. Haka kuma, ta tanadi hukunci ga duk iyayen da ba su saka yaransu makaranta ba.

Idan za mu iya tunawa, a cikin ‘yan kwanakin nan ne shuwagabannin gargajiya kamar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da Ooni of Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, suka bayar da shawara da aka kama iyayen duk wani Almajiri, domin ba yaransu ba ne kuma suna jawowa al’umma fitutunu. Sun kara da cewa, idan iyayen suna daukan bara a matsakin kayan ado, ya kamata su yi barar ne da kansu ba, ba su tura ‘ya’yansu bara ba. Muna da tabbacin cewa, za a magance matsalolin Almajirai a cikin ‘yan kwanaki kadan. Akwai kwakwkwarar dalili da ke nuna yadda masu tayar da kayar baya da ‘yan bindiga suke saka Almajirai cikin muyagun laifuka. A Magana ta gaskiya, wadannan yara da ke yin bara sun bai wa ‘yan bindiga gudummuwa mai yawa wajen gudanar da harkokin ta’addancinsu, yana da kyau mu goyi bayan hana wannan lamari.

Haka kuma idan za mu iya tunawa, mai bai wa shugaban kasa shawara ta harkar tsaro, Babagana Monguno, ya bayyana cewa, gwamnati tarayya ba za ta iya mayar da tsarin makarantun allo zawa na zamani a Nijeriya. A cikin watan Yunin shekarar da ta gabata, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya duba tsarin domin ta tabbatar ba bu wani yaro da bai zuwa makarantar zamani.

Bayan Jihar Kano, akwai jihohi da dama wadanda suke kokarin hana barace-barace a kan hanya. A cikin kwanan nan, Gwamnatin Jihar Neja ta hana bara a kan hanya tun daga ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2020, amma ta bayyana cewa, hanawar ba zai safi karatun allo ba. Mun sani cewa, gwamnatin kasar Saudi Arebiya da kuma kasashe masu arzikin man fetur sun hana bara.

Domin haka, muna kira da dukkan gwamnonin jihar Arewa da su hana barace-barace a kan hanya tare da bayar da ilimi kyauta da kuma tilasta ilimin. Saboda haka, muna kira ga gwamnan jihar Kano ya zantar da wannan tsari da ya amfata. Mun tabbatar da cewa, Ganduje zai samu nasarar rage yaran da ba sa zuwa makaranta a cikin Jihar Kano, za mu saka sunansa a cikin gwarzayen mutane.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: